MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Korarshi sukayi waje,ammh da ya zauna kusa da itane ya rikemata hannu yana Lallashinta,Ranar dagashi har maman Abba da Joda babu wanda ya Runtsa saboda tashin hankali,har wajen asuba malika shuru bata haihuwa ba,ga karfinta ya kare,kawai sai likitoci Suka Nemi Saleem daya saka hannu zasu Shiga da ita dakin Tiyata,nan da nan ko ya rattaba hankalinshi tashe,daman ya gaji da wahalar da Malika kesha hakanan..

Sai bayan an Shiga da ita dakin Tiyata din ne yasamu sukunin kiran Abbi ya sanar dashi Abunda ke Faruwa,wanda yadinga salati yana kiran Sunan Allah,Koda yake sanar dasu Ummi da hajiya,wacce bata dade da dawowa daga kumo ba,don ko bikin Zahra da Saleem da akayi batanan,Suma salatin suka saka suna Fatan Allah ya sauketa lafiya,itako Saleema tanaji ammh sai ta nuna kamar bata sani ba,nan ko cikin ranta addu’a take kada Allah yasa Malikan ma ta rayu.

Joda kuma ta kira Hajiya Binta ta sanar da ita Abunda ke Faruwa,matukar tsausaya Hajiya ta tsausayama Malika,saboda tasani yau zataji Abunda kowacce uwa taji kafin ta haihu,Haka ta dinga mata addu’ar Allah yasa ayi aiki lafiya afito lafiya.


Alhamdulillah Anyi Nasarar Yima Malika aiki kuma an Fito mata da kyakyawan yarinyarta wacce take kama da ubanta sak,sai dai ta debo hasken Fatan mamanta,Tuni har ankaisu dakin hutu malika bata Farfado ba,ammh an gyare bby tas gwanin ban sha’awa,Murna wajen Saleem ba’a mgana sai da yayi Sujjuda ya mika godiyarsa ga Allah (SWA) domin Shine ke badawa kuma Shike Hanawa.
.

Shi yayi ta kiran yan”uwa da abokan arziki yana sanar dasu anfito da malika lafiya kuma ansamu Babby girl,ciki harda Zahra wanda haihuwar kwata kwata bata mata dadi ba,sai ta nunama Saleem din don daya gayamata haka tayi Shuru taki mgana sai da yakara maimaitamata kana tace Allah ya raya ta yanke kiran,ya dade yana kallon wayar yana mamakin zahra yana so ya Fahimci wani abu game da yarinyar,wacce Tun Abunda tayi jiya ya gane ya bar Shiri Tun rani,ammh zai tambayi malika in takoma gida yaji wani irin zama suke gudawar ita da Zahra.

Malika bata Farfado ba sai da yammah,nan ta ci karo da Abunda aka Ciro mata,haka ta dauki yarinyar tana kuka,ba kukan komai take ba,sai kukan Mallam zai rabu da ita,acikin wannan Halin ya Shigo ya sameta nan ya hadasu ita da Bbyn ya Rumgume yana mata godiya,ammh abun mamaki Malika kanzil batace mai ba Tun yana ganin Rudin haihuwace da kuma aikin dake jikinta,ammh har washegari Batamai mgana ba,dayayimata zata kauda kai tana kuka Abun yabashi mamaki matuka,ammh sai ya kyaleta sai sun koma gida yaji meya faru kuma.

Sai Ranar yakoma Zamfara yabar Maman Abba da joda,koda ya koma Zahra kota tambayeshi ya maijego da bby,kuma koda yake chan Asibitin koda kuskure bata taba kiranshi taji ya ake ciki ba,sai dai inshine ya kirata,mamakinta kawai yakeyi,ammh sai bai mata mgana ba ya kyaleta yaga iya gudun Ruwanta,Ranar bai koma asibitin ba,saboda goggo Hadiza aka turo tazo daga Malunfashi don ta zauna da malika tana kula da ita,tunda dai joda yarinyace bazata iya ba,Maman Abba kuma ta dawo gida,washe garin ma kiran Ummi ya samu yana wajen aiki ta sanar dashi gasu asibitin basu ganshi ba,yace yana tafe,daga wajen aiki gusau din yakoma chan ya tarar da Ummi da Hajiya da Abbi sunce sunma dade da zuwa,sai wajen la’asar kana sukayi Shirin Tafiya inda Ummi taja Saleem gefe tana Tambayanshi”Ina abokiyar zaman malika da batazo asibiti ba,kuma joda ta sanar da ita makociyar Malika ce tazo ta taimakamata kwanansu biyu tare,bata tafi ba sai da goggon Malika tazo..?

