MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Da kanshi ya hadamata Ruwan wanka,ganin ya Nufota,da hanzari taja baya tana fadin”Zan iya yi da kaina..”Bai damu ya tabe baki yana Fadin”Ok..”Daganan ya Fice daga bayin,yana Fita tabi bayanshi da kallo tana Sakin Siririn kuka,Tanajin takaichi yadda yanzu komai na yaron yake burgeta,tanajin gwara ta zauna dashi Fiye da kowa ayanzu,dakyar ta iya shiga bath din ta gasa jikinta,ammh tanayi tana kukan makomar rayuwa,yanzu balle ma nan gaba.

Sai gashi Saleem ya nadadde kafan wando hannun Riga,shi ya goge aman datayi Tas,kamar bata bata wajen ba,Duk da babu wanda ya kaishi kyamkyamin amai,Aranshi yasa ne kawai don shine silan Shiganta wannan Halin ya barta da yunwa,da kar wani abu ya sameta Abbi da Ummi su tsinemai yabi Duniya,shiyasa ya zage ya gyara ko”ina,koda ta Fito bashi adakin ammh ya barmata sakon Take away dinta,kallo daya tayi ma take away din ta kauda kai domin Duk wani abinci ya Fitar mata aka yanzu,mai ta shafa tazo ta shimfida sallaya,ta nada mayafinta akai,Tunda hijabin ya lalace tayi sallar mangariba,bata tashi daga wajen ba,sai datayi sallar isha”i kana ta rarrafa ta hau gado ta kwanta tana ji kamar bayanta zai cire,Dakyar tasamu barci ya kwasheta.

Shima saleem ya dakinshi yakoma yayi wanka yayi alwala ya fita masallaci nan gaban gidan ne,shima bai dawo ba,sai da yayi sallar isha”i,ya shigo mata da kaza kasassiya koda ya leka dakinta tayi barci duk ta kure,Ya dade tsaye yana kallon Fuskarta yadda duk ta rame kwana biyu,bai san dalili ba kawai sai yana jin tsausayinta yana Shiganshi duk da bayason tasirin hakan ya shigesu sosai,kauda kai yayi zai Fita,sai idonshi yakai kan Lodojin take away din daya yimata,ganin bata taba bane,yasa ya dauka duka harda kazan ya kaimata kichen ya bude fridge ya sakamata aranshi yana Fadin”Zaki nemeshi gobe,in baki ci yau ba..”

Shima dakinshi ya shiga yayi shirin barci yafada gado,sai alokacin ya kara duba wayarsa,wacce ya bari agida misseds din Zahra ba adadi kai ya dafe aranshi yana Fadin”Allah ya hadani jaraba,kai yarinyarnan in mayyace takama mutum sai Allah kuma..”Tsaki yaja afili kafin ya latsa nombar ya marwan wanda hardashi a cikin wadanda suka kirashi baya kusa.


Washegari Saleem bai yarda yabar Malika da yunwa ba,12 nayi yaje yayo mata take away yakai mata,Tunda dai ba’iya girkin zatayi ba,koda ma zata iya yi bata iya dafa komai ba,so ko ma yace tayi zai batama kanshi lokaci ne,balle bata da wani issshiyar lafiya sosai,shiyasa ya dauki Nauyi kullun yayo mata takeway sau uku arana.

Basu samu daman cigaba da karatu ba,sai da suka kwana biyu da zuwa kana yake dora mata da daddare,da asuba kuma ta biyamai,babu laifi Tafara sanin addininta da abubuwan daya kamata tasani,Kayan sawanta kuwa Sargent musa yayima mganar yanason Siyan Atamfofi da lesuna,da hijabai,da kuma inda za”ayimai dinkuna masu kyau,nan yacemai ai baya da mtsalan wannan matarshi tana Sana”ar Saida Atamfofi,gabadaya kwangilan Siyan kayan da dinkin ya tura mata ta acccoun dinta ita kuma ta siyan mata atamfofi da lesuna,aka dinkamata dinkin Riga da sikat,da masu zani,ko masurement dita,shi ya fasalta yadda take,saboda yana ji aranshi ba wani wawan Telan da zai bari yazo ya saka tep ya gwadamai matarshi.????

Nadira kuwa tacika alqawari domin takira Saleem,ammh itama sai da tayimai 3 missedcalls,kafin ya daga lokacin yana office yana aiki,kanshi ya dau zafi,koda ya daga kiran Bai yi mgana ba ganin bakuwar nombace,Tunkafin yace komai Nadira ta gabatar da kanta amtsayin Cousin Sister din Zahra,yamutsa Fuska yayi yana asking dinta wacece zahra kuma? Amsa ta bashi da Fadin”Zahra bukar mada,sai lokacin ya tuna da mayyar yarinya,Tsuke baki yayi yana jin bayanin Nadira tana sanar dashi irin halin da Zahra ta shiga saboda shi,wai harda kuka baki ya rike yana Jinjina Abun,aranshi yana Fadin”Lalle yarinya kin zake dayawa..”Hakuri yabama Nadira yana sanar da ita Aiki ne yayimai waya baya samun lokacin kansa,ammh tabari zuwa anjuma in ya koma zai kirata insha Allahu,daga haka sukayi sallama ya kife wayar yana jan tsaki,haushi duk ya kamashi Afili ya Furta”,Nayi kuskuren bama Yarinyarnan Digit dina wlh..”Yafada yana Sosa kunnenshi da pen din dake hannunshi.

