MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Merry tace”Wacce kuka zauna atare Azamfara Anty..”Cike da Mamaki Malika ta zaro ido tana Fadin”Zahra..!Sure..”Merry tana Dariya tace”Very Sure Anty..”Malika bata jira Cewar Merry ba Fito daga dakin ta Sauko kasa merry tabi bayanta cikin Sarsssafa Malika ke saukowa daga Steps idanuwanta na cikin na Zahra tana Saukowa ta karisa gareta tana Fadin”A”a Hajiya Zahra ce yau agidan Namu..? Tafada tana sakin mata murmishi lokaci daya kuma ta bata hannu suka Sarke cike da Farinciki Zahra tace”Wlh kuwa,Na sameku lafiya ya yara,ina Ayda nasan yanzu anzama yan Mata..?

Tafada cike da kulawa,Dariya Malika tayi tana Fadin”Lafiya lau wlh,yara gasunan,Ayda kuma tana mkranta basu taso ba..”Tafada ta karisawa da Zahra bisa daya daga cikin kujerun Falon suka Zauna Zahra na Rike da Aryan,da hannu tama Dose alamun ta miko mata ayyan Duka ta Hadasu ta rike Tana Fadin”Masha Allah yan Biyu kyautar Allah..”Take Fada tana musu Wasa,Malika kuma ta umarci Merry data kawoma Zahra ruwa da Lemo nan da nan ko ta Shako mata Faranti guda da lemuka da Ruwa tazo taja karamin Center Table din dake Tsakar Falon ta ijiye akai kafin ta Zuba ma Zahra Ruwa ta mikamata ta karba tana Fadin”Tanque Merry..

Sai da tasha Ruwa kana suka kara gaisawa da Malika cikin Fara”a tare da Tambayan Yaushe gamo,malika ta Tambayi Nadira,Zahra tace da tare zasu zo,Ammh Mijinta ya hana Saboda tayi Nauyi baki malika ta rike tana Dariya take Fadin Allah ya Raba lafiya Kwata kwata Malika batama Zahra bakunta ba ko ta Nuna mata wani abu ba,Ta saki jikinta Sosai tana ta janta da Hira tana tambayan mutanen gidan,Cikin hiransu ne Zahra ta Fitoma da Malika katin bikinta ta Bata tare da Sanar da ita tana gayyyatanta,cike da Farinciki Malika tace insha Allahu zata zo indai Saleem ya barta,Shuru Zahra tayi kafin ta Sulale kasa tana Rokon Zahra gafara bisa Abunda ta aikata gareta Rikota Malika tayi tana Fadin”Wlh banta ba Rikeki ba Zahra,Da ina da yarda zanyi da Tuni Mallam ya dawo dake dakinki mun zauna tare,Ammh bani da yarda zanyi,har ga Allah Zahra banta rike ki ba har azuciyata ba..”Zahra na Sharan kwallah takema Malika godiya bata jima tace Zata tafi Malika ta Hanata tace ta bari ta kira Mallam yazo su gaisa,Ita kuma taki tace tafiya zatayi bataso tayi Dare ahanya,suna cikin mganar ne sai ga Saleem ya Shigo Shida da Ayda yana office ya samu wayar Shugaban mkrantan su Ayda an tashesu tun dazu ammh har yara sun gama watsewa Ba”a zo an dauki Ayda ba kuma yayi ta kiran Wayar Malika bata daga ba itako Zuwan Zahra ne ya Mantar da ita komai,kuma wayarta ta barota asama…

Shima yayi mamakin ganin Zahra,ammh sai ya Shanye mamakin ta hanyar Hade ransa itama Zahra gabanta na Faduwa ta duka tana Gaisheshi adakile ya amsa yana Shirin Haurawa sama Malika tace”Mallam zahra fa gayyatanmu tazo yi zatayi aure upper week insha Allahu..’Bai waigo ba yace”Allah ya sanya alheri..”Daga haka ya Haye sama ya Shige dakinsa ko waigo,duk da Malika bataji dadi ba,ammh Sanin Halin gogan nata sai ta barsa,itama Zahra haka taji ammh sai ta Share ta bar Abun duk laifinta ne,kuma bata ga laifinshi ba,don ta chanchanci Fiye da Haka…

Girman Ayda ne da wayonta ya bata Mamaki haka ta dauketa tana Tambayanta Sunanta tace”My Name is Fatima Saleem kabir kumo,know as Ayda..”Baki Zahra ta rike tana mamakin Ayda Malika na musu Dariya domin Ayda akwai kwanya kuma dayake wani lokacin Duka iyayenta basu mata mgana da Harshen Hausa sai dai Turanci gasu Merry ma basu mata mgana da Hausa Sosai dat why tatashi dashi abakinta koda ta Shiga mkranta Abun bai bata Wahala sosai ba.

