MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Kan daya daga cikin Kujerun Falon Abbi ya zauna yana Fadin”Yanzu mukayi waya da Alhaji Abdulmalik yana tambayana ko kun kariso nace haryanzu baku zo ba,yace yana ta kiran wayoyinku duka bai samu ba,kakirasa ka shaidamai kun iso..”Da Tom ya amsa yana latsa wayarsa bai sanar da Abbi tun wanchan lokacin ya sagale Nombar Daddy ba,sai ya lallaba ya ciresa daga blacklist,kafin ya kirasa Yadaga suka gaisa kafin ya sanar dashi sun iso,gama Abbi zai mai mgana,cike da fara”a Abbi ya karba suka gaisa kafin su cigaba da tattaunawa,daga karshe Abbi ya tabbatarmai da cewa kada ya damu insha Allahu zai kula da rayuwar malika tamkar yadda zai kula da Da’nsa Saleem,Daddy yaji dadin haka sosai,sukayi sallama cike da Farinciki.

Mikamsa wayarsa Abbi yayi yana Fadin”Dauki kayanta ka shiga mata dashi ciki..”Jiki asanyaye ya mike aransa yana Fadin”Karyata takusa karewa,daga ramuwa na koma dan dakon kaya…”Yake fada yana daukan manyan akwatun guda biyu ya nufi dakinshi yana Ayyana yadda zai Fita daga wannan gadar zaren daya Fada.

Yana Shiga dakin nasa,ya tarar da Ummi zaune gefen gadonshi ita da Malika,da alama mgana take mata,ita kuma malika tana gyada kai,wani haushi ya kamashi kai tsaye ya wuce wajen makeken wardrope dinshi yana ijiye akwatunan,ya juya zai Fita kenan Ummi ta mike tana Fadin”ina zaka,dawo ka hadamata ruwan wanka,tayi sallah,ni kuma bari naje na hado muku Abincinku ko..”

bai waigo ba yaji ya daskare atsaye saboda wani kololin Abu dayazomai Wuya,Ummi bata Fahimci halin dayake ciki ba ta Fice tana jawo musu kofa,Juyowa yayi yana kallon Malika wacce kanta ke duke tana wasa da zabban hannunta.

Kugunshi ya kama da hannu Biyu yana Fadin”Kuturin bala”i kenan ruwan wanka?lalle ya kamata nazo nayi gaba Tunkafin na tashi daga SAI NA RAMA na koma SALEEM BAWAN MALIKA………”

Yafada yana jin Tukukin Abun har cikin ransa,Itako tana zaune,sai da mganar ta kusa sata dariya,tayi saurin Rufe baki tana rawan jiki,Ganin ya Tsuramata ido yana kallonta cikin ni ki kema dariya? lalle zaki ci ubanki yanzu kuwa..”

Bai kara kallonta ba,ya shige tailet din da karfi ya bango kofar kamar zai ballah,ajiyar zuciya ta sauke kafin ta fara bin dakin da kallo,komai neat,kamar ba dakin Namiji ba,koda yake ta lura mugun baida kazanta yanaji da kansa.

Am srry wlh yau din sai aslow,ku karanta da hakuri…

Janaf.

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

KURIKE GIRMAN AMANAR DANA BAKU,KUYI MIN ADALCI KAMAR YADDA NAYI MUKU KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

16

      Tun tana saran Fitowarshi har taga bashi da niyyar Fitowa,sai chan sai gashi ya Fito,sanye da wani Towel mai dan girma,hannunsa kuma yana saman kanshi dauke da wani karamin Towel din yana goge ruwan dake kanshi

Kallo Daya tayimai tayi Saurin Sadda kanta kasa,saboda yadda ya Fito gabadaya kirjinsa dake lullube da gargasa,awaje yana maiko Ruwa yana bayyane,Suffar karfin hannayensa ma”ana muscles suma sun bayyana waje,shima ko barayinta bai kalla ba,balle ya tankata ko yasan akwai tsayuwar mutum awajen.

Wajen Dressing morrior dinsa ya nufa,yafara Shafe jikinsa da lotsin dinsa mai dadin kamshi,har yagama yayi cumbing din sumar kanshi bata ko kara motsi daga wajen ba,Wucewa yazo yi ta gabanta zai isa wajen wardrope dinsa,kafarta dake wajen ya bangaza kamar bai gani  ba,nan ko da gangan na haushi ya hadamata Ruwan wanka ne.

Jaye kafarta tayi tana Kwabe Fuska saboda taji zafi ko kallonta bai yi ba,yakarisa wajen wardrope dinshi ya bude yana dauko kayan da zai saka,wasu riga da wando ya dauko Blank and white ne,ada yaso sanya kayan agabanta sai wata zuciya tace”Saleem in har ka bari yarinyar nant taga girmanka toh daga yau shikenan ta gama rainaka gwara ka Rufama kanka asiri kaja girmanka..”Jin hakane yasa ya kwashi kayanshi ya Shige tiolet yana wata waka na ” Babe i love u,…Babe i kiss u..Babe i need u….

