MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Nakwa nakwa tayi da Fuska alamar zata kara saka kuka,Saurin taro habanta tayi tana Fadin”Oya Smile aha..,Smile MRS SALEEM KABIR KUMO”Kamar ana tallar closeup,haka ta washe baki tana Rumgumeta take Fadin”Tanque my best..”

Don Allah ku sakamin Mamata Acikin addu’o’inku bata da lafiya,kuyi mata Fatan Allah ya bata lafiya da darajan manzon Rahama sallallahu alaihi wasallam????????????????

Momyn Ladingo ce????

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

KURIKE GIRMAN AMANAR DANA BAKU,KUYI MIN ADALCI KAMAR YADDA NAYI MUKU KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

18

…………….Karfe goma da yan mintina Saleem ya shiga da motarshi cikin dan karamin flat din gidanshi,megadinsa ne ya rugo da gudu yana mishi barka da zuwa,bayan ya gaida Malika data ke Fitowa daga mota,tana bin dan karamin gidan nasu da kallo,duk da gidane daidai na talaka,ammh kuma ya burgeta sosai.

  Saleem da kanshi ya daukan mata akwatinta zuwa cikin gidan,mai dauke da Babban Falo da 2 bedroom sai kichen,shikenan,ammh duka dakunan akwai kayan more rayuwa aciki,Dayan bedroom din ya kaimata kayan nata,bai mata mgana ba,shi kuma ya Shiga wanda Tun dama nan ne dakinsa,Bai dade ba ya Fito ya Fice daga gidan gabadaya bayan ya sanar da ita ta shiga ciki Shi zai Fita.

Malika ta dade zaune afalo tana bin ko”ina da kallo kafin,tatashi ta shiga dakin daya nuna mata,shima din ba laifi,Tunda yana malale da wani makeken cafet,ja sai Gado da wardrope sai dressing morrior dinshi,sai Kofar tiolet,Dakin duk yayi kura sosai alamun andade ba”a Shigo shi ba,hankalinta ne yatashi ta rasa ta ina zata fara gyara dakin ita daba komai ta iya ba,Ta tuna sanda tana Asalin malikarta,wlh ko baranta bazai zauna awannan gidan ba,ammh gashi rayuwa ta juya da ita,itace zatayi rayuwa awannan gida,kuma batare da wasu yan aiki ba.

Hawaye suka cika mata ido,tayi zaune gefen gado tana goge hanci,ganin zama ba nata bane,cuz Malika bata son zama cikin kazanta mikewa tayi tafara kakkabe dakin tana gyarawa,sai gashi har kayanta ta zazzage daga akwati ta jera cikin wardrope tanayi tana hutawa,tana tunawa da merry da Dose,tana gode musu aranta,wanda ko dauko kaya batasan wahalanshi ba,

Koda tagama gyara dakin wanda harda tiolet ta wanke,don bazata iya wanka dashi ahaka ba,bayan ta ya kage,dakyar take mikewa,Falo kuwa sai da tayi hawaye wajen shareshi,kichen dai ko kallonshi batayi ba da dakin Saleem don koda tagama tafita hayyacinta,wanka tashiga tayi,saboda tsabar jigata azaune tayi sallah Azahar da la”asar alokaci daya saboda jirin data ke gani,Ashe harda yunwa sai lokacin ta tuna duk Wunin yau bata ci abinci ba,Jingina kanta tayi jikin gadon dakin tana tsiyayan hawaye,tana tuna yau fa in kaine to ka tabbatar da zuwa gobe waninka ne,Itace fa MALIKA MALIK abaya mace ce,mai aji da jinkai,ilimi da takama,In tagama sai tace bazataci abinci kasar Nageria ba kuma ta zaunu,Bata cikakken sati a kasa daya,ammh sai gashi yau ankoma itake rabe awannan gidan tana kukan Yunwa da gajiya,wayyo rayuwa kenan..

Haka take ta zencen zucci har barci yafara kwasheta babu Saleem ba dalilinshi,kiran wayartane ta farkar da ita daga barcin data fara nan kan Darduman,Zabura tayi ta mike ta dauki wayan wanda ke kan Stool din gadon tana neman Dauki,sunan Daddylove dinta tagani yana kiranta da hanzari ta dauka,tana gaisheshi amsawa yayi cikin murna da Farinciki kafin ya tambayeta iyayen mijinta da shi mijin nata,amsa mai tayi duk suna nan lafiya,nan take sanar dashi yau suka zo zamfara,yaji dadi sosai yayi ta sakamata albarka,jikinsa ta tambaya da kuma hajiya,yace komai lafiya,kafin yabama Hajiyar waya suka gaisa,tana kara jadaddamata data kula da kanta da Abunda ke cikinta,gyada kai take cikin zuciyarta tana kukan zucci.

