MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Madam Dora ita ta sanyata amkaranta,kuma mkrantan ma,na Turawa,shiyasa tun malika na yar karama dabi’unta da kuma hallayanta yakoma na Turawa,domin a iya wannan Shekarun batataba sallah ba,domin madam dora bata koyamata ba toh masulmace ita,balle ta koyar da ita,wanda yakamata yazauna ya koyar da ita neman Duniya ya Rufemai ido,banda zuwa coci da karatun,bibble bata koyamata komai,domin tayi alqawarin bazata bar Diyar Juliyat ta subuce mata ba, ko kafin mahaifinta ya karbeta ta riga da ta gama tusamata duk wani akidansu.

Shiko Abdulmalik duk wani soyayyah da tanadi wa malika yake yinshi domin yana matsanancin sonta da kuma tsausayinta na yarda bata taba shan Nonon uwa ba,sai dai madara,kuma bata rayu da mahaifiyarta ba,Shiyasa ya dauki son Duniya ya doramata yakan samu lokaci yazo,domin yanzu yabar england yana kasar spain yana aiki da wani kamfanin sarrafa agogon Fata na maza da mata,gida kuwa sai dai yayi musu sakon kudi ko ya kirasu ta waya bai samun sararin zuwa.

Sai da aka kirasa aka sanar dashi Innaro ta rasu kana yaje Nageria lokacin kuma Malika tagama primary sch ,t yaso ya taho da ita,ammh madam Dora taki yarda ta dinga kawomai uzurin cewa Ga mkrantar ta,kar yatafi da ita karatun ta yatsaya,ita kuma bata so yatafi da ita ne yan”uwanshi su Farga Da Abunda ke Faruwa su riketa yaki dawo da ita,ta haka ta ribaceshi ya tafi ya barta,sai dai yaje ya sanar dasu da baki,babu wanda yanuna wani damuwa domin lokacin Abdulmalik shine Sarkin gidan sakamakon yana da kudi yanzu so babu mai ce mai baiyi Daidai ba.

Bai dawo ba sai Da ya bada kudadade sosai wanda zai bude wani kamfanin sarrafa atamfofi akano,domin yanzu Abdulmalik yana da hannayen Jari da yawa akamfanoni da dama,shiyasa yake da kyakyawan alaka da Turawa sakamakon yasan harkan kasuwancin da yadda zai habaka kamfani ya shahara lokaci kadan ba”a Rufe Shekara ba DAN KASUWA INVESTEMENT ajahar kano, ya kammallah kuma kafin lokaci kadan ya shahara ako”ina aka sanshi kafin arufe shekara biyu Alhaji Abdulmalik ya mallaki manya kamfanoni masu yawa agida Nageria,kama daga na sarrafa takalma,dana Sarrfa kayan yara maza dana mata,harda na taliya,sai kuma na Tumatur,bayan gidajen man dayake dasu wanda ya bude su da sunan MALIKA MALIK PETROLEUM NIG LIMITED Ako wata wata jaha afalin Nageria in kaje zaka ga brach dinsu,hatta a malumfashi bai san iyakarsa ba.

Bai tashi karban Malika ba sai da tagama Secondry sch dinta a england lokacin tana da shekara 18 Aduniya duk inda girma da budurci yake to Malika tagama mallakanshi,ammh kallon Farko zakayimata ka shaida da mahaifiyarta take kama,don tafi kama da baturiya Fiye da jinsu hausa Fulani,duk da baban inda yazo yana kokarin nusar da malika cewa itafa ba irin dangin mamanta bane ita musulmace,toh zata jishi ne kawai ko ya takuramata tayi sallah na ganin idonshi ne kawai yana tafiya zata watsar takama harkan gabanta,tun tana karama ta iya zuwa party da club clubs gashi ta koyo banzan dabi”,an yayan Turawa na Shigar banza bata kunyar Fitar da tsiraicinta waje,gashi ,ammh wannan kwakwalwar ta mahaifinta tayi gadonshi wajen kokari da himma,Abunda yasa malika tadawo hannunshi saboda mutuwar madam Dora ce,yasa bayan anyi Shagalin binneta ya karbo malika tadawo hannunta wanda bai wani samu matsala da sauran yan”uwan mahaifiyarta ba,Tunda ya cikasu da kudi kuma yayi musu alqawarin kawota duk bayan wani Tsawon lokaci.

