MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Sai da yamma chan Sai ga Sadiq ya iso bai dade da isowa ba Sai ga Uban gayyan ya iso cikin motarsa 4 matic ya kara kiba da Fari kamar bashi ba,daka ganshi zaka Fahimci ya samu kwanciya hankali da Natsuwar Zuciya,shiko ya marwan sai chan dare ya dawo yana chan Tare da Wasu abokansa wadanda ya Saukesu a hotel,sai kalilan ne ya Saukesu agida suna tare dasu Saleem da Sadiq suna hira kamar ansan juna,Duk da Shi Saleem bamai yawan mgana bane,kuma yawancin abokan ya marwan din ba baki bane agaresa so Duk yasansu sosai.


Karfe 2:30 na Ranar Asabar Aka Daura Auren MARWAN KABIR KUMO Da amaryansa JODA MUHAMUD MALUMFASHI Wanda aka Daura shi kan Sadaki Dubu dari biyu lakadan ba ajalan ba,Daurin Auren daya samu Hallartan manyan baki daga kowani bangare kama daga barayin shi kanshi Uban gayyah,sai Saleem danashi Harta Sadiq Ba’a barshi abaya ba Uwa uba kuma Abbi da nashi Tawangan ga tawangan Sauran Daurin Aure guda uku Wanda suma ta kowani bangare sun Hallarcin Wannan Daurin Auren daya Tara Dimbim Jama’a.

Maman Abba ta cika alqawari ta biyo Baban Abba sunzo Tare Wanda Sai dai Malika ta ganta kwatsam haka Suka Rumgume Juna Suna murnan ganin Juna,haka amarya Joda Wacce aka tsarama kwalliya ta Nuna tsara tana Sanye da Wani leshi mai kalan Blue black da Ratsin kwalliyar pick,sai mayafinta ma pick da jakarta da takalmin kafanta,sosai taji dadin Zuwan maman Abba,haka ta Rumgumeta tana mata maraba da Zuwa,Ita kuma Tana mata Tsiyan Amarya tasha kamshi .
 
Ana gama Daura Aure da Awa daya bayan sungama sallaman bakin da zasu Tafi sai kuma suka koma Shirin komawa Abuja da amarya,wacce aka Dauketa daga nan gidan data ke party Zuwa Family House din Su Daddy Inda Hajiya ke taronta ita da Danginta domin suyi Bankwana,lokacin ita kuma Malika suna Tare da Maman Abba ta rakota kofar gida Baban Abba yace ta Fito su Wuce,shine ta roki alfarman ya dan mata lamani taje tama Hajiya Allah Sanya Alheri Tunda babu Nisa,dakyar ya yarda Ammh da Sharadin bazata Dade ba.

Malika na Sanye da Leshi ne mai maroun colour wanda keda kwalliyan Ja ajikinsa,Riga da Sikat wanda ya Fito da ita Sosai itama an mata kwalliyan Duk da ba cika mata akayi ba,ammh kam kallo daya zaka mata ka fahimci dama chan tana da Sirrin kyanta,mayafin data yane kanta Dashi Ja ne,mai wasu Ratsin Duwatsu masu daukan ido,hakama takalmin kafanta baki ne mai daurin igoyoyin ja ajikinsa kunsa mutuniyar akwai son Takalma masu Tsini da Tudu.

Ayda ce ahannunta Wacce itama taji adonta cikin Riga da wando,Rigar Pick ce,wando ko na Jeans ne baki sai wani takalminta mai kyau da Tsari pick colour kanta ko yasha kitso wanda aka sanya band din kanana aka kama mata Daki daki,Sun Fito da Maman Abba zasu koma Family House din su Hajiya,duk akwai maza sosai akofar gidan da kuma Tarin hadaddun motoci,.

  Saleem ko da suke jingine jikin motarshi Shida Sadiq da wani abokin ya marwan mai Suna Hamza,sai Baban Abba,dukkansu sunci Dayan Shaddodi Farare dinki Muhammed ne wanda ya dace dasu Samarin zamani,Lokacin da su malika Suka Fito hankalinsa na bisa waya bai gansu ba,Sai da Sadiq ya tabosa kana ya Dago ya Sauke ganinshi kan malika tana tafe sabe da Ayda suna hira da Maman Abba tana sakin mata kayatattacen mirmishin din,Wani yam Saleem yaji lokaci daya yaji Ranshi ya baci ballema Daya ga da Sadiq din har dabHamza sun kura mata ido,yana ji Sadiq na gayama Hamza mai jan gyalen nan matar Acp ne.

