MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

  Komawa yayi yazauna yana Dora kafansa daya kan Daya,wayarsa ya zaro wata faskekiyan wayar Kirar Samsumg,yana latsawa kafin hotonta ya bayyana,tana sanye da Riga da wando black and white,kayan sun dameta bayan sun Fitar da duka Surarinta waje,kanta babu kallabi,illah dogon gashinta wanda ta daure atsakiya da band,ta saki jelan yayi kasa,fuskarta sanye da wani bakin glasa,yacikamata rabin Fuska,kafarta kuma wani takalmi ne,mai tsini wanda har ya Wuce misali lokaci da aka dauki Hoton tana saukowane daga matattakalan benen Jirgi,wasu Exscorts suna biye da ita su biyu kowanne sanye da Court sun saka wasu galasai Abun sai wanda ya gani,daya yana dauke da Brief case,sai daya yana dauke da wata karamar jaka na mata,kunnanta yana sagale da waya tana mgana sanda aka dauketa hoton da alamun ma bata da masaniyar sanda akayi hoton.

  “”Kuramata ido yayi zuciyarsa na bugawa,Tuni hoton Abunda yafaru Shekaru biyar baya ya Shiga dawomai daki daki,har saida ya dafe kuncinsa ba dama inda ta shararamai mari,,har sai da ya Runtse ido,kamar alokacin take marin nashi,matse bakinshi yayi yana Shafawa,daidai inda ta tofamai miyau,idanunsa ya Runtse yana Sauke ajiyar zuciya yana tuni sanda ta watsamai kudi ajikinshi tana kiran aikin yan sanda da Rubish,Saurin bude ido yayi yana wani Zare ido,tsoro naji saboda ganin yadda gabadaya jijiyoyin kansa suka Fito radau,ga idanuwansa sunyi jajir kamar barkoni bayan gabadaya muscle din hannuwansa sun bayyana suna wani motsi daga cikin Abun tsoro wlh..????

Wayar ya kifar akan teburin kafin ya mike azuciye kamar tana gabanshi yasaka hannu ya daki gaban Teburin yana huci yake fadin”, *MALIKA MALIK..Sai na rama..”Nayi alqawarin sai na wulakanta rayuwarki sai na nuna miki ke ba kowan kowa bace,sai na miki matsayi tare da zati,jarumta da sadaukanta yafi komai muhimmaci,wlh tallahi sai na nuna miki mtsayin kakin yan Sanda yafi uwarki yafi ubanki da duka danginku da dukiyar dakuke takama…!!!!”Yafada yana Fitar da huci Shikadai kafin yakoma yazauna jagab yana Ajiyar zuciya.

Duk tsawon wannan Shekarun daidai da Rana daya baitaba barin Abun yafita daga Ranshi ba,barci yake,cin abinci,wanka yakeyi karatu yake,driving yakeyi,komai in yana yi sai Abun ya fadomai,zuciyarsa taki barinsa sukuni daya Runtse ido ita yake gani tana tsaye gabansa tana aibatanshi tare da wulakanta martaban mahaifinsa bayan ta hada ta shararamai mari,kamar wani sa”anta yarayu cikin wadannan shekarun cike da zumar da zati na Ramuwar gayyah ga malika malik,duk iya tsawon wannan Shekarun daya kwashe baitaba yarda yabar bibiyar Rayuwar Malika ba,duk wasu bayananta da hallayanta da komai nata yana dashi kuma ko”ina zata yana da ido kanta,bai ta bari koda ta minti daya yarasa wani Abu game da ita ba,saboda ita ya chanza burinsa na zama ENGNEARING,saboda ita ayau yake zaune awannan mtsayin domin ya nunamata Wutsiyar Giwa tayi nesa dana Rakumi,kuma tsakanin shi da ita kamar tazaran sama da kasa ne.