Bata karajin kuka ya ciyota ba,sai da Daddy ke tambayanta taci abinci,wasu hawaye ne masu zafi suka ketomata,bata samu zarafin sharewa ba,tabarsu suna ta sauka bisa hijabin dake jikinta,dakyar ta furta eh taci saboda batason Ta fadi wani Abunda zai tadama Daddynta da hankali wanda bata da kamarshi duk Duniya,domin shine gatanta yanzu,koda suka yi sallama Daddy yaso ya fahimci wani abu game da ita,ammh ta tabbatarmai da lafiyanta kalau kuma babu Abunda take bukata.

Itako Zuru tayi bayan sunyi sallama,tana tuna lokacin tana gida,sai taga dama ma takecin abinci,in bataci ba ko Daddy ya dinga rawan jikin lallashinta taci abinci,in ko iskacinta yatashi sai tace duka abincin basu mata ba,sai ansake dafamata wani,Watarana ma ko andafa sai tace bataci ta dauki mota taje wani Restaurant taci abincin data ga dama,ammh gashi tana neman abincin ma taci basai ta jira an lallasheta ba,ammh bata samu Ba,Saleem yayi tafiyarshi ya ma manta yazo da wata halitta wai Malika.

Shiko Saleem Tunda ya Fita bai zarce ko”ina ba sai headquater su,meeting din daya tara suka shiga,sai wajen 3 suka Fito yafada office, yana shiga office ya tarda tarin Cases cases,kala kala nan yazauna yana dubasu kwata kwata bai samu sukunin kanshi ba banda sallah babu Abunda ke tadashi,kwata kwata ya manta da wata halitta malika,sai da Ummi ta kirasa tana tambayan ko sun isa lafiya,kuma ya turomata nombar Malika zata kirata ta mata Allah huta gajiya.”Sai alokacin ya saki salatin aranshi yana dafe kai,koda ya duba agogon Shidda saura na yammah,da hanzari ya Fice daga office din yana jin ransa babu dadi in bai manta bata karyaba gwarashi ma dayazo Office yasha tea,ammh itafa bataci komai ba,Tun safe ga kuma ciki,kai ya illah nan da nan yaji bai kyauta ba, gaskiya.

Agurguje ya isa wani Restaurant yayi mata take away din Fride rice,da ferfesun kayan ciki,sai lemon hollandian da Viju,don yaga ko agidansu tafi sonsu sosai,koda ya isa gidan Abun gwanin ban tsausayi,ashe da yunwar ta isheta Sai ta tuna da dambun namanta wanda Ummi ta bata,shi ta dauko ta dinga ci babu kama hannun yaro,toh shine ma man Gyadan suyan Dambun naman ya dinga Taso mata,sai amai tun tana iya tashi ta Shiga bayi har daga karshe takoma tana kelayashi akasan cafet din dakin,koda ya Shige ya isketa kwance cikin amai tana maida Numfashi ga dambun naman ne agefe aroba taci fiye da rabi da kwata,Hankalinsa tashe ya duka gabanta yana Fadin”innalillahi,ke me kika ci haka..’,?

Yafada yana binta da kallo,nan idonshi yabashi amsa,ganin robar dambun naman,ido ya zaro daya tuna yawanshi ammh saura kadan,Dawo da kallonshi yayi kanta ganin yadda hawaye ke Fita idanuwanta sai da yaji tsikar jikinsa ya tashi,Cikin wani yanayi ya Furta'”Dole kiyita amai kalli uban Dambun da kikaji haba,shikenan bazaki dinga kiyaye lafiyanki ba,Tunda kinsan halin dakike ciki..”

Bata iya dagowa ba,dakyar ta iya Furta”Yun..wa…Na..ji..”,Tafada tana Sharbe majina,Wani tsoro ne ya shigeshi ganin tana kara dago ido sama kamar zata shide,da hanzari ya ijiye lodojin daya shigo dashi ya kama hannunta ya ciccibeta tsab ajikinsa ya nufi hanyar Toilet da ita yana Fadin”Am srry sam na manta dake,koda naje office na tarar da tarin ayyukane,su suka daukemin hankali,ammh da kika jini Shuru why not kikirani ta wayata..”,Tanajinsa bata iya bashi amsa saboda wani Haushi ma,daya kamata ita ina taga nombarshi balle ta kirashi,Kalmar ya manta da ita tafi komai bakanta mata,ita take sata kwallah tanayi tana Sharewa da hannu.,sauke ta yayi tayi saurin dafa bango ta tsaya kan kafafunta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button