MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Nan suka isa ga motocin aka bude suka gani harda na Malikan,jinjina kai kawai Sadiq yake aransa yana ayyana Dalilin daya sanya Saleem auren Malika saboda kudi ne,Ai basu saki baki sai da suka shiga gidan,daki by daki suka dinga shiga suna ganin Uban Dukiyar da”a Narkama gidan,basu tsinke da al”amarin ba sai da sukaga lefen dayayima Malika boutique Guda ne,aka tara,shikanshi Dakin Saleem din ya basu tsoro,kai Ai nan da nan Sadiq ya yarda da zuciyarsa na dama kwadayi ne da Auren jari yakai saleem ga auran malika Kai,babu shakka ya tsinci dami a akala.

Bayan sungama gani suka sanya albarka nan Daddy yake sanar dasu basai Saleem yazo daukan Amarya ba,shida kanshi zai kawo malika har dakinta,kana bai hanashi bayan sungama cin amarcinsu ba ya dauki matarsa zuwa wajen dayake aiki ba,in kuma zai barta nan ne,duk yadda yagani.

Saleem yaji dadin haka dama kuma Shirinsa kenan,domin adaren yau yake son dukkan wani Shirinsa ya kammallah zuwa waye garin gobe sai Dai aji bom din ya fashe shikuma kafin lokaci yayi nisa da jaharsa,kilama harda Kasar gabadaya.

Daganan gidan hanyar Abuja suka dauka,shikuma Alhaji Abdulmalik da danginsa suka koma gida,ko acikin motar,daga sadiq har marwan Zence suke tare da mamakin uban Dukiyar da aka batar suke,shiko Saleem ko baki bai tsoma musu ba illah danne dannen waya dayake tayi,ammh bayan lokaci kuma ana turomai sako ta waya kuma ya na maida reply batare daya bari wani cikinsu ya ankare dashi, ba Gabadaya zuciyarsa ta kekeshi,ba kamar dazu data nemi ta karaya ba,Abbi na gaba shida tawaganshi da sauran motocin yan uwa da sukazo daga kumo,suma lbrin arzikin da Saleem yatako kawai suke kowa aranshi yanajin dama shine saleem.


Malika ko tun daren jiya data Shiga dakinta bata Fito ba har gari ya waye,akayi ta hada hadar biki da kuma zuwa daurin aure batasan wainar da,”ake toyowa ba,tana kwance tana barcin gajiya sallar asuba ma,sai wajen 10 tayi bayan tatashi daga barcinta na asara,wanka kawai tayi,dama already Breafast dinta su Dose sun gama jera mata komai,Falo ta Fito daga ita sai wata yaloluwar riga Red colour,wacce da Kadan ta Wuce gwiwanta ,Wayace ahannunta wanda Tun jiya bata bi ta kanta ba,sakonni ta tarar bila adadin tare da kuma da kiran mutane,duk yawancin kiran na abokan kasuwancin Abbanta ne,na kasashen ketare,Abunda ya dauremata kai Shine sakonninsu ,mai dauke da HAPPY MARRIAGE LIFE MRS SALEEM KABIR KUMO

Abun ya Dauremata kai sosai,har ta zauna bisa daya daga cikin kujerun Falon tana sake cigaba da karanta sakonnin,Abun yabata mamaki ammh sai bata daukeshi wani Abu ba,tana tunanin kila kuskure ne,bata ji jikinta ya saki ba,sai da ta shiga shafinta na Twitter taga hotunanta dana Saleem Rututu ana Dorawa ,Friend dinta suna ta mata Happy marriage life.

Jikinta ne ya soma rawa,tafara Zargin wani Banza ne ya nemi bata mata suna aduniya kawai dare daya ya hada hotonta da wani kazami kazamin ma,wai wani Dan sanda,wanda basu iya komai ba sai lalacewa da shaye shaye,wai kuma da sunan mijinta,Kutumar uba ne,lalle kowani Wulakantattace ne, ayau basai gobe ba take son saninshi,taji dalilinshi na bata mata suna,da kuma yimata karya Aduniya

Fuuu tatashi ta Fice daga dakin dauke da waya ahannunta Falon Alhaji Abdulmalik dake sama Ta nufa tana kwalamai kira bata damu da Dimbin jama”ar dake falon kasa suna kallonta ba.

Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..

Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani

07065481260..Ko kuma 09069067488

Shakira

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

Dedicated To my Uwar Room, ZM CHUBADO Na sadaukar da wannan bautifull Chappy,gareki Ina so ki sani na YARDA DAKE kuma nima nasan Tuni kin gama bani Dukan YARDAN KI Son so Fisabillah ????

9

    “Tana Shiga Falon ta tarar da babu kowa ciki sai wasu baki goggoninta na malumfashi dasuke zaune bisa lumtsuma lumtsumar kujerun Falon suna hira…

Kallo Daya tayi musu ,bata kara ba bayan taja musu uban dogon tsaki ba wanda tacema kala ta tsallakesu zuwa bedromm din Daddynta tana kwalamai kira,anan ma wayan Fitowa tayi a hargitse daga Falon tayi Falon kasa bibbiyu take hada Steps saboda yadda Ranta yake amatukar bace,gana Abunda tagani  ga kuma na ganin wayanan zugan yan kauyen da suke zaune musu agida basu Tafi ba.

Tana saukowa Falon Tashiga kwalama Hajiya kira muryanta akaushe…”Hajiya…?Hajiya…? Take Fada tana takowa zuwa tsakiyar Falon Fuskarta babu Annuri tana bin mutanen dake zaune da wani wulakatattacen kallo….

Joda ce ta Fito daga dakin Hajiyar tana Fadin”Anty Malika lafiya,…? Kallonta tayi tana wani mele baki a sangarce tace”Bai shafeki ba,juz ina hajiya…? Ta bude baki tayi mgana sai ga Hajiya ta Fito daga wani bangare na gidan tana Fadin”Lafiya malika,ina wanan kiran fa..? Baya taja tana Fadin”Ina Daddy shi nake nema banganshi ba…?

Kada kai Hajiya tayi tana karema malikar kallo,da ita da rigar jikinta tace”Bayanan ya tafi daurin aure,ammh nasan yana bisa hanyar dawowa..”yamutsa Fuska Tayi kan tajuya tana kallon mutanen Falon tana fadin”Toh su kuma wadanan me suke jira basu tafi ba,sun zo sun share kafa kamar wadanda aka gayyata wani sha’ani plz nidai su tararra su Tafi ko ni na bar musu gidan…

Wata goggon Alhaji Abdulmalik dataji haushin mganarta kai tsaye tace mata”,Mu tafi ?muje ina Amarsu ta ango? ai muda tafiya sai mun mika ki gid…”Kai Goggo Baraka don Allah kiyi Shuru…”

Hajiya ta katseta da hanzari jikinta na rawa,domin Alhaji Abdulmalik sai da ya gargadeta datayi taka tsan – tsan ko Malika ta Fito kada ta kuskura tabada damar da zata Fahimci Abunda ke Faruwa,shi zai sanar da ita da kanshi,to gashi goggo Baraka Tayi baram barama.

Malika dataji mganar bata maida kai ba,Saima mele baki datayi wanda ga duk alamu ya zamanto mata jiki,ta juya gabadaya duwawukanta na wani rawa ,da alama ma ko pant bata saka ba,ammh sai me Abun ne ya shiga mata yawo akunne Mu tafi muje ina Amarsu ta ango? Ai muda tafiya sai mun mika ki gidan ki.. Toh me hakan ke Nufi..? Tafada tana kara kallon hotunansu dake yawo A Twitter,da sauran sakonnin Jama”arta.
.

Hajiya binta harta Fara murna,sai kawai taga Malika ta juyo cikin mamaki tana kallon Goggo baraka kafin tace”Kikace me? sai naji kamar kin ambace ni da Amarsu….? Tafada tana kure ta da ido,Tuni Hajiya binta tayi saurin tarewa da cewa”Tafiyarki Malika bada ke take ba,kawai tana zencenta ne…”Tafada bakinta na hardewa saboda tsoro.

Malika bata samu zarafin mgana ba mazan yan Daurin aure suka fara Shigowa,wani kawun Alhaji Abdulmalik ne ya Shigo yana Fadin”Kai yau naga jama”a Bura ube,????alqur”an harda wandanda banta tsammani ba,duk na gansu,yau gani ga Shugaban yan sanda na kasa gabadaya mukayi hannu dashi duk dalilin Auren Malika,kai babu Abunda zance sai Allah ya basu zaman lafiya kawai mallam”.. yafada yana saba babban rigarsa bakinsa har kunni.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button