Da kallon mamaki ta bisa tana gimtse baki,bai dade ba ya Fito daidai sanda Ummi tayi Knoking din kofar kafin ta turo,Da Malika taci karo zaune inda ta barta,cike da mamaki take kallon Saleem dake tsaye yana faman gyara Botiran gaban riganshi,Ganin tana mai wani kallo ne, yasa ya gimtse Fuska yana Fadin”Ummi menene naga kina hararata,ko haryanzu baki bar jin haushina bane..?

Dakuwa ta sakamar tana Fadin”Kaniyarki da Ummi,don mai garinku kumo ina Abunda na sakaka..”?Tura baki yayi kamar yaro yana Fadin”Toh Ummi don Allah bayan na hadamata ruwan wanka so take najata bayin nayi mata? itace inaga bata ra”ayin wankan..”Yafada yana zakuda kafada.

Haushi yakama Ummi ta kalli malika tana Fadin”Diyata ya baki tashi kinyi wankan ba..”?Kwalkwal malika tayi da ido zatayi mgana suka hada ido da Saleem yako zabgamata harara yana kada mata harshe ganin haka yasa Ummi ta kaimai Duka akeya tana Fadin”Fice kaban waje Maketacin miji kawai..”Dafe kansa yayi yana kallon Ummi kamar zaiyi kuka kafin yace”Kai Ummi,yanzu ni ace kamata  ban girmi da fada da duka ba? kuma ma wai agaban wannan yarinyar,plz Ummi don Allah  kidaina min Fada agabanta sai kisa ta rainani aie..”Yafada yana hade rai kyace wani ubanta.

Tsaki Ummi taja tana Fadin”Shin zaka ficemin ne,ko kuwa sai na nuna maka kalata yanzu nan..? Juyawa yayi yana Fadin”Meye Zafi lauyan Abbi,Allah baki hakuri Ummin Saleem da marwan,da munafukar nan Saleema..”Dariya ta kama Ummi ammh sai danneta har yafice ya Rufo musu kofa.

Maida kallonta tayi ga Malika tana Fadin”Meyasa baki shiga kinyi wankan ba dota..”? Dukar dakai tayi kafin tace asanyaye”Ai bansan ya hada bane,bai Fadamin ba Ummi..”Mirmishi Ummi ta mata tana Shafa kanta tace”Ok tom Shikenan barni dashi,yanzu tashi maza ki Shiga kiyi wanka kizo kiyi sallah kinji ko..? Kai ta gyada mata tana mikewa,Hannunta Ummi takama har kofar bedroom din tana Fadin”Ki saki jikin ki kinji ko? nan zan kawo miki abincin naki,ko zaki Fita Dining tare damu..? girgiza kai tayi kafin tace”Bazan iya cin komai ba Ummi..

Kallonta tayi kafin tace”Meyasa.. ?Kanta na kasa tace”Ina son naci buh ammh ko naci Sai nayi amai..”Takarishe Fada hawaye na cikomata ido,Dafo kafadunta Ummi tayi cike da tsausaya tana Fadin”Ayy srry,sannu kinji haka kowacce uwa tagari ke Fuskartan,ki daure ki dinga ci ko yayane, saboda abunda ke cikin ki,kuma koda kinyi aman ko ba duka ba,wani zai tsaya kinji..? Gyada kai tayi hawayen nata na zubowa cikin so da kauna da tsausayinta ta sanya hannu ta sharemata kafin ta bude kofar bedroom din tana Fadin

“Yi maza kiyi wankan ki Fito,kan kigama sallolinki na kawo miki Abinci..”Batayi gaddama ba ta Shigen makeken Tiolet din mai kama da Falo guda,bin ko”ina da kallo take tana jinjna tsarin bayin,ammh wannan ko rabi da kwatan tsaruwa da haduwan nata bai kai ba,wasu kwallah ne suka zubomata tasa hannu ta share,ko acikin bath din kuka tayi tayi kafin ma tayi wanka tana Tuna sanda tana Gida komai sai dai ayi mata,ammh ga yadda rayuwa ta maidata.

Sai da tagama wankan kana ta dauro alwala ta Fito,daure da tawul,akwatunta ta bude ta ciro kayan shafanta ta shafa kafin ta nemi wata doguwar rigarta Red colour,ta sanya wanda take da budadden hannh,tana tufke gashin kanta ne Ummi ta Shigo dauke da kololi abinci bisa wani katon Tire mai girma,Tana ganinta ta washe baki tana Fadin”Yauwa kefa,kinyi sallah ne..?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button