MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Wacce aka kira da best ta bamberata daga jikinta tana Fadin”Toh tsarani,kika dai tsaya tsinannan rawan kanki,keda wa nake hango ki tsaye tun saukowata daga jirgi..? wani Fari ta mata kafin ta ja hannunta da hannu daya dayan kuma taja trolly dinta tana Fadin”Kedai bari my best today i meet my mr Right wlh…”Da kallon mamaki Best din ta bita kafin tace”Topha wanene shi..?

Suna tafiya ta bata amsa da cewa” * ACP SALEEM KABIR KUMO*….”Baya taja tana maimata sunan da sigan tambaya”Acp saleem kabir kumo fa kika ce? tsayawa tayi itama tana kallonta kafin tace”eh kinsan shi ne…? Mirmishi ta saki kafin tayi gaba tana Fadin”Eh mana waye baisan shi ba yaron IGP ne fa nakasa gabadaya…”Ido  Zahra ta zaro tana Fadin”Wow!Kice Abba ma zai sanshi…?

Tsaki taja tana Fadin”Kina da mtsala,toh bama Abbah ba,kowa dake kasar nan yasanshi,ko kin manta shine fa kwanaki ya auri diyar dan kasuwan nan mai kudin bala”in nan Malika malik,kuma ya saketa adaren Auren..”Kwalalo mata ido tayi daidai lokacin da suka iso bakin motar da zahra tazo da ita kirar 306 tana Fadin”Kai don Allah ya”akayi ni ban sani ba..?

Tsaki taja tana zagayawa bangaren mai zaman banza,sai da ta bude motar ta shiga kafin itama zahra ta bude baya ta jefa Torolly din ta bude bangaren Direba ta shigo daidai lokacin da Nadira take Fadin”Dallah wake ta sha”aninki keda sai kiyi sati baki hau social media ba,mu gani kamar last 3 month ne Abun ya faru,wlh kwanakin kowata jarida Abunda tayi ta bugawa kenan haka Social media anyi ta yama didi da zencen..”

Shuru zahra tayi bayan tayi Tagumi take Fadin”Toh kuma wai da gaske ne..”?Hararanta tayi tana Fadin” Bansani ba,Tunda zan miki krya ne,Kinga zaki tukamu zuwa gida ne,ko kuwa zaki tsaya jin gaskiyan ne..? Tafada cike da kosawa,tabe baki tayi tana fadin”Oho miki dai,badai ya saketa ba,niko naji na gani inaso,don ganin farko naji yamin wlh best ya sace zuciyata inaji kamar i can’t do Withount him…”Galala Nadira ke kallonta kafin ta kada kai tana Fadin”Eh naga alama..”Ta fada tana binta da kallon mamaki,yadda take driving tana mirmishi ita kadai.

  WACECE ZAHRA BUKAR MADA

Diyace ga Tsohon Alkalin Alkalai na kasa gabadaya BUKAR MADA Asalinshi dan Maiduguri ne,dagashi har matarshi HAJIYA SAHURA Kafin zuwanshi wannan mtsayin ya rike alkalai akotuna dadama kafin yazama Alkalin Alkalai.

Sun dade da aure kafin Allah ya basu Haihuwa Mace ZAHRA Kuma Tunda ga ita bai kara samun haihuwa ba,gashi da son ya”ya wannan Dalilin ne bayan rasuwar dan”uwanshi Shehu dake lagos da zama shida matarshi da yaranshi,ya dauko Biyu daga ciki, NADIRA da NADIR wanda ya rikesu tun suna yara awajensa sukayi karatu,har zuwa girmansu….

Ita kuma Nadira da Zahra kusan sa”annin ne tare suka tashi sun Shaku da juna matuka,komai nasu tare sukeyi kamar wasu yan biyu,shiyasa suke kiran juna BEST,tare sukayi karatunsu a jami”ar Base dake Abuja,Nadira ta karanta Microbiology,sai Zahra data karanta Mass com Dukkansu sun kammallah harta master dinsu kowacce ta gama,ammh basa aiki saboda Abbansu bayi da sha’awan haka sai dai yafi sha’awar kowacce taje dakinta in mijinta ya yarjemata ta yi aikinta,in kuma ya hana ta dai samu ilimin,shiko Nadir likita ne ajami”ar Malesiya yayi karatun likitansa,abangaren mata,ayanzu haka yana Asibitin Mallam Aminu kano yana aiki a matsayin babban likita.

