MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Da mirmishi afuskar Saleem ya Waigo yana Kallon Goggo Hadiza yake Fadin”Goggo ki Shirya in mun karya zamu Wuce gidan Ummi..”Mikewa tayi tana Fadin”Tohm bari na Hanzarta ai yan Wutar ciki Sun tafi Su..”Tafada Tana Dariya.

Sai da ta Fita Afalon kana Saleem ya Manno Malika da jikinsa yana Shinshinar Wuyanta lokaci daya yana Shafa maranta Zuwa Cikinta,Dariya tayi tana Danna kanta bisa kirjinsa cikin Wani yanayi tace”Mallam,meka ke Bukata ne..”Akunne yayi mata Rada..”Ciki nake so nayi miki..”Ido ta zaro ta dago tana kallonsa cikin Mamaki tace”Ciki wani iri..?Kumatunta ya Shafa yana Fadin”Cikin Haihuwa mana Amanata,Hutun ai ya isa haka yakamata ama Hajiya kani ko kanwa..”Yamutsa fuska Malika tayi tana Fadin”Haba Daddy wani irin ciki kuma Ai ni gama kuma..”Wani kallo yayi mata kafin yace”Ko..? Saboda kinga na daga miki kafa kwana biyu ko..? Bari na Nuna miki har yau ina nan da karfina Insha Allahu kafin mu Tafi gidan Ummi yau sai nayi ajiya acikinki..”Yafada yana Kallonta ido cikin ido,Kwabe Fuska tayi zatayi kuka kawai taji bakinsa cikin nata,yana kissing dinta cike da kwarewa,itama Tallabeshi tayi Tana bashi Hadin kai,sai da yagaji don kanshi ya saketa yana Ajiyar Zuciya Kura ma juna ido Sukayi kafin Malika tayi Lum da ido ta koma Bisa kirjinsa tana Fadin” Ina alfahari dakai Mijina…A komai na Malika malika kaci gaba da Ramuwa Har Abada..

Dariya ya saki yana Sumbatar Saman kanta Kafin ya Mike ya Dauketa Cak ya Fara Tafiya da ita Zuwa sama inda Master Bedroom dinsu yake,Kallon Cikinta idonta yake yana Fadin” MALIKA MALIK SAI NA RAMA…Ammh bana Ramuwar da yawa Saboda Wani lokacin in Na rama ni nake Ramewa.. Dariya ta kyalkyalece mai dashi shima yana Tayata ahaka suka isa cikin makeken dakinsu da kafa ya Bude kofar suka ci burgi bisa Makeken gadonsu Cike da Kauna da Muradi mai girma Suke Gudanar da komai har abada bazasu gaji da juna ba,Kowani lokaci suka kebe kowannensu yana kokarin Farantama Dan”uwansa ne,wannan itace Kauna ta Gaskiya wacce ko man Tsufa bata yankewa har Gaban Abada.

TAMMAT BIHAMDULLAH

GODIYA TA TABBATA GA ALLAH (SWA) WANDA DA IKONSHI NE KOMAI KE FARUWA,KAMAR JIYA NE MUKA FARA MALIKA MALIK,GASHI YAU 05/03/2020 NA RANAR THURSDAY,MUKA KAWO KARSHENSA HAKIKA DUKKAN GODIYA TANA WAJEN ALLAH DA MANZONSA SALALLAHU ALAIHI WASALLAM,TARE DA IYALANSA DA KUMA SAHABBANSA

*Godiya ta musamman gareku *MALIKA MALIK PAID GROUP* da kuma HAFNAN AND JANAF PAID GROUP Bisa kaunar da kuka Nuna min wajen Siyan Littafina kuma ku ke Bina da Sharhi,Nagani kuma na yaba ina muku godiya tare Da Fatan Samun Cigaba arayuwarku ta Duniya gabadaya ina Rokon Allah ya Rabamana Ladan da mukayi dani daku wajen Rubuta Daidai acikin wannan Lbrin ya kuma yafemana Kura kuran da muka aikata Acikin wannan Rubutun,Allah ya saka muku da gidan Aljannah Firdausi Hakika Kalaman bakina yayi Kadan Wajen Mika muku Godiyata sai da Na bar Allah Shi zai biya muku Abunda kuka Man..Allah ya jikan magabata ya kuma Barmana Zumuncinmu Har Gaban Abada Ni Janafty Uwar Ladingo ina muku So Filla babu algus..*

Assalamu Alaikum Janafty Freeking Fans ga wani Albishir danake Tafe muku Dashi na Wani Sabon Lbrina mai Tafe da Sabon Salo wanda Zai Taba zukata wannan karon salon ba irin na bayane,Banta ba Dora alkalamina da irin wannan Salon ba,Na tabbata lbrin ZAMAN GIDANMU..! Mai cike da kunci Zai Taba Zukata dadama,Ma’u Yarinyace kin kowa kin wanda ya rasa wacce tatasO Acikin gidansu mai Tarin ya”ya ammh sai aka wayi gari Kannenta da Suke Kasa da ita Sunyi Aure Sun barta bawai don Bata da kyau ko tana da Wani Nakasu ba,sai don Ita nata Jarabawan Rayuwar kenan,Ta Fuskanci Tsangwama da Tsana,Kafin Allah ya Bata miji na Nunawa Jarida Burin kowacce mace,Ammh sai dai kash Nan din ma bata yi Dace da samun Jin Dadin da kowa yake Mata Fata ba,domin Abdallah Bashi da Ra”ayin kansa sai Abunda matarshi wacce ta mallakeshi dashi da Dukiyarsa gabadaya tace,ta Rabashi da kowa nashi Hatta da Uwar data Duka ta Haifeshi ta rabashi da Uban daya zama Ginshikin kawoshi Duniya ta rabashi da duk wasu abokananshi na Gari da yan’uwanshi ya kasance yana Rayuwa Wajen Bautama matarsa da yan”uwanta Saboda sakacinsa da kuma lalaci wajen addu”a,Kwatsam Rana Tsaka Ma”u ta yanki Tikitin Shigowa Rayuwarsa batare daya sani balle sanin ita matar tashi,Ma”u zatayi gwagwarmaya Sosai Zata Sha Wuyar RayuWa Sosai,Zata Samu Nasaran kwato Abdallah daga Hannun Muguwar matarshi..? Ko kuwa zata Samu Nasaran Rabashi da Wata karuwa wacce tayi Nasaran Shiga Rayuwarshi Saboda Sakacin Matarshi…? Duka Wadanan Amsoshin zaku Samesu ne ta Hanyar Biyan Naira 300 kachal ta wannan Account Nombar kamar Haka 0552179550 JAMILA UMAR GTB bayan kin Dauki Hoton Trancsation din kin Turo kai Tsaye ta wannan Nombar, 09069067488 ko kuma katin Waya na Mtna ta Wannan Layin 09069067488 Bayan kin Dauki hoton katin Kin Turo kai Tsaye,Ina Maraba daku Masoyana masu Son Cigabana kada ku Manta akwai Free Buk dina zai Fita Bayan Sallah insha Allah…

Gaisuwar ban Girma gareku????

Sahiba Hafnan
Sisinah Aisha Alto
Momyna Anty Hauwa
Dota ta Ladingota..

ALLAH YAYIWA RAYUWARKU ALBARKA YA KUMA DAFA MUKU FIYE DA YADDA KUKE DAFAMUN..Ameen

Janafty Aka Shakira ke Cewa BISSALAM????????

SHAKIRA
JANAFTY
MOMYN LADINGO
ANITHA
SUNIATIN

????????????????
E-book Creater by Sardaunah
08066046091

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button