MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty


“”Yau din takama Weeked ne Ranar Sunday kenan,gashi suna cikin Hutu ne dagasu har yaran,Tun jiya da Daddare da suka dawo Daga kano,wajen Taron Na Malika malik Foundation inda ta gudanar da Bada Kudaden da za”a ma yara yanmata guda Hamsin kayan daki wadanda zasu aure ammh iyayensu basu da Hali sosai Shiyasa kwamitin kungiyar ta jahar kano Ta nemi data Taimakamusu,wannnan Shine Dalilin Zuwanta Kuma Alhamdulillah Ta taimaka Daidai gwargwardo,duk inda taje bata kwana Koman dare zata dawo,shima Saleem din bayanan ajiyan sunyi Taro Afadar Shugaban kasa,shima sai dare ya dawo Dukkansu Tunda suka kwanta sai barcin gajiya Dakyar suka iya tashi Sukayi sallar asuba suka koma suka kamkame juna suna cigaba da barcin gajiya.

Ummita da Sadiq Tun daren Jiya suka Hada kayansu Tsaf sukace wannan Hutun Sufa gidan Goggo Saleema zasuyi shi,su kuma hajiya da Khalipa suka ce ada sunzo zuwa gidan Ummi ammh Tunda su Yaya aryan na chan sun Fasa,yanzu Gidan Dadddi zasu je su gama Hutunsu achan,tunkafin Ranar suka Shaidama iyayen nasu ammh sai sukace su bari Weeked sai su Tafi,ammh gashi Weeked tayi Dukkansu basu Wuni agida ba,ga yau ma tayi ammh dukkansu babu Wanda ya Sauko kasa.

Tun Karfe 8 na Safe suka Shirya kowanne ya jayo Trolley dinsa ya kame kan Kujera suna Jiran saukowan Iyayen nasu,kowanne ya kurama upstair ido yaga ta ina zasu bullo,Da ka kalli Fuskarsu zasu tabbatar da Ransu bace yake,gashi Tarbiyan da iyayen suka basu babu ta Shiga musu dakin barci indai basu tashi ba,Baba Larai mai aiki wacce Suka daukota daga Kumo tayi tayi suzo su karya kowanne ya Tura baki yana Fadin”Am ok..”Dayake yaran Sun taso cikin Tarbiyan iyayensu suna da girmama na gaba dasu,sannan Saboda yadda bakinsu ya saba ko”ina sukaje ba kasafai suke mgana da Hausa ba,sunfi saka yaren Turanci abakinsu ta wani bangaren kuma suna jin larabci sosai saboda Abbansu ya iya Shiyake koya musu,balle kuma Malaminsu wanda ke koya musu karatu bayan sun Dawo Hutu Mallam Usman baya musu mgana cikin harshen Hausa Shiyasa suka iya,duk bangaren Daka tabosu basu da wasa.

goggo Hadiza ta kalli Ummita tana Fadin”Ummita Wannan Hade Fuska kuma Duk tamana yaji ne..? Tura baki Ummita tayi tana Fadin”Goggo Hadiza ,Su Mommy fa sukaki Fitowa,Alhalin kuma mun Fada musu zamu Hutu yau gidan Goggo Saleema…”Sadiq ya karbe da Fadin”Eh wlh,kuma lagos ba kusa ba,Ni addu”ata Allah sa ko Daddy ne yafara Fitowa da Mommy kunsanta in tayi Tafiya ta gaji bata Fitowa da Wuri.”Baki khalipa ya Tura kafin yace”Ni fa na gaji da zaman gidan Allah bai kawo Wani light.”Yafada yana Cije baki Hajiya ce karamarsu yar Shekara Shida tace”Nidai ina son zama da Mommy da Daddy muyi ta hira..”Harara Ummita ta sakarmata tana Fadin”Ji wannan,Yasin ki ma kama kanki don Daddy bayason Hira da kowa sai Mommy su kule suki Fitowa mu su barmu da game ko kallo,gwara muje Hutunmu mu hade da Ya Ayda ehyyyyr…”Tafada tana Ihun murna,Goggo Hadiza da Baba larai na musu Dariya.

Hajiya tace”Toh zan biku gidan Goggo Saleema..”atare Ummita da Sadiq suka taso suna Zaro ido lokaci daya suka ce”Ina….?,Waza ki bi..? lalle ma yarinyarnan kima kama kanki Tun Wuri don Wlh bazaki bimu ba,tabdijam ki Wuce kibi Khalipa gidan Daddi..”Jin haka yasa Hajiya ta bare baki ta saki Kuka harda buga kafa,Suko mai zasu yi banda Mata Dariya itako tana kukan Wlh sai ta bisu Gidan Goggo Saleema.

Daga chan Sama Sukaji muryan Daddynsu yana Fadin”A”a Wa Yatabamin Hajiya da Safen Farin haka.?.”Dukkansu suka Kurama inda sukaji muryan Daddynsu ido,Dan matashin Dattaji ne yana Sanye da Jallabiya Mai Ruwan Toka,Idanuwansa suna lullube da Farin glass mai kara karfin gani,Kallon Farko zakama Saleem lokaci daya zaka Fahimci yafara zama Dattijo,domin har Farin gashi yafara bayyana a kansa,duk da Halittace dan kimamin Shekaru 50 aduniya ne ayanzu Bai kara kiba ba,sai sai yakara Murjewa da Kuma kara haske Saboda Hutu da kuma karin Jin Dadi.