Ko atasowar Nadira da Zahra akwai bambamci hallaya atare dasu,domin Nadira tafi zahra wayau da sanin kan Duniya sosai,sakamakon ita Zahra bata son komai sai tabara da sangarta,ga rawan kai da Feleke barta da son asani da kuma Shigen Shisshigi ammh fa sakaryace,sai dai akwai daukan wanka bata shigar banza,saboda Bukar mada bai barsu haka ba,Shida Hajiya sahura basu yi musu Rikon wasa ba,

Zahra sha”anin Shigen shigen Yanar gizo bai dameta,ko waya ma ba damunta yayi ba ita dai barta da kallon India Series kamar wata mayyah,to anan tafi Auki,ta Wuni tana kallo bata gaji ba,in ko ka ganta da waya toh ba chart take ba,sai dai game don anan Tafi auki,sakamakon Nadira mace ce mai son Nuna ita wayayyiyace,Tana son Shiga yanar gizo,babu Kalan Social media Da batayi sai dai wanda bai Fito ba,kuma babu Wanda indai ubanshi kusa ne agwannati da bata sanshi ba,shiyasa tasan lbrin Saleem da Malika,domin Malikar ma tana Following dinta a intergram dinta,ada suna zaune Abuja ne,ammh bayan saukan Bukar mada daga Kujerar Alkalin Alkalai,sai suka koma kano da zama.

Haduwarta da Saleem A Airport ma taje dauko Best Nadira ne,wacce taje lagos wajen mamanta Hutu,shine suka hadu da Saleem kuma lokaci daya taji ya sace mata Zuciya da gangar jiki gabadaya.

Wannan kenan.

  _________

Shiko Saleem daganan Kano Zamfara ya Wuce kai tsaye,bai fara isa gidansa ba,sai da ya biya headquater su yayi Report ya gaisa da abokan aiyukansa,kafin ya isa gida,yayi wanka yaci abinci dama already ya tsaya wani restaurant ya yi ma kanshi take away,yana gamawa ya fadi bisa gado yana barcin gajiya wanda bai tashi ba sai gab da kiran sallar mangariba.

Washegari Tun karfe 7:30am na safe yasaka hancin motarsa bisa hanyar Abuja,domin ya kosa yaje ayi wacce za”ayi domin yasan Abbi da Ummi suna jiracesa dashi ne.

A yau din yana sanye ne da Riga da wando,Wandon Nevy blue ne,sai Rigar Ash ce tana da ratsin layin blue ajikinta,kuma dogon hannu gareta,mai dauke da botura ta kasan hannun,kafarsa ko Yau Budadden Takalminsa ne mai kalan blue shima mai kyau da tsari.

Kusan mutumin naku da gudu bisa hanya kamar zai tashi sama,sai gashi koda karfe 11:00am na safe tayi mai kofar Tamkamemen gidansu yana Zuba hon,megadi yana lekowa ya ganshi,jikinsa na rawa ya wangalemai get yana mai sannu da zuwa,Shiyama budemai kofar motar sanda ya gama daidaita zamanta a parking space….

Bayan ya Fito sun gaisa kai tsaye ya nufi cikin babban Falon gidan,ammh wani sashe na zuciyarsa na bugawa da tsoro baisan da wani tarba Abbi zai karbeshi ba,da siririyar sallama ya kutsa kai Falon,babu kowa sai karan tashin Talabijin daya keyi Shi kadai,tsaye yayi atsakiyar Falon yana karema ko”ina kallo,ganin babu motsin kowa shiyasa ya kara daga murya yana sallama cikin fargaba…..

Ummi na kichen tana hadama Abbi breafsat dinshi yau ya tashi bayajin dadin jikinsa,.taji sallama daga farko,ammh jin Shuru ba”a karayi ba yasa tabasar,ammh sai takaraji an sakeyi bata dauki murya ba ,ta Fito da hanzari tana amsawa sai ta ci karo da Saleem tsaye yana kallonta,

Daure Fuska tayi kamar bata taba saninshi ba ballantama ganinshi tace”Lafiya mallam daga ina..? Gwiwanshi ne yaji yayi sanyi yana neman dukawa ya gaisheta yaji Muryan Abbi da kakkausan murya yana Fadin”Kai…Kul!…Kada ka sake ka dukamin Agidana…”

Abbi ya Fada yana saukowa daga saman Step sanye da bakar jallabiya,Jin haka yasa Saleem bai dukaba ya mike yana marairaicewa Abbi yana gama saukowa ya kalli saleem yace cikin kakkausan murya

“Yi baya nace…!Ya fada da tsawa,sororo Saleem yayi kafin ya bude baki yace”Ab….!Yi baya nace Saleem..!Abbi ya kateshi yana sake maimata mganarsa,mganar Abbi cikin fada ne yasa Hajiya Fitowa tana Fadin lafiya,sai kuma ta ci karo da Saleem baki ta kama tana Fadin”Kai kuma Salihu daga ina haka? sai kace wanda yayi sata aka biyoshi kana wani rarraba ido kamar wani maye…”Tafada fuskarta ba Fara”a

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button