MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Yadda ya saki baki ne yana kallonta yabama Joda dariya,wanda tana ma gaisheshi bai ji ba,yana chan ya saki baki yana bin Malika da kallon sha”awa bata gama dariyan ba taga ya ijiye lodojin hannunshi asaman cafet din daki ya ware ma Malika hannu yana Fadin”Oya YAR AMANATA.. Come here…’Yake fada yana sakin mata wani kayatattacen mirmishi.

Itako kunya duk sai ya kamata ganin Joda tsaye,ganin taki zuwa ne yasa ya isa gareta da sassarfa ya Rumgumeta kam yana Fadin”Idanuwanki suna cike da kewata,ammh kinki ki Nunamin yadda kikayi kewata ko? Yafada yana tusa kanshi jikin Wuyanta

Da hanzari joda ta bude kofa ta Fice tana yar dariya ita kadai.

Momyn ladingo..

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

22

Malika taga Fitan Joda da sauri Abun sai ya bata dariya,ganin tana dariya ne yasa ya dagota yana kallonta Tunkafin yayi mgana Malika tace"Joda ce ta Fita da sauri.."

Ido ya ware yana kallonta kafin ya kalli kofa yana Fadin”Wai dama ku biyu ne adakin nan..? Yafada kai tsaye yana shafa gemunsa,Dariya yabama malika sai da dan dara,Kumatunta ya shafa yana Fadin”Eh mana,dole na tambayan kinsan ke kadai nagani..”Mirmishi ta sakarmai kafin tace”,”Ai tama Fice Abunta,Sannu da zuwa..”Yana zama gefen gado yace”Yauwa ya hanya? kun dawo lafiya,ya karin hakurinmu..?

Yake Fada yana rikota bai mata mazauni ako’ina ba sai akan cinyarsa,Yana zaunar da ita,Kanta na kasa ta zauna tana Fadin”Mungode Allah..”Kanta ya aza bisa faffadan kirjinsa yana Shafa kanta yake fadin”Allah yajikan Daddy da rahama yasa yana kyakyawan mtsayi..”Da Ameen ta amsa muryanta asanyaye

Sun dade ahaka kafin ya tada ita zaune ledan Takeway din dayazo dashi ya dauko yana riko hannunta yake Fadin”Muje falo,na gaisa da joda,sai kuma naje nayi taking shower ko..?gyada mai kai tayi kafin ta rike hannunshi gam,su Fice daga Dakin yana rike da ita….

Joda na zaune suka Fito mikewa tayi tana dariya take kara gaishe da Saleem,ledojin hannunshi ya mika mata yana Fadin”Yauwa Hajiya Joda,barka da zuwa garin zamfarawa,Kiyi hakuri fa dazu ban ganki ba,kinsan Abunda akace amanace gareka toh dole sai ka kiyaye,kinsan Malika amana take awajena,shiyasa idona ya rufe bana ganin kowa sai ita..”Ba Joda kadai ba hatta malika sai da ta murmusa,karban ledan Joda tayi tana Fadin”Eh lalle naga alama,gaskiya acigaba da kularmana da Amanar Daddynmu muna son haka..”Tafada tana yar dariya

Mirmishin yake yayi yana Fadin”Au kema kin bada goyon baya kenan,? Da hanzari Joda tace”Sosai ma..”Kada kai yayi kafin yace”Toh Allah bani ikon Kula da Amanar taku,ammh itama yar Amanar naku bata jin mgana,tacika taurin kai..”Yafada yana kallon Malika adage,hannu daya kuma yana Sosa dan sajensa,Dariya Joda tayi tana kallon Malika data shagala da kallon Saleem saboda yadda yayi mata kyau cikin Uniform dinsa na kakin yan sanda????

Taimakama Malika yayi ta zauna bisa kujera kiss ya sakarmata a goshi kafin ya mike yana Fadin”Let me go and take Shower na dawo kinji..? Gyada mai kai tayi kafin tace”Toh…”bai kara mgana ba ya juya cikin takunsa na isa ya nufi dakinsa,daidai sanda wayarsa dake aljihu ta dau Tsuwan Neman agaji,Tana gani ya ciro wayar daga Aljihu yakara akunne daidai sanda yake Tura kofar dakinshi ya Shige tanajin sanda yake Furta”Amin Afuwa Madam..”

Wani Yam taji acikin ranta,Nan da nan Zuciyarta suka raya mata abar sonshi ce Ta kirashi ma”ana amaryanshi,wani takukin abu takeji yana mata wayau bisa kirjinta,har sai da wasu siraran hawaye suka zobomata tayi hanzari sanya hannu ta share tana kokarin daidaita kanta,lokacin dataji sawun tafiyar Joda wacce ta Fito daga kichen dauke da Filet din data Juye musu abincin da Saleem ya taho musu dashi.

Waina ce da miya sai Ferfesun kayan ciki,wanda shi din nema malika taci ba laifi tasha ruwa takoma tana maida Numfashi,itako Joda wainarta taci takoshi tanayi tana kallon katon talabijin dake Falon inda ake haska Shirin akushi da rufi daga Tashar Arewa24,tuwon Shinkafa ake koyawa nan da nan Joda tace”Anty malika gaskiya yakamata bayan kin haihu ki zage ki koyi girki ba dadi ace kullum ya Saleem na bisa hanyar Restaurant zuwa Siyo abinci alhalin kowa yasan yana da mata..”

