MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Sai gashi hira tayi dadi tsakanin zahra da Saleema,sai wajen 12 suka kafin suyi sallama,shima bawai don Zahra ta gaji ba,sai don Saleem ya nuna yana jin barci saboda Fita aiki gobe,itako Nadira tun tana jinsu sama sama har barci ya kwasheta,sai da zahra tatasheta tana ihun murna,tana sanar da ita yamzu suka gama waya da Saleem,Nadira ta rumgumeta tana ihu,wanda gar Momi dake dakin Abbansu,ta Fito tazo kofar dakinsu tana tambyansu lafiya,sai lokacin suka dawo hayyacinsu,Nadira ce tace wai Ya Nazir ne yayi musu kyautan 50k ta account yanzu,tsaki taja ta wuce tana Fadin”Allah ya Shiryeku kuyi dai ahankali yanzu dare ne..”

Sai gashi duk dare sai zahra da saleem sunyi waya da juna kafin su kwanta,duk da yanzu ta rage kiranshi,ammh kuma ta chanza taku takoma turamai sakon soyayyah masu sanya zukata,wanda Nadira ke Rubuta mata tana turamai,na safe dabam na rana dabam hakama na dare shima dabam,kuma kalamai so sexy and Romantic,shiyasa lokaci kadan Zahra ta fara burge saleem,har baya iya barci sai yaji muryanta,duk da wani lokacin yana basar da ita,bayason soyayyarsu tayi zurfi kuma yazo yace zai aureta Abbi ya dakatar dashi.

BAYAN WATA DAYA

Wata daya kenan da zuwansu zamfara,Alhamdulillah kawai malika zatace domin abubuwa suna Tafiyan mata yadda Yakamata,duk da akwai abubuwan da ba haka taso ba,bangaren karatunta kuwa Tuni tayi nisa son Saleem bai yi mata da wasa,koyar da ita yake kamar yadda ya dau alqawari,bata aikin komai sai gyara dakinta da Falo in yayi kura,da yan kwanuka in ta bata,Mganar abinci kuwa Saleem yadauke mata wannan Nauyin nayimata takeaway kullum sau uku arana,kuma babu laifi yana bata kula sosai abangaren cikinta,ga kuma kayan daya kawo mata kamar za”a bude shago,ta dade bata iya daura zani ba,sai da ya dinga koyamata,ko daura dankwalin ma,shike amsa yana gwada mata yadda zatayi har tasamu ta iya dan sagala shi,ganin Riga da zanin na bata wahala sai takoma sanya masu sikat kawai saboda sunfi mata saukin sawa,duk tafi sati kafin ta saba da saka kayan,da farko damunta sukeyi ba kadan ba,sai hijabai wajen kala ashirin da masu hannu da marasa hannu,kuma duka yadi uku da rabi rabi ne,in tasaka har kasa suke kaimata kamar wata zulumbiya????

Satinsu biyu da zuwa gidan ta samu ziyarar wata makociyarsu wanda gidansu ke kallo nasu,MAMAN ABBA,Nurse ce tana aiki general hopital Zamfara. Mijinta kuma manajan bankin First bank ne,danta daya Isma’il suna kiranshi Abba,Ta shigo suka gaisa da malika,nan take sanar da ita ga gidanta nan kusa da nasu,tun sadda Acp ya sanar da Baban Abba,cewa yazo da matarsa takeson Shigowa ammh kuma bata samu lokaci ba sai yau,fatan zasu dinga zumunci….

Murna ta cika Malika rana ta farko Tun bayan Shiganta wannan Halin ta samu wani akusa da ita,cikin Fara”a da sakin Fuska ta karbi Maman Abba,wanda suka dade suna hira kafin tayi mata sallama tatafi,da saleem ya dawo jikin Malika na rawa ta sanar dashi zuwan Maman Abba,tace kuma ya barta itama ta Shiga wajenta,murtuke Fuska yayi yace bai yarda ta Fita konan da kofar gida ba,Dole ta hakura duk da ranta baiso ba ammh bata nuna mai, ba,Wannan Abun yana sa Kimarta yana karuwa a idon Saleem sau tari zai kuntatamata da gangan ammh ko a fuska bata nuna taji haushi ko ranta yabaci,sai dai shi yadaga baya yaji bai kyauta mata ba sam.

Maman Abba batayi Fushi ba dataga Malika bata Shigo ba kamar yadda tace sai ita ta Shiga wajenta,suka kara gaisawa,nan take kara lura da cikinta har ya Fito,ada kamar bazata tambayeta sai kuma ta tambayeta ko ta fara zuwa awo..? amsa mata tayi da”a”a.Nan,Maman Abba tace aiko yakamata kifara zuwa awo,saboda daga ganin cikin jikin ya kai 4month in ma baifi ba,Mirmishi kawai malika tayi tana sunkuyar dakai,don azahirin gaskiya bazata iya dora komai kan cikin jikinta,game da Saleem ba,don bata ga yana wani damuwa dashi ba balle dokinshi,balle har yagane ya isa zuwa awo.

