MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Saleem dake gefe shima kamar yayima Daddy kwallah,saboda yadda suka bashi tsausayi,baisan sadda yasaka Tattausan hannunshi yana Sharema Daddy kwallah ba kafin ya koma ya dago Malika yana kallon cikin idanuwanta cike da wani yanayi wanda Shikadai ya barma kansa,sani itako,runtse idanuwanta tayi tana jin wani Fargaba acikin zuciyarta Hannaunta ya damka ya damke da karfi yana Fadin”Na karbi Amanarka Daddy da zuciya daya kuma nayi maka alqawarin ni Saleem kabir kumo zan kula da Malika Fiye da yadda zan kula da kaina,zan tarbiyarta da ita kamar yadda uwa zata tarbiyarta da yarta,zan bata kulawa tamkar yadda yaya zai kula da kanwarsa,Sai dai Abunda na gaza zan barma Allah sauran..”Ya fada yana hada duka hannunsu su uku ya damke atare.

Daddy na hawayen Farinciki yana ma Saleem godiya kafin ya kalli Malika yana Fadin”Ki tashi kije ki Shirya babby,daganan ki tahomin da mukallayen gidan nan dana motocin nan,tare da takardan sakamakon likita game da cikin da kike dauke dashi…”Dam!Gaban saleem ya buga,da rawan baki ya kalli Daddy yana Fadin”,Ci..ki….Ma…Li….Ka…..Ke…Da…Shi….”?

Yafada bakinsa na rawa,gyada mai kai Daddy yayi yana Dafa kanshi daidai lokacin da Malika ta mike tana shesshekan kuka ta Fice,Wani yanayi Saleem yaji sai ya samu kanshi da kurama bayan Malika ido,yana Jin wani iri acikin ranshi,ciki kuma? kai yanzu wai har ya isa yin ma mace ciki…? Bai gama mamaki ba,yaji Daddy na gayamai jikin da malika takeji,gyada mai kai kawai yakeyi yana kiyasta abubuwa da dama cikin ransa,gefe na zuciyarsa na Farinciki ammh kuma wani shashe na fadin”Koda cikin sai ta ci ubanta,ai babu daga kafa yarinya…”

Ba Malika takawo makullyan ba,Hajiya binta ta kawo,shiko Daddy ya hada duka ya damkama Saleem yana Fadin”Duka kyautar danayi maka,da zuciya daya nayi maka shi,saboda haka gasunan na maida maka,sai dai in bakaso ka kyautar dasu,duka mallakinka ne..”Girgiza kai yayi yana bin takardan sakamakon Cikin Malika yana Fadin”Bazan kyautar ba Daddy,ko wanchan karan dana dawo dashi rashin sani ne,ammh wannan karan na karba kyautan naka da hannu bibbiyu Allah ya saka da alheri ya kuma baka lafiya..”Da Ameen ya amsa yana ta sakamai albarka.

Malika ko tana chan tana ta kuka kamar za”a zareta ma rai,Hajiya binta ke ta lallashinta,bata chanza kaya ba da wannan bakar dogowar rigar hajiya ta riko hannunta suka nufo dakin Daddy,yayinda da Su Dose suka fara Fita da manyan akwatunanta guda uku suma jikinsu duk yayi sanyi na Tafiyar madam dinsu,wanda suna zaton wannan karon bada su za”a tafi ba.

Gaban Daday da saleem ta durkusar da ita tana Fadin”An gama hada komai,sun Fita da kayan zuwa waje…”Saleem najin haka ya mike yana duba agogon hannunshi,biyu saura na rana,Kallon Daddy yayi yana Fadin”Toh shikenan Daddy mu zamu Wuce kada muyi dare bisa hanya..”Kallonsa Daddy yayi yana Fadin”Haba Saleem kamar na koranku kubari kuci abinci kuyi sallah sai ku dau hanya ko..”Saurin cewa yayi “No Daddy karka damu zamu tsaya bisa hanya muci abinci muyi sallah,bani so muyi dare ne…”

Shuru Daddy yayi kafin yace”Shikenann Saleem Allah ya kiyaye hanya,ngd sosai ka gaida su Kumo din Allah ya kaddara saduwa…”Da Ameen ya amsa yana mikamai hannu suka sake musabaha kafin yafara taku zai Fice daga Falon,da hanzari Daddy yafara tura kekenshi zuwa cikin bedroom dinsa yana fadin cikin wata irin murya..”Binta ki Fita da Malika daga dakin nan,bani son ganin tafiyarta don Allah…”Yafada yana tsiyayan hawaye,Jin haka yasa malikar kwace jikinta dagana Hajiya binta ta bishi da gudu ta rumgume bayanshi tana Fadib”Wayyo Allah!Daddy na…..”Take Fada tana kuka kamar zata shide,bai saurareta ba,yana share kwallah,ya cigaba da tura keken zuwa cikin bedroom dinshi yana Fadin”Kije Babby,insha Allahu nan gaba zaki zama Abun alfaharin ya”yanki da al”ummah baki daya koda bana raye,kije Allah yayimiki Albarka yakuma zaunar dake lafiya agidan mijinki…”Yafada yana wani kuka na zuwarma,tura kofar bedroom din nasa yayi ya shige yana Rufe kofar….

