MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Tana shigowa sai ta Wuce dakinta tashige tiolet taci kukanta kafin ta wanko Fuskarta ta Fito,cikin kichen din tabi su Maman Abba,wadanda ke ta aikin soye soyen miya da naman kaji bakin da zasu yan kawo amarya Tunda su ba taro zasuyi ba,Abunda yayima malika dadi da Hajiya binta ta mata waya tace Goggon daga malumfashi, da Wata zaliha wacce take ya ga Daddy zasu zo mata gobe,Ho zo kuga murna har bakinta yaki Rufuwa ko bakomai ashe dangi ma suna da ranarsu,gashi zasu suyi mata rana lalle duk wanda baisan darajan dan adam ba,yana tare da Nadama duniya da lahira.

Nan take tambayan joda wani abu ne ake sanya ma Hannu yayi ja,Mallam yace tasaka,Maman Abba da joda suka sanya dariya harda tafawa,Joda ne tace”La Anty Malika Kunshi fa yake nufi..”Maman Abba ta karbe da cewa”sha kuruminki dama nayi ma wata Mami mai lalli na kusa damu mgaba tana kitso tana kunshi,so gobe zan kawota tazo ta Chanchare min ke,yadda Acp zai ka rikice yakasa gane Amarya da uwargida..”Dukkansu suka sanya dariya suna cigaba da aikinsu suna hira ita kuma malika na zaune tana tayasu da hira,gefe daya kuma tana sakin mirmishi ita kadai.

  ***
Koda Saleem ya isa Abuja ya tarar da gida cike da Yan”uwansu wadanda suka zo daga kumo,maza da mata,wadanda zasu tafi daurin aure gobe,Koda yaje Sadiq ya gaji da jiransa har yayi Fushi ko takanshi baibi ba,saboda haushin dayake bashi na yadda yake wani rawan kafa,akan aure,Abun takaichi ma sai mutum yaga yadda Su Nadira suka maidashi kamar wani kakansu komai suke so shi suke kira suna rawan kafa gayamusu shi kuma yana rawan baki sanar dashi,harda mai masifan kin zuwa da Wuri su wuce kano ayau su samu Dinner dasu Zahra suka Shirya,wani dogon tsaki yajama Sadiq bai kara tankanshi ba,ya Cigaba da laluban nombar wayar Malika yana so ya sanar da ita Ya iso lafiya.

  Abokan wasansu kuwa sai tsiya suke mai,suna fadin yayi rawan kafa,da Son mata ko kuma suce mai jaraba ne,Akanannan Shekararunsa har yatara mata biyu,Dariya kawai yake musu yana Fadin”Kunga alamun cewa Saleem lafiyayye ne,don da bani da karfin mazantaka da ba’a kara bani wata matar..”Rufe baki sukayi suna sunne kai sunji mganar dayafi karfinsu,Dariyan mugunta yakeyi cikin ranshi,dama da gangan yayi saboda ya kashe bakinsu.

   Ya marwan kuwa da bai samu zuwa ba,ya taimaki kanshi don haka suka tasa mai tsiyan yaki aure har kaninshi yana Shirin yin na biyu raggo kawai har suna Fadin in bai lahiya ne ya sanar su neman mai mgani,dariya takama Sadiq yayi ta darawa har sai da yakira Marwan din yabashi lbrin,dariya yayi kafin yace”Kamar yasan za’a rina,shiyasa ya noke wannan karon,ammh shima insha Allah da zarar yahadu da wacce yakeso zai yunkuro..”

   ****

Washegari da karfe 11:30 na Safe aka daura Auren SALEEM KABIR KUMO
Da Amaryanshi ZAHRA BUKAR MADA akan sadaki mafi daraja Dubu Dari da hamsin,wanda aka daura akofar gidan Alkalin Alkalai bukar mada,daurin auren daya samu hallarta kusoshin gwannati dadama wanda sai dai wasu ka gansu acikin jarida ko gidan talabijin.

Bayan gama Daura auren aka Shiga gaggaisawa,musamman Abbi wanda yake ta sallaman jama’a wadanda suka zo dominshi,shiko angon Amaarya yana gefe,sanye da wata Navy blue din Shadda wacce taji aiki,riga da wando har da babban Riga,sai hulanshi zannah bukar,Shida Sadiq suka sha anko wanda Sadiq din ya Siya shaddan ya kuma dinka musu suka sanya,Sadiq ne keta hada hadar jam’a bakinshi yaki Rufuwa ammh banda Saleem,wanda ya wani hade rau,in kaga yayi dariyan yake toh anzo an bashi hannu ne,ana tayashi murna da Allah sanya alheri.