A Canada Malika tahada digirinta na Farko akan Accounting daganan ta Wuce kasar America a babban birninta US tahada digirinta na biyu,bata dawo ba sai ta Hada takardan  Phd dinta,lokacin shekaru biyu da suka Wuce mahaifinta yagama cin moriyar Turawa suma sunci nashi yasa ya tararra yakoma gida akatsina ya gina wani tamfatsetsen gida mai kama da aljannar Duniya,kuma yayi aure da matarsa Hajiya Binta,yar”uwansa ce suka manna masa,saboda kudinsa,duk da ita Binta bata sonshi,dayake bazawarace,mijinta ya rasu ya barta da Diya daya mace JODA wacce bazata wuce Shekara 22 da biyu ba, ammh dole ta hakura Tunda kowa na Son daula ,uwa uba kuma tasamu jin dadin Rayuwa,domin shi ya kaita makka,kuma suna zuwa yawon duniya duk bayan wata daya bayan ya saka Joda a mkranta ,yanzu haka tana Final year dinta ne Barrau dikko dake zaria tana karantar SB NURSING.

Tun zuwanta gidan Ta fahimci daga yar har uban babu mai tarbiya da ilimi gabadaya jahilci na dawainiya dasu ranar da suka fara kaima Malika ziyara a US sai da ta zubar da kwallah yadda ta ganta da irin Shigarta da yadda ta maida rayuwarta wlh ko wasu Turawan Sun fita kyan gani,gashi ya shagwabata ya sangarta baya iya mata Fada,yanzu sai takama kuka tana hargowa,shikuma baya son bacin ranta Shiyasa duk Abunda tagama dama shi takeyi,gashi Tun tana karama kudi sun batata komai take bukata aikwai Shi bata taba neman wani abu tarasa,tun dataji lbrin mahaifinta yayi aure,taji tsani matar tukan ta ganta,sai gashi sun hadu banda harara babu Abunda ya shiga tsakaninsu,sai ma ita Hajiya binta ne Alhaji Abdulmalik ya umarta data gaishe da ita Malikan saboda lalacewa,koda suka dawo gida,ta nemi gayamai gaskiya game da yadda yabari Rayuwar malika ta lalace tana ya”mace,ammh sai yaki bata dama yace ta kyaleta taji dadin Rayuwarta Allah yaba mahaifinta Dukiya mai yawa so Dole tayi Abunda taga dama.,Tundaga Ranar Hajiya binta takawo ido ta sanya musu bata kara saka Musu baki ba, Ba kome zasuyi tasani akwai ranar kin Dillanci.

Bayan tagama karatunta dakyar Alhaji malik yashawo kan malika tadawo Nageria da zama saboda kula da kamfoninsa,saboda malika yarinyace mai kokari,she is very talent and smart,gata da wayau da kuma lura,shiyasa lokaci kadan Alhaji malik yasakarmata duka ragaman Kamfoninsa,domin ya Fahimci tafishi iya gudanar da komai,shi sai dai yana gida suyi waya agudanar da komai ita kuma malika taje ta tabbatar,kowani taro za’,ayi,daga gida Nageria zuwa kasashen waje duk malika ke Zuwa ta gabatar da kowani ragama,shiyasa kafin lokaci kadan Tayi suna Aduniya don Aduniya inda kafarta bai taka ba kadan ne,kuma babu wanda baisan Rashin tarbiya da rashin mutumci irin na Diyar Abdulmalik Dankasuwa ba,abokansa sunsha zuwa suna kokarin mai nasiha ammh duk sai ya toshe kunni,daga kuma ranar ya yanke alaka da mutum,masu kwadayi kuwa sunsha kawo tallah da tushen hada ya’yansu aure da Malika ammh yaki bin mganarsu domin malika yanzu ba aure bane agabanta batama sanshi ba,domim bayan dawowarta dakyar da yaki yarabata da karatun Bibble,dakyar kuma ya ke sata tana sallah ammh wani lokacin,sai tazo kwanciya take hadawa,tana Tura bakin ita an takurata tafison Rayuwar england taje coci taje Club,tayi yawo yarda taga dama,ammh dawowarta Nageria,yasa duk tazama atakure ga wani takuran wai sai ta dinga sallah,ita wlh bazata iya ba,mganar dressing dinta kuwa Shi baya ganin aibun hakan,domin rashin saka dankwalinta yasamo nasabane da tashin datayi cikin Turawa shibaya ganin hakan awani mtsala Tunda shima ba ilimin addin yake dashi ba.

Shiya samomata masu kula da ita mata har guda biyu mrry da Dose,sai excort dinta harsu ashirin masu take mata baya,in zata Fita kamar wata yar Shugaban kasa yadda combain yake biye da ita,ko kafin kace kwabo Alhaji Abdulmalik Dankasuwa yashahara kuma yayi Fice Aduniya bayan tarin dukiyan dayake dashi,ga kuma manyan hannayen jarin daya ke dashi akamfanonin kasashen ketare,inda malika take kula da Shige da Fitar komai,saboda hakanema yasa tayi karatu akan ilimin na”ura domin ta saukakama kanta wasu al”amuran rayuwa ta yau da kullun Tunda komai na business din mahaifinta ita ke kula dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button