Itako Zahra agabanta Nadira ta kira Saleem, bayan ta saka wayar aspeaker,tana jin sanda yace zai kirata ta koma gefe tana tsallen murna,Suna gama wayar ko,ta daka tsalle ta Rumgume Nadira tana mata godiya,itako tana binta da dariya bayan ta zaunar da ita tana bata Wasu karin Sirrinka da zata kama zuciyar Saleem dashi itako tana gyada kai murna duk ya cikata,kamar ance gobe ne bikinsu.

Shiko Saleem aranar bai koma gida ba,sai araound 10:39,yakoma agajiye Takeway din Malika ya kaimata fridge,saboda ya iske har tayi barci,Wanka kawai yayi dakyar yayi shafa’i da Wuturi,ya haye gado zai kwanta,wayarsa ya dauka zai kashe,sai yaga sakon zahra na yawo bisa saman wayarshi,yana ganin sakon bai kai ga Shiga ba alqawarin da yayi mata ya fadomai arai,bai karanta sakon ba ya lalubo nombarta wacce bai adanata ba,ammh tsabar nacin kiranta yasa ya ke gane Nombar.

Zahra ko tana zaune dirshan akan gado tayi tagumi da hannu bibbiyu faskekiyar wayarta ne agabanta ta zura mata ido,fuskarta tana nuna tsantsan damuwar datake ciki,Nadira dake gefe kwance ta dago tana kallonta kafin tace”Wai don Allah best baki kwanciya kibar wannan damuwar..?

Bata kalleta ba tace cikin Sanyin murya kamar zata fashe da kuka,..”,Toh bai kirani ba best..”Ajiyar zuciya ta sauke kafin tayi mgana wayar Zahra dake gabanta ta dau tsuwa,koda ta kyallah ido taga Sunan Saleem wanda tayi Saving da COOL EYES da wani uban zabura da chakuma ta damko wayar ba inda jikinta baya rawa take Fadin”Best..best gashi yana kirana..”Mikewa zaune Nadira tayi tana Fadin”Dallah to ki dauka,kin zauna kina rawan jiki,har sai wayar ta katse..”Tana jin haka ta dauki wayan tana karawa akunne cikin sanyayyiyar muryanta ta Furta..”Hello…”

Gyara kwanciya yayi yana Fadin”Hello kina lafiya..”Ya fada kai tsaye,Washe baki tayi kamar zatayi dariya,Hararanta Nadira tayi tana Mata mgana da hannu,da hanzari ta gyara muryanta tana Fadin”Lafiya lau,Fatan kaima kana cikin koshin lafiya kamar yadda nake..”,Fuskarsa ya dan saki kafin yace”Normal…”Shuru ne ya biyo bayan kafin Saleem ya kauda shurun da Fadin”Dazu cousin Sis dinki ta kirani,duk da am very Sure,kina wajen ta kirani,so tayimin complain din kina kirana bana picking,do u know what..? Girgiza kai tayi kamar yana ganinta kamar yasani ya cigaba da fadin”Ban cika son yawan takura ba,ni mutum ne jama”a,kuma ina kokarin kare hakkin kasata,da kuma Tsoron rantsuwan danayi wajen sanya kakin yan sanda,so plz nd plz kidaina damuna da kiranki kina Shiga uzuri na sosai,ki bari ni dakaina in na samu lokaci i promise u i will call u..”Wani yamm Zahra taji idanuwanta suka ciko da kwallah,Ta juya tana kallon Nadira,wacce taji komai domin Zahra ta sanyamata aspeaker.

Alamu tayi mata da hannun data bashi hakuri,Maida kwalarta tayi kafin tace”Ayyh am srry bansan cewa kulawar danayi dakai zai zama laifi ko takura ba,buh insha Allahu korafinka ya karbu za”a kiyaye..”Tana Fada tana yaken karfin hali,mirmishi yayi mai sauti ganin kamar mganarshi ta sosa mata rai,sai yadan saki ranshi yana tambayanta mutanen gidan,kafin ya gangaro yana tambayanta karatu,nan zahra ta tankwashe kafa tana bama Saleem lbrin matakin karatunta,dayake ta iya lankwashe murya,duk bawasu kalamai ta iya ba,Nadira ce ke dorata bisa hanya,Tunda ta Fita budewar ido.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button