Su Abbi basu Wuce ba,sai da Bukar mada yatsayar dasu sukayi walima acikin babbann falon gidanshi,wanda sukaci suka sha,suka tashi suna fatan Allah yabada zaman lafiya,Suko su Saleem da sauran abokanshi basu bi tawagar su Abbi su zasu tsaya su taho da amarya..
   
  Tun after 1 Saleem ke masifan Yakamata su Fito su dau hanya,saboda kada suyi dare,don shi yagaji da jira,ammh kuma tawagar amarya suka ki fitowa,Dole tasa Sadiq yajasu da sauran abokan aikinshi zuwa cikin gidansu Zahra suka gaida iyaye da baki,Amarya suna wani bangaren na gidan,sukaji lbrin Shigowar ango cikin gidan,ai zahra dake zaune ana gyara mata Fuska wacce aka Firgita Fuskarta da kwalliya kamar wata aljanna,tana sanye da wani leshi dinki riga da sikat,wanda ya Fito da Suran jikinta,saboda yadda kayan suka kamata,bata ma jira sauran kawaye ba,ta fito Mayafi ahannu,su Nadira ne suka biyo ta da gudu da jakarta suna kokarin gyara mata mayafi.

Lokacin da Saleem yaci karo da Zahra da farko ya tsorata da Fuskarta ganin yadda aka chabamata abubuwa babu kyan gani,kamar wata aljannah,Abunda yafi bashi mamaki babu kunyar Amaren zamani afalon gidansu gaban dubban jama’a ta rikoshi tana mai mgana cike da shagwaba,Sagale yayi mata ammh kuma ya chanza Annurin Fuskarshi kwata kwata ya tsani mace mara aji da kamun kai,shi Tunda kan malika yadaina ma mata kallon goro,toh ji dai malika bai taba zata zai sameta aburduwa ba,ammh sai gashi ta bashi mamaki,Ammh kalli zahra Da yake ganin tatashi cikin hausawa ammh ji Abunda take kamar ba diyar hausa Fulani ba.

Haka ta matsamai suka yi hotuna tana manne dashi,Kawayenta ma duk sunyi hotuna da Sauran abokanshi,Saleema ma tashigo sunyi hoto,ammh fa yanayi yana hararanta,saboda haushinta yakeji,ganin yadda ake Kiranta ko’ina kyace gidan ubanta ne,ko wata kanwar uwarta,Chan suka ja gefe da Sadiq suna gulmansu na fama yana kallonsu aranshi yace”Munafukai kawai…

Suna gama hotuna aka zo aka ja Zahra aka kaita wajen Babanta yayi mata nasiha daganan sai dakin Hajiya saratu momi,itama tayi mata nasiha daidai gwargwardo,acikin nasihan nata taja kunnanta kan ta rage rawan kan nan nata,da shigen Fi’ili da kuma tsiwarta,don wasu mazan basu son Rawan kai,daga karshe ta mata Fadan tabi mijinta,ta kuma zauna da abokiyar zamanta lafiya,kada taji wani baraka ya bullo daga barayinta,Zahra na dunkunkune cikin mayafi kamar ta Allah nan ko Allah Allah take  asadata cikin mota don Nasihar Momi ba Shiganta yake ba,Cikin ranta fadi take”Kishiyar ne zan bi ? Hala ita ta auroni tabdijam ai kowa tashi ta Fisshine..”Take fada babu ko alamun Nasihan ya Shigeta.

Haka aka Fito da zahra,ko hawaye babu a idonta,koda na gulmar da amaren zamani keyi ita batayi ba,idonta kir,sai da Nadira ta maketa ta ja mayafinta ta Rufe mata Fuska tana mata mgana cikin kunne kana ta daina Fito da kanta waje????,Motoci hudu ne suka tafi Abuja,Domin bukar mada yace bayason bidi’an nan duk maison zuwa daga baya yaje ganin daki,duk da dama ango yace amayar kadai yake bukata basai an kawomai wani kaya ba,toh dayake Duniya tana cike da yan boko da masu dashi,shiyasa suma iyayenta basu damu ba.

Motar Sadiq aka sanya amarya Saleem Tun da yaga ana bata lokaci yabi motar wani abokinshi Dcp Sulaiman gidado(Na kishin mata),kusan dama abokai ne???? ,kuma halinsu yazo daya suna da Shigen jinkai da rainin wayau,suka kamo hanyar Abuja su biyu suna tafe hiransu ta abokai suna Shekewa da dariya,shi gidado shi kebama Saleem wasu dabarun zama da mata biyu,saboda shi yariga yin gaba,Hafsa da Jameela suna fafatawa dashi,duk ya da tara daya gida har yana ba Saleem shawaran duk wacce ta kawo wargi ya bata takarda ya sanda ta gida????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button