MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Hannayensa Duka ya Tura acikin aljihun Wandon barcinsa na pjm,Yana kallon Fuskar malika cike da so da kauna Hade da Wata kewa,Rankwafa yayi yana kallon karamin bakinta da kirjinta wanda ya kara cika,Kamar zai kai hannu ya Shafa mata Fuska sai kuma ya Fasa,yana tsuramata ido saboda yaga kamar tana motsi kenan ba barci take ba,Asirinta ne ya Tonu da mirmishi ya Subucemata bata Shirya ba,Agaggauce ya dago yana Kara Tamke Fuska yayi Saurin Juyawa zai Tafi ta damko hannushi da Hanzari,bai waigo ba yace cikin muryan Dakewa

“Meye haka kuma..? plz leave my Hand..”Yafada yana jin Wani iri kawai yadda ta kamkame hannun nashi,Jin Haka yasa sai ta kara narkewa cike da Shagwaba take Fadin”Haba mallam..,Ni..Ni ko nice fa Yar Amanarka kadaina sona ne yanzu..? Muryanta ta narkar dashi ya dago yana kallonta yadda take wani lumshe ido Baki ya tabe kafin yace”Keba Amanata bace,don da kin dauki kanki ahaka da bazan hanaki Abu ba,ki mtsama sai da kikayi,Mganar ko na Daina Sonki ne Eh na daina Sonki ko da mgana ne..”Yafada yana Tara gashin Giransa waje Daya.

Mirmishi ta sakarmai tana kokarin mikewa kenan Sai ga Saleema ta Shigo,ganin hannunsu sarke cikin na juna yasa ta koma da baya tana Fadin”Oh!Srry…”Tafada tana kunshe dariyanta ganin yadda ya Saleem yake maka mata Harara,Ganin haka yasa malika ta sakeshi tana kallonshi bai kara bi ta kanta ba ya Fice daga dakin Duka hannuwansa suna cikin Aljihun wandon barcinsa kamar wani basarake.

   Girgiza kai tayi ta mike daga Kan gadon Tiolet ta Shiga ta Dauro alwala tazo ta yi Shafa’i da Wuturi kafin tayi Shirin barci ta kwanta tana Tunanin mallam dinta wanda tayi Kudiri Niyyar sai sun koma Zamfara zata Shiga Fagen lallashi Ta lura bazai sauko da Wuri ba,har tayi barci Saleema bata Shigo ba itako Saleema dakin Hajiya taje tayi kwanciyarta Azatonta ya Saleem zai kwana wajen Malika ne,Tunda ya Sadiq na dakinshi.


Washegari Tun 7 Saleem yakai Sadiq airport inda ya Shiga jirgi yakoma wajen aikinsa,itama Saleema koda karfe 9 tayi ita da Direba sunyi nisa ahanyar komawa kano,dama Weekend ne tazo,suna da aiki sosai a asibiti ,Shima Saleem wajen 12 din Rana ya Fito cikin Shirn sa na Tafiya yacema Ummi zai Wuce da Ummi tamai mganar ba tare zasu Tafi da malika ba,sai ya tamke Fuska yace gobe Direba yazo da ita,shi yanzu sai ya bi Wani waje ba zamfara zashi kai Tsaye ba,kanzil Ummi batace mai ammh Tana Lura da Saleem da malika wannan Zuwan ba wata jituwa atsakaninsu,bata yi Shisshigi ba balle tazo taji kunya Fatan isa lafiya tamai Domin tasan ko tace ya tsaya Su Tafi tare da Malika sai ya bata mata rai Don Shigen Taurin kai gareshi.

Malika bata da masaniya sai dai Fitowa tayi ta iske Saleem ya Tafi,tana duba wayarta kuma taga ya Turo mata sakon Ummi tace mu Taho tare nayi mata karyan Ba Zamfara zani Direct ba,Ban yi ra’ayin Taho dake bane,so wanda ya kawoki sai kimai mgana ya maidoki.. Sakon nashima Dariya ya bata sai Da ta kyakyata ita kadai tana kaunar Halin Mallam Shifa akomai na MALIKA MALIK..”! Sai na rama ne Bata damu ba illa itama ta Hau Shirin tahowa don batason daga gobe takara kwana kada ta kara wani laifin.