Zuciyarsa ke bugawa da karfi tana Fat!Fat!Ammh kuma gefe daya Farinciki yake na ganin ya sauke wannan Nauyin dake kanshi wanda ke damunshi Shekara da shekaru,na damka amanar Malika hannun wanda zai gyara mata rayuwarta daga Duhu zuwa haske,kuka yake yana Fadin”Allah na tuba Allah ka yafemin ya Allah..Astagafurrillah.!”Yake Fada yana daga hannunshi sama hawaye suna zuraromai..!

Wayyo Allah!wlh Sai  da nayi kuka????Wannan page din ina rubutashi inaji yana tabamun zuciya sosai…Kai Allah kadamu da kyakyawan kaddara,ka kuma bani damar yin Nadama cikin lokacin irin na Daddy,ba sai lokaci ya kuremana ba kamar Fir’Auna..,Allah ka tsaremu Ameen

Nan wajen Malika ta Fadi tana gunjin kuka,Hajiya binta ne ta kamata tana lallashinta ita ta rikota har suka sauko Falon kasa inda Su Atika da Dose suke tsaye suna share kwallah tsausayin Madam dinsu da kewarta,Kallonsu takeyi sai taji yau sune fa yan”uwanta don dasu ta saba,tayi musu tsawa,tayi musu Fada,ta wulakantasu,ta dakesu,ammh sai gashi yau suna kuka don zata rabu dasu,ashe ba Farinciki zasu yi ba,don zasu rabu da ita ba..? batasan sadda tatafi da gudu ba ta fada jikinsu tana kuka ba,Suma kamata sukayi suka Rugume suna Fadin,”Plz madam we are going wit u”

Girgiza musu kai takeyi kafin ta dago tana share musu kwallah dukkansu kafin tace”No,stay here…buh i promise u zan zo na tafi daku insha Allahu kunji,stop craying Sweetheart ,and tanque very much For u Time,May god bless u Ameen…”Wani kuka ne ya kwace mata tayi baya da Sauri tana daga musu hannu.

Gaban Hajiya taje ta durkusa tana Fadin”kiyafemin MOMMY…”Take Fada kanta sunkuye tana kuka,Wani tsausayi da sanyi ya kama Hajiya ta duka ta dagota tana Share mata kwallah tana Fadin”Bakomai yata,dama banta ba rike ki ba,Kisani tamkar yata joda haka na daukeki,shawarata gareki Shine  kibi dukkan Abunda Mijinki ya umarceki,komai kike bukata ga iyayen mijinki nan,ki tambayesu komai kike bukata zasu baki shi, Abu na karshe ga waya nan,zamu dinga kiranki muna tambayanki lafiyanki,daga karshe don Allah malika ki kula da kanki da kuma cikin dake jikin yanzu dai baki da kowa sai Allah sai mijinki kinji ko? .

Fadawa jikinta kawai Malika tayi tana kuka take Fadin”Naji Mommy,kuma insha Allahu zanyi amfani da shawaranki Nagode sosai..”Take Fada tana share kwallah,Megadi ne ya shigo yana sanar dasu Yallabai yace Madam ta Fito su Tafi,jikinta ba kwari ta daga kafa ta fara tafiya tana karama Falonsu kallon Sai watarana,ahaka har ta Fice bata waigo ba itama hajiyar sai taji kwallar na silalo mata,Su Dose ko faduwa sukayi suka kamkame juna ita da merry suna kukan tsusayama madam dinsu,don daga ganin fuskar mijin nata baida imani,balle sun tsorata dashi Tun kusa kashe musu madam dinsu da yayi.

Cikin kukan ta Fito tanayi tana sharbe kwallah,nan ta iske joy da peter tsaye suna zare ido,kallonsu kawai tayi sai tasamu kanta dayi musu mirmishi tana daga musu hannu,saleem na tsaye jingine jikin motarsa yana kallonta wani wawan tsaki yaja kafin ya kauda kai,jikinta asanyaye ta kariso gabanshi tana rawan jiki,kallon sama da kasa yayi mata kafin ya bude baki yace.

“Ke…”Afirgice ta dago idanuwanta da sukayi jawur saboda kuka tana kallonshi Ware mata ido yayi yana Fadin”Uban wa zaki bi da wannan dan Figigin mayafin…? Yafada yana jefamata wani banzan kallo,baya taja tana saka hannu tana goge kwallar da suka zubomata takasa cewa komai,ganin ta maidashi wani mahaukaci ne yasa ya daka mata tsawa yana Fadin”Ke bada ke nake mgana ba,dont force me to mention my First statement,wlh bazaki ji da dadi ba..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button