Bata mai mganar ba,sai da aka kwana aka Wuni,bayan sun gama karatun dare,take mai mganar zuwa awon da Maman Abba tayi mata ya dade yana kallonta domin shima satin daya Wuce Ummi ta kirashi take tambayanshi Malika ko tafara zuwa awo..?karya ya zabgamata yace eh kafin ya gyada kai yana Fadin”Yaushe ne tace zaki fara zuwa awon..?Kanta na kasa tace “Bansani ba,sai in ta shigo na tambayeta..”Mikewa yayi daga tsaye yana Fadin”No gobe da Safe ki Shirya ki shiga gidan sai ki tambayeta,ko goben zaki fara sai ki sanar dani..”Gyada kai tayi tana Fadin”ngd..”Bai kulata ba ya Fice daga dakin zuwa nashi,yana kokarin amsa wayarshi wacce zahra ce ke kira.

Haka ko akayi da safe bayan ya tafi tayi wanka ta saka atamfanta dogowae riga da dogon Hijabinta ta Shiga gidan Maman Abba ta sameta tana Shiri zata asibiti yau Dutyn safe gareta,nan suka gaisa cikin Fara”a Shine take sanar da ita Abunda Saleem yace,Maman Abba tace “Toh ai Faduwa tazo daidai da zama,gobe ne ranar Zuwa awon ,sai ki koma ki sanar dashi,gobe in zan Tafi sai mutafi tare,Allah barshi bayan an miki scaning da sauran abubuwa,ni sai na cigaba da dubaki agida.

Haka ta sanar da Saleem da daddare bayan ya dawo,bai yi gardama ba yabata kudi 10k yace taje dashi,da kanshi ya dauki wayarta ya saka nombarshi yace takirashi in ance ana bukatar wani abu,Murna takama malika ranar batayi barci ba tana murnan yau itama zata asibiti ta shiga sawun iyaye mata masu ciki,koda 8 tayi sun tsufa ageneral ita da Maman Abba,wacce ta tukasu asabuwar motarta 306.

Sakamakon zuwanta da wacce take da sani awajen Bata wani jima ba,aka bude mata Fayel likita ya dubata kafin aturata dakin awo,Shima din bata jima ba Tafito,Aka bata sati hudu ta dawo,batayi amfani da kudin da Saleem ya bata ba,saboda asibitin ta gwannati ne,sai dai ta siya magungunar da’aka Rubuta mata na karin jini,Maman Abba da kanta takara tukota ta maidata gida tana ta mata godiya.

Saleem yana office ammh kuma rabin hankalinsa na kan Malika yana so yaji ya ake ciki,gashi bai karbi nombarta ba,Ganin har wajen yammah bata kirashi ba,kuma yau bashi ya kaimata abinci ba, Sarger musa ne,ammh ya tabbatar mai da megadi yace ta dawo Zahra ce ta kirashi ta daukemai hankali da hirarta tana mai kukan Shagwaban yaki yazo ya ganta,Shikuma bayaso yayi mata alqawari ya saba ne,yau dai ya tabbtar da mata data jirashi zai zo dis weeked insha Allahu,Murna kamar zata kashe Zahra tayi ta murna tana tsalle ita da Nadira,wacce itace ke dorata adukkan hanya data kama Saleem yanzu ahannunta,duk da bai gama kamuwa duka ba.

Shiko Saleem yanajin aransa zai iya maneji da zahra,domin yana cikin wani mayuwacin hali na bukatar mace akusa dashi,bayaso yaje ga malika tadauka yafara sonta ne,Ko ana Farko yayi mata hakane don tagane kuskurenta,yanzu kuma sai yakoma..? Abun da kunya gaskiya bayason yarinyar ta rainashi sam,ammh kuma yakasa Fuskarta wani abu koda zai ga mata awaje koda ko da wani irin banza Shiga ne basa burgeshi kuma bayajin hankalinshi ya tashi,ammh da zarar ya dawo gida yaga Malika,sai kawai yaji yanayin jikinsa ya chanza,ko dakinsa tazo karatu haka zai dinga jinsa konai nasa na chanzawa,In ya kalli cikin idanuwanta tsausayinta da sha’awarta na kara Tsumashi balle yanzu yadda ta cika sosai kirjinta da kugunta sun kara Fitowa,haka Fatar jikinta tayi kyau Fuskarta tacika da kumatu ta kuma kara haske Fata,koda kuskure jikinsu ya hadu da juna,ranar haka zai kwana mafarki sai Da asuba yayi wanka Kafin ya tafi mssallaci,Yarasa yadda zaiyi da rayuwarsa,Sai kawai ya yanke shawarar yayi aure,Tunda dai bazai iya kara Tunkarar malika ba,gwara ya neman ma kanshi mafita duk da yana tsoron kada Ummi da Abbi su dakatar dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button