Zahra bata tafi ba Sai da Malika ta matsamata ta ci abinci kana ta rakota har Wajen mota suka rabu bayan Malika ta karbi Digit din Zahra da alqawarin insha Allahu zata lallaba Mallam zata bikinta da Yardan Allah,Zahran Tadai jita je,ammh ganin Yadda Saleem din yayi batayi tsammanin Zai Barta tazo ba,da zata tafi tabama Ayda 5k ita dasu Ayyan bayan Tarin tsaraban data zo musu dashi na Chaculate,suka rabu cike da kewa har motar Zahra ta bar Haraban gidan Malika da Ayda da su Merry suna Daga mata hannu.

Koda Malika ta dawo cikin gida Saleem bai mata mganar Zahra ba itama Sai ta Share bata Tankashi ba har Washegari kanzil bai Ce mata ba,kuma yana ganin Ayda ta saka Rigima da safe ita sai an saka mata chaculate din da Anty Zahra ta kawo mata cikin basket dinta,Yana jinta tana Fada da ita kan Shan zaki,sai ma tasowa yayi da kanshi ya kwashi Chaculate din ya Zuba mata cikin jakarta ya kama hannunta Suka Fice daga Dakin,da kallo Ta bishi kafin Ta murmusa,domin inda sabo ta Saba da Halin Miskilamcin Saleem.

Har Bikin Zahra Ya matso Saleem bai cema Malika komai ba,Ana jibi bikin Saleema ta kirata awaya, tana Tambayanta in zataje Zata zo gobe sai su Wuce Kanon Tare,Malika bata yanke mgana ba Sai da Saleem ya dawo da daddare take Tambayanshi Zuwa bikin bai ce mata komai ba,balle ta saka Ran Zuwa har Washegari Ta kira Saleema tace bazata samu Zuwa ba,Suka Rabu da Saleema kan zata Abuja aranar jirgi zata biyo gobe Direba zai kaita Kanon Tunda dai Tayi Ra”ayin Zuwa.

Sai da Daddare har sun kwanta yace gobe ta Shirya Zasu tafi Abuja gabadayansu Suyi Hutun karshen Mako daganan sai tabi Saleema su Tafi bikin Murna ta kama Malika har Sai da tayi tsalle ta Rumgumeshi tana Murna,gari na wayewa,koda 11 tayi tayi musu Abuja dama already ta kira Saleema tace ta jirata gatanan Zuwa tana Zuwa basu tsaya Ba,Direba ya kwashesu Zuwa kano,Ayda ne ta tsaya wajen Ummi da Babanta,Merry kadai Malika tataho da ita,saboda Kula dasu Aryan,Dose kuma an barta Wajen Ummi.

Koda Su Malika suka Isa gidan Su Zahra,Hatta da Momi tayi murnan ganinsu,balle ma Da Malika ta bata 50k Gudummuwar biki,tayi ta mata godiya  Sosai ballatana Zahra da Nadira Wadanda suka Rasa ina zasu sakasu saboda Murna da Farinciki kamar yadda Saleema ke Fama da ciki Haka Nadira ke Fama dashi Haihuwa yau ko gobe,Zahta tayi kyau Sosai in ka kalleta baka kirata bazawara ba,Saboda tana kyan jiki,kuma batataba Haihuwa ba,La”asar nayi aka kai amarya gidan Ya Nadir dake kusa da asibitin Murtala,tare ya Hadasu da matarsu,Zahra tasha Fada da Nasihan Hakuri da juriya,Zafin kishi kuwa Tunkafin wani yayi Mata Fada Duniya tayi mata,shiyasa yanzu taWatsar da komai ta kama Allah ta Shiga da Zuciya daya cike da alheri.
.
Su Malika basu samu dawowa Aranar ba sai washegari Saboda Dare yayi musu Gidan Nadira suka kwana,sai da Safe suka kamo hanyar Abuja bayan Sun Biya gidan,Zahra sun mata sallama suka Rabu cikin kararramawa da Farinciki,tare da alqawarin in Saleema ta Haihu zasu zo,suma sukace in Nadira ta sauka su Sanar dasu insha Allahu zasu zo.

Ranar da suka dawo sai yammah Suka Shigo shiyasa Su Malika basu koma katsina aranar ba Sai Washegari suka Wuce da Safe ita kuma Saleema jirgin yammah Tabi ta koma Don taso Sadiq ya barta ta zauna Har ta haihu ya nuna bai yarda ba kamar ma ya nuna achan yakeso ta Haihu,Allah barshi sai aturo wacce zata zauna da ita,ammh Bashi da Ra”ayin Ta dawo gida wanka,Dole ta Hakura ta koma bayan Ummi ta bata bakin in Ta haihu ita zataje ta zauna mata,Hajiya tace gata itama zata Dole ne,jin haka shiyasa Saleema ta koma Cikin Farinciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button