MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Mikewa Saleem yayi agaugauce yana Fadin”Haba Abbi,wai bazakayi mgana afitar da Daddy waje ba,Tunda sunkasa komai..”Yafada cikin Fita hayyaci idanuwansa sun chanza kala,Kinsakin hannunshi Daddy yayi yana girgiza kai yace”Karku damu dani,ni tawa ta kare,Nidai Fatana don Allah kada kubarmin malika cikin kunci don Allah,ku kula da ita,ka rike mata Dukiyarta kar ka bata har sai ta kara mallakan hankalin kanta..Da..da.ga…Kar…She…ina son Ku..Sanar…Da..ita…Na yafemata..Nima…Ta..yafe…Min….”Yafada Kirjinsa na wani tasowa,Yana shirin Shidewa,Da hanzari Saleem ya kwasa gudu zuwa waje,shiko Abbi hanzarin daukan Oxygen din yayi zai mayar mai, Daddy ya kauda kai yana Fadin”Ka..Bar..Ni..Na..Cika…Da..Kal..mar..Shahada..Laila… ha’illalahu..Muhammadan Rasulillahi…”daga nan ya kafe idonshi nayin sama,Abbi da jikinsa ke rawa agabanshi aka zare ran Daddy,Hannu ya sanya ya karisa rufemai ido yana kareshe “Salallahu alaihi wasallam..”Yake Fada yana share kwallah,daidai lokacin da Saleem ya shigo da zugan likitoci.

Turus yayi yana kallon Abbi dayake Hawaye,Baya yafara ja yana Dafe kanshi,da hanzari likitocin suka karisa ga Daddy suna gwaje gwajensu,basu dau wani lokaci ba,suka ja mayafi suka Rufeshi kafin su waigo suna kallon Abbi,kai Dr ya girgizamai kafin yace”,Am srry We list him..”Yafada kafin ya kada kai ya Fice daga dakin da hanzari sauran ma suka Rufamai baya.

Kukan zucci Saleem keyi,domin na sararin yaki zuwa,Wani imani na kara Shiganshi,Malika yake Tunawa yana tsausayin halin da zata Shiga in taji lbrin rasuwar gatanta Aduniya,Abbi ne yazo ya rikoshi yana bashi baki suka Fita waje,ganin halin da suka Fiti ya sanya su hajiya ta tabbatar da zarginsu kan Daddy,Kanta ta tusa cikib hijabi tana kiran sunan Allah,,Suko yan malumfashi hannu suka dora akai suna kuka tare da Fadin sun bani sun lalace.

Koda Karfe 7 na dare yayi Tuni har sungama wani cike ciken takarda an basu gawanshi cikin ambulance suka nufo gida dashi zukata cike da alhini da rauni,wanda kafin isowarsu gidan har mutanen malumfashi har sun kariso sun cika gida suna ta keko koke,Lbrin rasuwar Alhaji Abdulmalik Dankasuwa tagama zagaya duka kafafen yada lbrai,sakamakon shi mai jama’a ne,da kuma abokan kasuwancinsa da suke son samun jana’izarsa sai aka sanya Lokacin jana’izarsa karfe ,11am na safiyar Gobe.

Abbi da kanshi ya kira Ummi ya sanar da ita rasuwar,salati tayi tayi tana karajin tsausayin malika aranta,nan yake sanar da ita anan zai kwana,saboda haka gobe su taho ita da hajiya,Saleem ko bai zauna ba yayima Abbi sallama akan zai koma yaje ya taho da Malika gobe da safe zasuyi sammakon tahowa,Gyada kai Abbi yayi kafin yayimai Fatan Allah ya kaishi lafiya.

Yana Tafiya bisa hanyar komawa zamfara,ammh kukan zucci yake,kukan tsausayi da wani  Shauki da baisan daga ina yake zuwa ba game da malika,Bayason ya kasance shi zai sanar da ita,wannan babban rashin datayi,Ga kuma wani karin Nauyin Daya rataya awuyanshi na girman Amanar dukiyar Malika da Daddy ya bashi kafin ya cika,hakika Daddy ya cika mumunin kwarai,Allah ya karbi bakuncinsa Ameen.

Sai karfe 11:08pm na dare ya saka motarshi acikin gidan bayan yayi hon megadi ya budemai get,Koda ya faka motar a parking space,kasa fitowa yayi saboda yadda ko”ina na jikinsa yayi sanyi,agogon dake daure ahannunshi ya duba,kafin ya kada kai ya Fito yana amsa gaisuwan da megadi ke jeramai bai jira cewarsa ba ya nufi cikin gidan cike da fargaban da wani ido zai kalli Malika yace mata babu Daddy yau yatafi ya barta…

Yana saka kanshi cikin Falon yaci karo da ita zaune kan kujera tayi tagumi da hannun bibbiyu,tana ganinshi tayi saurin mikewa tana raba ido,da alamun bata cikin natsuwarta,Shiko tsaye yayi yana kallonta yana Fitar da Numfashi sama sama,Ganinta kaawai sai ta kara sanya jinin jikinsa yayi gudu,Kuramai ido tayi tana karantar halin dayake ciki,cikin son nuna jarumta yafara taku zuwa gareta yana kara Kankance idonshi don karta fahimci halin daya ke ciki,itako Tuni ta fahimci Something is wrong.