Kame kame Yafarama Ummi Tundaganan tagane akwai mtsala,kafin yasamu karyar cemata zahran itama tana gida bata da lafiya,Ajiyar zuciya Ummi ta sauke kafin tace”gaskiya Abun baiyi tsari ba ka gyara zamantakewar gidanka,ai yakamata Tunda ba kwance take ba,ta biyoka yau tazo dubata ko? kansa na kasa yace ma Ummi ba daga gida yake ba,ammh insha Allahu gobe zasu zo tare,Ummi bata komai ba,sukayi musu sallama suka koma hanyar Abuja,su suka kawomusu kwando guda na coolers,cike da abinci sai kayan Fruits.

Mganar da Ummi tayima Saleem ta tsayamai arai har yakoma gida yana auna magarta inda yaga tabbas gaskiya ne,kuma Duniya na nan na Zaginshi akan Abunda Zahra tayi,ammh ba komai bari Malikan ta daawo gida zaiji dalili,Tun adaren ya sanar da Zahra cewa gobe zasu je asibiti da ita ta Duba malika,kodaga yanayin yadda tayi ya Fahimci batayi niyyar zuwa ba,aiko hakane gari na wayewa Zahra ta kwanta tana rawan sanyi tace bata da lafiya,mamakinta ya kamashi bai mata mgana ba ya sakai ya Fice,wanda duk Abunda tayi Saleema ce ta kitsa matashi,yana Fita ko ta kirata suna Dariya,nan Saleema ke sanar da ita gobe zata zo,su cigaba daga inda suka tsaya murna ta kama zahra tadinga Jin dadin zuwan Saleeman agobe.

Har Washegarin Ranar da Saleema zatazo Saleem bai sani ba,saboda Tun Safe yatafi gusau saboda yau din za”a sallamosu su dawo gida,koda yaje shiyayi cike cike da kuma biyan kudin wasu magungunar daba’a biya ba,kafin abasu sallama,shida kanshi yazo yana hada musu kayansu bayan su joda sun kwashi wasu kayan zuwa mota,Nan ne Malika ta kalleshi kafin tacemai tana neman wata alfarma ne,koda ya bata dama kawai sai tace don Allah yayimata alfarma barin ayi suna kafin ya saketa..”Mganar tazomai abazata zama yayi kusa da ita yana tambayanta shi bai gane ina ta dosa ba? waye yace mata Shi Saleem zai saketa..? kin amsashi tayi yayi mganar Duniyar taki magana daga bayama sai ta sakamai kuka,dole ya rabu da ita,ammh bawai don ya bar mganar ba,sai da yayi Shuru ne sai sun koma gida ya turketa yaji daga ina aka samo wannan iskancin.

Suna dawowa sukaci karo da Saleema ta iso,Saleem har ga Allah yayi mamakin ganinta,daya tambayeta meya kawota kuma yaushe tazo..? Sai tace bata dade ba,kuma tazo ganin mejego ne da kuma bby,Cikin mamaki yake tambayanta meyasa bata zo asibitin ba,sai tayi missing step tace wai Zahra tace mata yau zasu dawo gida,Yayi mamakin jin haka sabida ko zahra batasan yau za”a sallamo Malika daga asibiti ba? toh waya gaya mata..?bai maida mganar Serious ba,ya share kawai bai zauna ba yakoma wajen Aikinsa,itakuma goggo Hadiza ta saka Ruwan zafi tatara malika bayi tamata wanka ta gasata sosai duk ko achan asibitin tana gasata,ita kuma maman Abba ita tama bby wanka aka sanyata cikin kayan sanyi masu kyau da ban Sha”awa..”

Zahra ko Da Saleema wannan Haihuwa dai bata yi musu dadi ba,Har yammah basu shigo sun duba Maijego ba,kuma anajin dariyansu afalo,ammh kuma basu shiga ba,sai dare kana suka Shiga suka dauki yarinyar awulakance har zahra na Fadin tabiyo jar Fatan kakaninta Arna,Tafada tana dariya Saleema ko Fadi take,sai dai amata fatan Shiriya kinsan ana tsotson Iskanci da rashin tarbiya ajikin Nonon uwa..”haka sukayita fadar maganganu son ransu,Joda taso tayi mgana Ammh goggo Hadiza ta hanasu tace su kyalesu komai zasuyi kada su tankansu saboda su neman wanda zai tankasu ne suyi fada dashi,Haka akayi ba wanda ke bi takansu aiki ko ko changal basayi acikin gidan alhalin Saleema cewa tayi zatazo ta taimakama zahra da aiki,Joda ce da Maman Abba ke ta dawainiya da Malika suyi girki su gyara gida,su sakama malika Ruwan wanka,aikin goggo Hadiza kawai Yima Malika wanka da kula da ita ita da Bby,wacce ta samu Ruwan Nono sosai wanda yake taimaka jaririyar wajen samun Abinci sosai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button