Da hanzari ya mike yafara tararra kayansa,Wayarsa ya maida aljihun kafin ya maida laptop dinsa ama”ajiyarsa key din motarsa kawai ya dauka ya Fice da hanzari,yana Fitowa suka dinga kamemai suna Fadin”Sir..”ko kallonsu baiyi ba iilah jefama wani daya daga cikinsu key yayi yana fadin”Close d office,..Kai kuma Sargent musa follow me,Abuja zamu yanzu..”Gabadayansu suka amsa da ok sir Safe landed..”Har yafara taku ya waigo yana kallon Sargent musa yana Fadin”Bring d key back to me sargent musa,i will drive my self juz take care, komai kenan zamu waya sai Monday,zan dawo ok..”Da kai suka amsa kafin sargent musa ya mikamasa key din motar,da sassarfa ya fice suka mara mai baya,sai da suka rakasa har wajen motarsa 320 kirar Toyota,Sargent musa ya budemai gidan gaba ya Shiga,sai da ya daura belt kafin ya bama motar Wuta rufemai kofar motar sukayi suna dagamai hannu,mirmishi yayi musu yana kara jadaddamusu su kula sosai,ribas yayi yana danna hon da hanzari megadi yazo ya wangalemai babban get din waje ya sulala zuwa waje da gudu,sanin dayayi akwai Tafiya agabanshi yasanya yasakarma mota Wuta,duk da yasan ko atsarin doka hakan ya haramta,ammh bashi da zabi dole ce tasashi yin haka domin yana bukatar isa Abuja kafin duhu ya shiga,sanda yake duba Rantsatsen agogon Fatan dake hannunsa Hudu saura kwata,jinjina kai yayi bai Fita daga garin zamfara ba,sai da ya tsaya awani masallaci yayi sallar La”asar kafin ya dauki hanyar Abuja.

   ____

GARKI ABUJA

  Karfe 8:30pm na dare yasaka Hancin motarsa Cikin Rantsatsiyar anguwan nasu tamasu hali,wato GARKI,wani tamkamen gida naga yana ta zuba hon,inda megadin gidan yazo da hanzari ya wangalemai get,Koda ya sulala ciki,parking space ya nufa inda ga motocin nan birjit,afake akaton haraban gidan,gidan gabadaya dauke yake da Security yan mopal,sukai su goma suna zagaye gidan,megadin da kanshi yazo ya budemai yana Fadin”Barka da zuwa yallabai..”Amsawa yayi yana Shafa kanshi Motar Ummi dake fake a haraban gidan ya kallah ajiyar zuciya ya sauke,Thank god Tunda Ummi tana gida yafada aransa,Wayar dake aljihunsa yafito dashi daidai lokacin da kiran YA MARWAN yafito daga wayarsa da hanzari ya daga yana Fadin”

“Wai nikan Yaya marwan,bazaka iya kwana bane, batare da kaji muryata bane..? yafada yana dagama Mopal din dasuka sarama hannu,,hanyar dazai sadashi da Falon gidan,ya nufa yana dariya jin Abunda Ya marwan ke fada”Kai kai..lallenema yaron nan,daga ina kula da Amanan Abbi,sai na murdema kunni in nadawo malalacin Acp kawai”Dariya ya kece dashi daidai yana Shiga falon,tsaye yayi yana Fadin”Kai ya marwan,kullum haka kake cewa,ammh kaki dawowa u know  we all miss u ko.? yafada yana kokarin zama a daya daga cikin Royal chair din dasukayima Falon Kwanya,kawai yaji kikam ta fadomai tana Fadin

“Oyoyo Ya saleem….”Take Fada Tana ihu,saboda yadda ta fadomai harsai da wayar hannunsa ta subuce tafada kan kujeran da yake kokarin zama,dagowa yayi yana riketa dakyau kunnanta ya murde yana Fadin”Yarinyar bakijin mgana ko? Baki ta bare da karfi tana Fadin”wayyo Allah kunnena Abbi,Ummi ku fito ya saleem zai karyamin kunni na, yarage min sadaki..”Take Fada tana kware baki harda buga kafa,shiko da gangan yakara murdemata kunni yana Fadin”Har yaushe ne,zan ce kidaina fadomin ajiki kai tsaye,ke bakisan kin girma bane..”? yafada yana dalle mata baki da dayan hannunsa,yana dariya yace”Dallah yima mutane shuru,ai babu mai zuwan cetonki…”Gum…!Yaji an makamai Filon kujera a keyarsa lokaci daya da Fadin”Sakarta don mai garinku kumo..”Tafada tana tsaye tana hararansa,dafe keyarsa yayi bayan ya saki SALEEMA wacce takoma gefe tana Fadin”Yauwa hajiya,ramamin..? tafada tana murza kunnanta saboda zafin dataji bana wasa ba.

Da Kallo yabi HAJIYA BABBA wacce ke tsaye da Filon kujera tana Fadin”Ai Tunda naji ihunta nasan Azzalumi ya dawo,wlh duk kakoma dukanta sai naci kaniyarka acikin gidan nan,yarinya tazama budurwa ko yanzu aka kaita daki zata zauna,ammh kana jibgarta kamar kasamu jaka..? Tafada tana Hararansa again,Bata Fuska yayi yana kallon Saleema wacce hajiya ta karisawa wajenta tana fadin”Muga Fuskar da kunnan,wlh indai naga Shaidan yatsu sai yabiyamu,kowani yatsa dubu daya ne,dubu biyar dinmu ahannu,kaji da wai kuma Uwarka ce zata bimana hakki tunda lauya ce..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button