Tuni Ran maza ya baci,idanuwansa har sun kada saboda kishi wayarsa ya Cigaba da dannawa kamar babu Abunda ya Dameshi Sako ya Turama malika kamar haka Ki tsaya a inda kike ganin zuwa,ban Amince ki kara ko taku daya ba. Tana jin Shigowar sako Dama wayar na hannunta tana Danna Sreen din Sunanshi yana Wayo ta saman Wayanta Dauke da Sunan data Sanya mai * ABBU AYDA* Mirmiahi tayi kafin ta Shiga sakon da ya Rubuta ne ya Daure mata kai ta Dakata da Tafiya tana waige waige ganin Haka yasa maman Abba tsayawa tana Fadin”Matar Acp lafiya kuwa…? Kowani kike nema..?

Miyau ta Hadiye kafin tace”Kinga mallam ne yamin Sako yanzu yace na jirashi gashinan Zuwa,kuma inata waigo banga ta inda zai bullo ba..”Tafada tana Raba ido,mirmishi Maman Abba tayi kafin tace”Baki lura dashi ba gashi ta bayanmu yana Tahowa aie…”Da hanzari Malika ta juya sai ko ta hango Saleem yana takowa wajensu cikin takunsa na isa yadda taga yanayin Fuskarshine Sai da Firgita,cikin jin kai ya kariso garesu maman Abba na gaisheshi ya amsa cikin sakin Fuska kafin ta danyi gaba,Malika ta kalleshi taga ya Hade rai duk sai ta Daburce cikin sanyinta tace”Mallam ina yini..”

Bai amsa ba ya mika hannu yana Fadin”Bani ita Kirjin biki…”Yafada kai tsaye yana kallonta batayi gardama ba Tamikamai Ayda ya karbeta itako tana ta wangalemai baki dama Tunkafin ya karbeta bai kalli malika ba ya Juya yana Fadin”ki koma ciki malama ban amince kije ko’ina ba,yanzu zamu Wuce Abuja in kuma baki gama bikin bane,in ngama ganin Ayda zan aiko miki da ita ciki..”Daga haka ya juya ya Fara Tafiya,Kunya da Haushi suka kama Malika tayi jagale tana kallon Bayan Saleem kafin ta saki ajiyar Zuciya ta karisa kusa da maman Abba tana Sanar da ita Yadda suka yi da Saleem,dariya tayi mata tana Fadin”Kishi ne ya taso karki damu bari naje kila in yagama dama ya biya dani ko Sharp sharp ne mu gaisa..”Jin haka yasa sukayi sallama dama Tun aciki malika ta bata kayan biki musabaha sukayi kafin su Rabu malika takoma cikin gida itakuma maman Abba ta Nufi Baban Abba wanda har ya Shiga mota Shida Abba ita kawai suke jira.

Malika ko data Shiga cikin Abun sai yaki barin Ranta sai da tayi kuka aboye,Kafin ta dauro alwala bayan ta Wanke Fuskarta tana cikin sallah ne kawayen amarya suKa Dinga zuwa daukansu suna Fadin gashi chan za”a tafi bata damu ba,don ko da ta idar sallar bata Fita zaman ta tayi tana mamakin mallam,shifa yake koyar da ita hakuri ammh yau gashi laifi kadan ya Riketa dashi yakasa yimata Afuwa.

Tanan zaune sai ga kiranshi kamar bazata Dauka ba sai dai ta daga kiran cikin Gadara yace”Kina ina..? Ranta acunkushe tace”Ina cikin gida..”Kifito ki karbi Ayda mu zamu Wuce ne..”Daga haka ya yanke kiran,Wayar tabi da kallo kafin tatashi ta Tafi,Abunda ya kara mata mamaki mikomata Ayda Yayi ya juya zai Shiga mota sai itacene tace”Mallam ni wata mota zan Shiga..? A karkarce ya kalleta kafin yace”Zuwa ina..? Kwallar har sun Fara cikamata ido tana kallonshi tace”Zuwa Abuja..”Tana Fada cikin Sanyinta,Ganin yadda tayi ne yasa ya sauke ajiyar Zuciya yana kallonta akarkace kafin yace”Au yau zaki koma kenan..? Ni zatona sai kin sake Wani satin kinga ko sallaman Jama’a kya taya Hajiya..”Jin Abunda yace ne yasa taji Zuciyarta ta tsinke batamai mgana ba ta juya,ganin haka yasa ya Sha gabanta yana Fadin”Ki Shiryo kayanki mutafi don Tun dazu su ya marwan da tawagar amarya Suka mika..”

Bata kalleshi ba ta mikamai Ayda ita kuma takoma cikin ta dauko karamar jakarta bayan tama matar gidan Sallama Tunda anan suka zauna Tsawon kwana uku,Koda ta Fito Shida Sadiq ta gani yanzu,ba don Sauran kayanta na gidan Su Daddy ba,da Saleem baida niyyar biyawa,Allah dai ya Dorata akanta ta Biyama tama Hajiya sallama suka kwashi kayansu ita da merry,shi kuma ya bude musu booth suka saka kafin su Fada mota su dau hanyar Abuja.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button