MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Tafada tana duba Fuskarta itako Saleema tana kara Narkewa tana fadin”Hajiya dubamin kunnan nan,Allah banaji sosai..”Tafada tana matso kwallah,Tsaki Saleem yaja yana Fadin”Allah yasa kidaijin gabadaya naga karshen iyayi da rashin kunya..”Hajiya ce tayo kanshi da gudu tana fadin”Ja’irin yaro kawai..”Take Fada tana binsa da gudu suka fara zagaye falon Saleema dake gefe tana dariya tayi wajen wayar Saleem nan ta iske haryanzu Ya marwan na bisa layi,dariya kawai yake ci diramar hajiya da Saleem shiya hanashi kashewa domin duk duniya babu wanda yakeso da kauna kamar family dinsa,da ihun murna Saleema tace.

“Ya marwan I miss u..”Miss u too our little kiddo,ya sch..? Amswa tayi da lafiya kalau kafin tace”Ya marwan yaushe zaka dawo…? Kwalla ya Share saboda kewan Gida yace”Very Soon Little,naji Hajiya ita da megidanta suna kwamawa,ina ta dariya”Dariya tasaka tana kallon yadda Saleem yake gajiyar da hajiya da gudu itako taki daina binsa shiko da gangan yake zagaye falon yana mata gwalo,dariya saleema ta saka Tana Fadin”Wlh ya saleem zai gajiyar ma Da hajiya kashinta kaga yadda yake sakata gudu..? Da sauri Ya marwan yace”Little bari na kiraki Vid cll,juz ki haskamin nga wannan diramar kinji..”Da hanzari tace”Yanzu kuwa ya marwa mai jirgi,..”Tafada tana dariya yanke kiran yayi da hanzari ya Shiga wattsop,dayake tasan wayar Ya Saleem baya sanyamata password da hanzari ta shiga chairt dinshi tana bude data sai ga kiran ya marwan ta dauka tana Fadin”Ya marwan wacth dis comedy plz..”Take Fada tana haskomai Saleem wanda ya dage yana zagaye kujera hajiya na binshi da Filon kujera tana Fadin”Allah sa na kamaka ka gani maketancin yaro kawai..”Kan kujera Saleema ta haye tana Fadin”Yauwa hajiya ki kamasa,kin kusa,yauwa kamasa ….”

Take Fada tana dariya Ya marwan saboda dariya sai da ya duka cikin dariya yake Fadin”Dan sanda yabada training na rage kitsen jikin hajiya fa..”

‘””Kai Saleem ungo naka nan,don mai garinku Uwartawa kake son kashemin…”

Sukaji anfada daga  saman saukowa step Din benen dakin Abbi,dukkansu suka waiga suna kallon wani Dan Dattijo wanda akallah zai bama Shekaru 58 baya aduniya,ammh akallon Farko bazakace haka,saboda yadda yake dogo,kadan kadan Farin gashi yake akansa da gemunsa,Sanye yake da bakar jallabiya sai wani karamin gilashi mai karamai karfin gani,Jarida ce ahannunsa yana kokarin saukowa yake kara cewa”Saleem wlh kafita daga idona,so kake ka kashemin uwa da shanshancinka ko?

Hajiya na jin haka ta zube kasa tana Share gumi ga hawaye suna zubomata tana Nurfafashi kamar mai Asthma,Saleema tayi saurin yanke wayarsu da Yaya marwan ta nufi Hajiya tana Fadin”Hajiya hajiya sannu bari na kawo miki Ruwa..”Tafada tana kunshe dariyarta,Saleem dake gefe ya tafi ga Abbi yafadamai yana Fadin”I miss u Abbi…”Turesa yayi yana Fadin”banyi kewarka ba,tunda daga dawowa zaka saka hajiya adamuwa..”Yafada yana karisa saukowa gaban hajiya ya durkusa yana Fadin”Don Allah hajiya kidaina biyema Saleem,wahalar dake kawai yakeso ya dinga yi..”Dagowa tayi tana share kwallah tace”Kabiru ka barni da yaron nan,Allah sai na mai rashin mutumci,kalli yadda yasani Gudu yanzu gabadaya jikina ciwo yake,Numfashina na Fita da Sauri Sauri,kilama na samu ciwon na Iska me ma sunanshi Saleema..”Da hanzari Saleema tace”Hajiya Asthma..”Da hanzari tace”Eh Asma,kalli kagani..”Take fada tana share zufa.

Saleem dake gefe  ya kyalkyace Da dariya Haryana rike ciki yace”Bawanni Fa Asthma,Abbi kawai nasata gudu ne ta jijjiga jini,kullum tana zaune agida,kitse yazauna mata waje daya..”Yake Fada yana ta kwasa dariya ji yayi an Damkemai kunni ta baya ana Fadin”Saleem wai kunnenka na kashi ne? kwata kwata bakajin mgana,kullum kana girma ne,kana cin kasa ko..”Hannunta yariko yana Fadin”Ummi na…”Yake fada yana zagayowa ta gabanta kallonta yayi kafin kawai ya Rumgumeta yana Fadin”Nayi kewar Lauya mamata..”Yafada yana wani narkemata bayansa ta shafa tana Fadin”Nima haka my Son,ya aikin..?Tafada tana dagosa daga jikinta Yamutsa Fuska yayi yana Fadin”Ba dadi Ummi,wlh wahala tayi yawa baki ga sai Rama nake ba..”Dariya suka sakamai kafin saleema tace,”Bawani kaida wlh lalacinka yayi yawa Ya saleem…”