Sai da yazo gabanta kafin ya zura hannunayenshi cikin aljihun wandonshi yana kallonta kai tsaye yace”Me kikeyi har tsawon wannan lokacin baki kwanta ba..”?

Rau rau tayi da ido tana kallonshi kafin tace”Nakasa barci ne wlh,gabadaya zuciyata babu dadi gabana keta faduwa,tunda dazu da mangariba,kuma na kira wayar Daddy akashe,ta hajiya kuma ba’a dauka.Shine..Shine..Gabadaya na kasa natsuwa..”Tafada cikin karyayyiyar murya hawaye na taruwa a idanuwanta

Gabansa ne ya fadi da sauri yace”Toh kuma shine Abun kuka,kila network ne yasa baki samu wayar Daddyba,ita kuma hajiya may be bata kusa ne,in tazo taga kiran zata kiraki..”Ya fada cikin karfin hali,ammh baya kallonta kanshi na kallon gefe cike da tsausayinta.

Komawa tayi ta zauna bisa kujera tana Fadin”,Toh ammh tun dazu haryanzu fa bata kira ba Mallam..”Tafada hawayen datake rikewa suka zubomata,kallonta yayi yana tsausayama Rauninta,Bata bashi damar mgana ba tace”Kuma ni zuciyata namin rawa duk sadda na tuna da Daddyna,ina tsoron ko wani abu ne mara kyau ke faruwa dashi,don Allah Mallam ka gwada kiranta agani ko zata daga..”Jin Abunda tace ne yasa yace”ok bani wayar taki na dauki nombar..”Da hanzari ta mikamai  bayan ta lalubomai nombar hajiyan,bai mata mgana ba, kawai ya Fito da wayarsa kamar yana dauka nomba,nan ko da wayau wayar malika yayima Shoutdown cuz bayason wani ya kirata ya sanar da ita kai tsaye baisan wani hali zata shiga ba.

Kara wayar akunne yayi kamar yana kira kafin ya saki ajiyar zuciya yana Fadin”batama shiga ba kwata kwata..”Yafada yana tura wayarsa aljihu harda wayar Malika,Zuru tayimai da ido tana sharan kwallah,ganin haka yasa ya mika mata hannu yana Fadin”To kuma miye Abun kuka anan..? keda kuka bai miki wahala,oy taso kizo kiji wata mgana..”Yafada yana sakarmata idanuwanshi,Kallonsa tayi kafin ta mikamai hannu ya mikar da ita kai tsaye ya jawota zuwa jikinsa,dukkansu suka saki Ajiyar Numfashi,Hannayensa yasa yazagayo bayanta dashi,itako ta lafe bisa kirjinsa lokaci daya ta fashe da kuka,domin taji kasa control din kanta ne,..

Kanta yake shafawa zuwa bayanta da sigan lallashi yake Fadin”ShiiiI..Ki bar kukan nan don Allah,insha Allahu babu komai..”Yafada yana kara matseta ajkinsa,kukan natane ya lafa,ammh kuma ta sanya hannunta ta zagayo bayanshi dasu takara shigewa jikinsa tana kamkameshi sosai,Wani yam!Yum!yarr!Kawai yakeji gefe daya kuma tsausayinta ne da wani shaukin sha’awarta ke kara tumurmusanshi,Kasa rike kanshi yayu shima,baisan sadda yayimata tsautsaran riko ba yana Fitar da Numfashin wahala da muradi mai tsawo.

Cikin fitan mgana ya Furta”Kinci abinci..? Kanta ta girgiza mai alaman a”a,yana tusa kanshi jikin wuyanta yake fadin”Meyasa..? yafada yana Fitar mata da hucin Numfashinsa awuyanta,wanda ya hassada mata wani Barin jiki mai hade da muradi mai girma,Kasa bashi amsa tayi saboda yadda yake ta shinshinanta gefe daya kuma duka hannayensa basu bar kara kaina ajikinta ba..

Fuskarta ya dago yana kallon kwanyan idonta,rintse ido tayi tana zubar hawaye wanda batasan dalilinsu ba,Harshensa ya Fito dashi baisan dalili ba kawai ya samu kanshi da kama kanta da hannayenshi guda biyu ya shiga lasheta mata hawayenta sai da ya lashesu tas,bayan ya tsotse harda saman idanuwanta inda gashin idonta yacika da ruwan hawaye,Karkarwa take tana kara shigewa jikinshi tana karban sabon sakon nashi,yaraf takoma ta lafe bisa kirjinsa kafin yakara dago Fuskarta yana kallonta Hannunshi ta rike tana kallonshi idanuwanta cikin so da zallar kaunarshi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button