Tafada tana kallon Malika,wacce tayi zuru ta kurama Talabijin ido,Abunda Joda ta fada gaskiya itama tayi wannan Tunanin ammh rashin wanda zata fadamawa ne yasata tayi Shuru da bakinta,ammh Tunda har Joda tayi mgana bari tace wani abu,Cikin sanyinta na kullum tace”Tabbas hakane Joda na dade da wannan Tunanin araina,arayuwata na rasa abubuwa dadama daza”ace mace ta gari ta mallakesu,shiyasa Mallam zai kara aure..”Tafada tana Sharan kwallah,Ido waje Joda ke kallonta kafin tace”Wani mallam din..? Malika na kallonta tace”Saleem…”da hanzari Joda ta tsame hannunta daga Filet din wainar datakeci tace cikin tashin hankali..”Ki bari don Allah,? Wlh bansani ba yaushe zai yi auren? kuma wata yarinya ce..?

Malika na Yamutsa fuskar takaichi tace”Karki ga laifinshi Joda wlh yayi kokarin sosai,samun Namijin da zai zauna dani Awannan zamanin wlh irinsu sunyi karanci,Bansan yaushe bane bikin ammh kamar Ummi tacemin wata uku akasa yanzu kuma da gayamin za’a kai wata Tunkafin rasuwar Daddy..”Tafada cikin rauni,Cak joda ta Dauki Filet din wainarta ta maida kichen taje ta wanko hannayenta tadawo falon kusa da Malika ta zauna tana Fadin”Anty Don Allah kidaina damuwa,Kinga Fa halin dakike ciki,kada kibari wannan mganar tasaki cikin damuwa..”Mirmishin yake Malika tayi kafin tace”Kinga na damu ne Joda? ni tsorona Daya yadda rayuwata zata dawo acikin gidan da zarar mallam ya samu nasarar auren wacce yakeso..”Zuru Joda tayi mata da ido kafin ta sanya hannu ta dafa kafadanta tana Fadin.

“”Wlh bazaki Wulakanta ba Anty malika,haba aiko yadda yaya Saleem ke miki dagani yana cikin mayen sonki ne..”Idon Malika na maiko tace”uhmm haka kike gani dai,ammh babu soyayyata acikin ranshi sai dai tsausayi da kuma girmama girman Amanar da Daddy ya barmai..”Wani Shu’umin Mirmishi Joda tayi kafin tace”Haba Anty malika Kifa daina gaddama akan wai yaya saleem baya sonki…? Ai tsausayi shine ginshikin Soyayyaha,Tunda dai yana tsausayinki toh ina mai tabbatar miki da cewa yana Sonki har cikin ransa..”Tabe baki Malika tayi batayi mgana ba,sai ma ta yunkura ta mike tana mikama Joda Filet din Ferfesun kayan cikin data ke ci tana Fadin”Sakamin shi A fridge gobe da safe zanci..”Mikewa joda tayi tana Fadin”Toh Allah ya kaimu,ammh yakamata kima yaya Saleem mgana ayo cefene sai na dinga girkawa ni,ya huta yawon siyo abinci..”.

Malika na tafiya zuwa hanyar dakinta tace”Ki mai mgana mana..”Tafada cikin Kufula saboda harta Saleem din saboda kishi haushinsa takeji yanzu,Da kallon tsausayi Joda ta bita kafin ta kada kai zuwa kichen tana Fadin”Insha Allahu Anty malika zaki Farinciki arayuwarki,domin nima sai inda karfina ya kare na ganin kinyima sauran mata zarra agidan mazajensu.

Shiko Saleem yana Shiga daki yafada gado suna cigaba da waya da zahra,wacce ke mai kukan Shagwaban Tun jiya ya manta da ita,shi dariya ma ta bashi,tana wani sangarta duk don ta burgeshi,shiko acikin ranshi yana Fadin”Duk sangartanki naga Malikata????,ammh azahiri sai ya biyemata yana lallashinta da bata bakin tarinka hakuri dashi tasan yanayin aikinshi ko yayarta ta gidama hakuri take dashi Tunda tasan yanayin aikinshi,Zahra batasan dalili ba daya ambaci Malika sai taji ranta ya baci,ta alura akomai akace sai yace Malika kaza,abun na bata haushi Duk da ta riga tasan yadda badakalan aurensu ya faru,wanda abaya taso ta taso mai da mganar tana tambayanshi,Daure mata Fuska yayi yace kada ta sake tafara Shiga hurumin da ba nata ba,bayason rainin hankali sam,kuma a yarda ya nuna mata,bazai dauki ta raina mai malika,don zata samu matsala babba ma kuwa itako Zahra arawan kanta tagananin Malika bata da wani anfani wajen Saleem Tunda ya aureta ya saketa adaren Farko,sai daga baya ne ya dawo da ita,akwai ko ahaka tayi mata zarra????????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button