Daure Fuska yayi yana Fadib”Waye malalacin..? Makewa tayi bayan Abbi tana Fadin”Acp Saleem kabir kumo mana..”da gudu ya bita bayan Abbi,Ummi na Fadin”Saleem kabari meye haka,zaku fara ko..? ina ko jinta bayayi zungurota yake daga bayan Abbi yana Fadin”Ki fito kigani wlh sai na Barki kwance yau zaki gane waye malalaci tsakanin ni da wanchan dan kauyen Saurayinnaki..”Abbi ne ya harde hannu akirji yana Fadin”To daketa mara kunya,ai ko mutuwa najin kunya mahaifi mallam..”Bata Fuska yayi yana Fadin”Haba Abbi yanzu don Allah sai na bar karamar yarinya nacemin malalaci in kyaleta..”Hajiya dake zaune tace”To karya tayi,ai ni inaga aikin yan Sandan ma,babanka yayi munamuna aka baka,ammh bawai don ka chanchanta ba,jarumi dayane agidan nan Marwanuna shine kadai Namijin gaske..”Tafada tana hararansa,wani Abu yazomai wuya ya juya yana kallon Hajiya rai bace”Karki kara walh…”Abbi yace”in kuma takara fa..? Yafada yana kallonsa Waigowa yayi yana wani hade rai yace”Ta kwana acell..”!,Yafada kasa kasa yadda bamai jinsa,kallonsa Ummi tayi tana dariya tace'”Mekace..? Hanyar Dakinsa yayi yana Fadin”Bance komai ba..”Dariya suka sakamai Abbi ya girgiza kai yana Fadin”Ke kuma Fito daga bayana,sau nawa zan fadamiki kifita harkan Saleem ehe…?Tura baki tayi tana Fadin”Abbi shifa ke shiga harkata..”Hajiya ta karbe tana Fadin”kaji ka dawani zence,wannan Ja”irin Da’n naka,ko ba’a shiga harkansa sai ya Shiga na mutum,ni wlh addu”a,nake Allah yabashi wata mata masifaffa,yadda zataci mana ubanshi dakyau..”Gabadaya suka kece dariya Ummi na dariya ta Wuce kichen tana Fadin”Little ni zo ki tayani kwaso abincin nan zuwa Dinner area,don rigimarku bata karewa keda Saleem da hajiya..”

Jin haka yasa ta Fito daga bayan Abbi zata bi Bayan Ummi kamar walkiya taga Mutum agabanta yana fadin”Wa na kama..”Ai da gudu ta juya ta nufi sama tana tana fadin”Wayyo Ummi,kinganshi ko..? Shima agujen ya marata baya yana Fadin”Ummi ta aikeki kiman Rashin kunya,..”Taka taka sukayi sama aguje,Girgiza kai Abbi yayi yana zama kan kujera yana Fadin”Saleem,da saleema bansan yaushe zasu girma ba..”

Hajiya data cicciba tatashi dakyar tace”Sai Ranar da kuka gama akidarku ta boko kuka aurar dasu,banda lalacewa yara sun balaga sun balage agida,ammh ba wanda yayi aure,shi wanchan babban kwabo,yana chan yana yawo asama,shiko wannan banda lalaci bai iya komai,sun zauna suna ta sakarci da saleema acikin gida,Allah dai ya ganar dakai kabiru..”Tafada Fuska ba Annuri kafin ta dingisa ta Shige wani korido tana ta mita ita kadai,da kallo ya bita kafin yabi Ummi da kallo,wacce ta kwaso kololi,yana kallonta ta kalleshi ta kauda kai,tana cije baki,kamar zatayi dariya,dan mirmishi yayi yana maida hankalinsa kan jaridan dayake karantawa,domin indai wannan mganar ne,Hajiya kullum sai tayimai gori,kamar shi yahanasu yin Auren,batasan komai lokaci bane.

Hohoho Fans,yanzu fa aka Fara wasan akwai kitimulmula????tare da chakwakiya awannan KAFCHAN????Wlh Duk wacce bata karanta Malika malik ba,taga salon Soyayyah cikin daukan Fansa ba,am srry to say ansha da ita,domin Abun zaifi daukan hankali Fiye da Amanar da HAFIZ ABDALLAH RUMA Yabama HAFSAT ATTIHIRU ATTA,Kuma zai bambamta da irin Sakacin da SAKINA KABIR KANKIA,tayi ga mijinta DR SAFWAN SALE SAFANA,Kuma soyayyar ba irin wacce NAZIR ADAM GALADANCHI ,Yanuna ma NUSIBA ABUBAKAR BUNZA,bane,Kana ba irin kaunace wacce MU”AZZAM MUHD MODU,Yanunama ZAHIRA ABUBAKAR BHAGANA,bane Kuma ba irin Shakuwa da Kauna bane irin wanda SARKI ALIYU ABDULNASEER,yanuna ma Masoyiyarsa AZEEMA LAWAL BATURE,bane✌,wannan salon zai Bambamta dako wanne,wannan zuwan Salon na ACP SALEEM KABIR KUMO NE,Dakuma MALIKA ABDULMALEEK DAN KASUWA,Kada kibari ayi baki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button