Joda ko da ya marwan basu Fito ba sai bayan Azahar Amare kenan Akwana a Hantse inji Hajiya Babba,Dukkansu sai Shekin amarci suke suna walwali kamar Zara da Wata,daga gani Ya marwan baiyi Wasa ba,don Joda idonta ya tona mata asiri saboda yadda ya kode saboda kuka,koda suka kebe da malika adakin Saleema kuka ta sakama ta Ita kuma tana mata Dariya,aranta tana Fadin!Uhmm joda aike bakiji komai Tunda har kika iya Tafiya da kanki,nice Wacce tafi kowa jin maza Tunda harda su Dinki da jinyar Sati biyu,ammh afili sai ta Shiga lallashinta da bata wasu Shawarwari Wadanda zasu amafeta,tare suka Wuni Ranar hatta Dinner ma tare suka taya Ummi Shiryaawa sunayi suna Hiransu Cike da Kaunar juna da Soyayyar,wanda kaunar Ummi ya cika ransu ayayinda itama kaunar Surukan nata ya ki Boyewa acikin Ranta tayi ta godiya ga Allah daya Hada Zaratan ya’yanta da mataye na gari tare da Fatan zaman lafiya a tsakaninsu har Abada…


Malika Tun Safe tagama Shirinta ita da Ayda da Merry,Direba ya kwashesu sai Zamfara,sukansu su Ummi da Abbi Sunji kewar Tafiyar malika mussaman ma Ayda Wacce ta Shiga Ran kowa.
 
Da Wuri suka isa Wajen Azahar Direba Ruwa kawai yasha ya juya ita kuma suka zage suka gyara gidan Abunda ya bata mamaki wlh Saleem bai taba abinci datamai ba,harda miyan data hadamai,dama ya Fada,ta zata Wasa ne ashe da gaske yake miyar dai batai komai ba,da soyayyen Nama,wanda saboda ya Soyu sosai,sai ta zubar da Shinkafa kawai ta gyara kicin din kafin ta Dora girki Duk da Uban gayyah baison da Dawowarta ba,so take yau ta wanke laifinta kaf.

   Sai Bayan la”asar ta Dora girkin Megadi tabama kudi yayi mata cefanan miyar ganye Ta yimai Tuwon Semo,don ta san mutumin nata yana Son Tuwo kowani iri ne yana Son Shi da miyar ganye,bata gama ba sai gabda mangariba,lokacin ta Mulmulashi a leda ta zubasu cikin kololinta masu kyau da tsari,Ta gyara kichen din kafin ta Fito tA karbi Ayda ita kuma saka merry tace takara gyara mata Falon ta sakamata Socket din Turaren Wuta.

Wanka ta Shiga tayi ,tayima Ayda suka chakare,bayan tayi sallar Mangariba,Wani material less dinta ta saka Doguwar riga wacce ta Fito da Tsarinta tsab dayake Rigar Ashape ce,ta ci daurinta wanda ya zubomata da gashinta bayan ta saka band ta matseshi ta baya,Ayda taci wata Doguwar rigar bulawus mai bulewa itama harda Jan baki Malika ta saka mata domin Taran Abbanta…

  Bayan issha’i motar Saleem ta sawo kai gidan Bayan ya Zuba hon megadi ya wangalemai get ya Sulala ciki,Malika na jin tsayuwar motarshi yasa ta Fada daki da Sauri ta Fara mata kanta Feshin Turare,sai da tabbata da kowani lungu Ya samu mazaunin kamshi kafin ta Fito Falo tana takun isa,Shiko Tunda ya doso kofar Shigowa Falon,yaji wani kamshi ya dakeshi Lumshe ido yayi yana Shafa kanshi afili ya Furta”Lalle na yarda mata ne Ni’imar cikin gida..”Yake Fada yana Mirmishi Shi kadai kafin ya saka kanshi cikin Falon da sallama hannunsa na kada key din motarsa sai wayarsa dake Rike A hannunsa.

   Da Malika ya ci karo Wacce take kasheshi da murmishinta Tundaga Nesa,wani sanyi ya ratsashi tsaye yayi yana kallonta ita kuma tana wani Taku Zuwa gareshi kamar Wata Wahainiya tana Zuwa ta Fada jikinsa daga ita har Ayda tana wani Narkemai ganin Sunyi baya ne kamar zasu Fada yasaka Duka hannunsa ya tarbesu dashi ya Rumgumesu tsam ya matsesu yana sakin Wasu tawagayen ajiyar Zuciya,Ayda ko tana ta taba Sajensa tana gwarancinsu na yara,tana wangale baki bata gane iyayen nata Sun Shiga wani yanayi ba..”

Kiss ta sakarmai awuya tana Fadin”Nayi kewar malamin mijina..”Tafada tana,Kara lafemai kamar wata mage,Ajiyar Zuciya ya saki kafin yace”Nima nayi kewar marajin matata Sosai,Malika kece Farincikina..”Yafada yana Sumbatar Tsakiyar kanta,Shuru tayi kafin tace”Baka na Fushi dani ba,kai akomai na Malika sai ka rama ko..? Yar Dariya yayi kafin ya Rabata da jikinsa yana kara Rike Ayda yace”Ashe kingane,Ammh Kadan nake Ramawa saboda in na Rama da yawa yana Zurmawa dani..”Yafada yana Dagamata gira,Hannunsa ta riko tana Dariya tana Fadin”Tuba malika take,Mallam yayi mata Afuwa bazata kara nuna damuwa ko Bacin rai game da Hukuncin ka ba..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button