Hannunsa na Sarke cikin na Malika Wacce ke Sanye da Wata abaya Doguwar Riga kirar Armani,Ta yane kanta da Wani jan Vail domin kwalliyan adon Kayan Red colour ne,Kyakywan Fuskarta wacce bata bayyana alamun Tsufa ta bayyana Sosai masu jere da Hakoran makka guda biyu,wanda suka karamata kyau,duk da Shekaru sun ja,ammh bazaka taba ganewa ba,saboda Hutu da jin dadi sun boye hakan sai dai zaka Fahimta da yanayinta Tunda ai jiya ba yau ba,

Da gudu Hajiya ta ruga ta Rumgume iyayen nata dake kokarin Saukowa daga Steps,cikin hanzari Saleem ya Saki Hannun Malika ya Daga Hajiya Sama yana Fadin”Waya taba min ke..? gayamin yanzu na masa bulala..? Kwabe Fuska tayi tana kara Rufe ido Tace”Ba su Ya Ummita ba ne,da ya Sadiq bane suka ce bazasu dani gidan Goggo Saleema ba..”Tafada Tana kara Saka kuka,Dariya ta kama Malika tasa hannu ta karbi Hajiya suna karisawa saukowa daga Steps take Fadin”Wa ya isa..? Manta dasu ke kadai ma zaki Hutu wannan karon..”Tafada tana Dagama Ummita gira wanda suka kara Hade rai jin Abunda Momy tace.

Goggo Hadiza sai dariya take Ganin yadda yaran suka kara Hade rai Suna kunkuni,suko iyayen nasu namusu Dariya ganin yadda sukayi ne yasa Hajiya dake hannun Malika ta hau ti musu gwalo,Zuciya ta Ciyo Ummita ta mike tana Hararanta,Saleem ne ya Daga mata hannu yana Fadin”Hy duk wannan Bata Fuska da Fushin na miye ne Ummitan Daddy..? Goggo Hadiza ce tace”Fushinku ne,nan fa duk jiran saukowanku Suke sun Shirya tsab yau sai Tafiya Hutu..”Sai lokacin suka Lura da manyan akwatun nasu dake Tsaye awajen Baki Saleem ya kama yana kallon Malika kafin su Gimtse dariyansu,Saleem ne ya zauna tsakanin Ummita da Sadiq ita kuma Malika ta zauna gefen Khalipa suka sanya ya”yansu atsakiya,Saleem ne yace”Duk ku tsaya yanzu kowa ya Fadi inda yake son Zuwa Hutu. “Da hanzari Ummita tace”Daddy ni da Sadiq Wajen Goggo Saleema zamu Hutu wannan karon mun barma su Ya aryan gidan Abbi..”Dariya yayi kafin ya kalli Khalipa yana Fadin”Babban yaya kai ina zaka..? Mirmishi yayi yana Fadin”Daddy gidan Daddi na zani nidai kasan bana chanji gidan Hutu..”Kansa ya Shafa yana Fadin”God boy,dama Ai Shima takwaran naka sonkai yake Nunawa,yafi son Zuwanka Fiye dana kowa..”Malika ne tace”Hajajju ke ina zaki Hutu ko zaki zauna damu..”Saurin girgiza kai tayi tana Fadin”No Momy gidan Goggo Saleema zani..”Da Sauri Ummita ta zaburo zatayi mgana Saleem ya dakatar da ita ta hanyar Rike ta yana Fadin”Ke wlh kin gado mai Sunanki sam baki da Hakuri..”Yafada yana Dungure mata kai,Kwabe Fuska tayi ta koma tana Hararan Hajiya,Malika ne tace”Toh Duk ku tsaya naga duk kuna Neman guduwa ne bamai tsayawa Wajen Goggo balle Wajen Anty Marym..”Dukkansu suka cuno baki suna bazasu tsaya ba,goggo Hadiza na Dariya tace”Allah Raka taki gona nima wlh na gaji da ku ku kara gaba gida yamana Shuru..”Malika Ta murmusa tana Fadin”Kyelesu goggo ai ke dama Uwar Malika ce,kinga duk zumudin nan da Sukeyi gidan Ummi zasu ci burgi don Jiya da daddare duka Daga gidan Goggo Saleeman har Gidan Daddi Marwan din Sun sauka gidan Ummi..”Jin haka yasa suka saka ihun murna Suna Fadin”Da gaske Mommy..”aiko amsa bata basu ba Suka mike kowanne ya Dauki akwatinsa suka Bi hanyar Fita suna Fadin”Daddy,mommy goggo,Mun tafi gidan Ummi,Achan zamu yi Hutunmu sai kunzo..”Suka Fada Suna Ficewa Harda Hajiya wacce ta Tashi Daga Hannun Malika ta bisu da gudu,Iyayen nasu suka bisu da kallon Sha”awa da kauna,Waje sukayi Dole Direba ya kwashesu amota Zuwa Gidan Ummi don sun matsu suga yan”uwan nasu musamman ma Ya Ayda Wacce ke Nesa,gwamma Su Ya aryan suna ganinsu in sunje Gidan Ummi ko kuma In su sunzo gidansu Duk da ba kasafai suke Zuwa ba.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button