MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Suna tafiya Zuwa hanyar dakinsa yace”Gud matar Aljannah,Allah miki albarka ammh na dade da Hucewa kawai Ramawa nima nakeyi..”Yafada suna Shiga dakinsa kan gado ya kwantar da Ayda kafin ya kamo Malika ya Rumgemu yana Faman Shinshinar Wuyanta,hannayensa kuma yana karakaina ajikinta,itama matseshi tayi tana Sauke ajiyar Zuciya kafin ya lalubi bakinta yana bata wani irin kiss mai tsaya a zuciyar wanda aka yimawa.

   Da malika taga Saleem ya Rikice mata,Dakyar ta yakice jikinta ta Dauki Ayda ta mikama Merry ta dawo Mallam ya Dasa sabon karatunsa,domin yayi kewar Dalibarsa tasa sosai,Susuce mata yayi yana zayyanamata yadda yayi kewarta itama zagewa tayi tana mai salo salo mai Tafiya da Zuciyar masoyi,sai da suka dawo natsuwarsu kafin ya Kwasheta Zuwa Tiolet ko awajen wankam ma Rabi da rabi Duk Romance ne da tsotse tsotse,Shikanshi wanka dakyar sukayi bayan kowanne yayi wankan Tsarki,Suka Fito suka Shafama juna mai cike da Soyayyah ko abinci ma Ranar cikin Bedroom ta kawomai nan suka ci,tana kan cinyarsa tana cinyar dashi,shima yana cinyar da ita cike da Soyayyah da kauna,Ranar dai an gantale suka kare????????,don kololin kadai ta tattara Zuwa kichen,kafin ta Dawo suka Cigaba daga inda suka tsaya Ranar dai Ko Ayda Wajen merry ta kwana Tunda taga iyayen nata Tunda suka Shige daki ko lekowa basuyi ba,Shiyasa itama tayima Ayda Shirin barci suka kwanta.

Ko Washegari basu Fito da Wuri Ba,sai da Merry ta buga musu kofa Ayda na Rigima kana malika tazo ta amsheta,Ranar Saleem ko aiki baije ba yana Nanike da Matarsa da yarsa Abun Alfaharinsa wanda ko Kuda bayaso ya tabasu saboda yadda yake Kafa kafa dasu,itama malika haka take,Duk Abunda tasan Saleem bayaso tana Gudunshi,shiyasa yanzu karatun nasu ya Dau Nisa,don Malamin nata ya Rike mata wuta,Rabi karatu ne Rabi kuma Karatun Samun lada ne,Wanda dukkansu yanzu sun zama cimgam din juna ko gajiya basuyi,kowanne baya gajiya da Rabar jikin Dan’uwanshi.

Ina kai kyakyawan gaisuwata Zuwa gareki KAWA???????? MALAMA JUWAIRIYYAH, Kawata abokiyar Cin mushena,alherin Allah yakai miki Aduk inada kike,Allah kuma yabada Sa”an mkranta,Ammh wannan Sakon gaisuwa ne da kuma cigiya don kwana2 najiki Shuru ne,Allah yasa Lafiya Ameen

Mommyn ladingo..

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

Mallakar:Janafty????

KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada

34

……………….”””Rayuwar Farinciki tare da Wata Soyayyah mai tsayawa azuciyar masoya Shi Saleem da Malika Suke gudanarwa gwanin ban Sha’awa ga Wanda ya gani,Yadda take mai ladabi da biyayyah yafi komai burgeshi da ita,uwa uba kuma komai zata gudanar sai da Shawaranshi da kuma izininshi.

Malika tana da tarin Dukiya wanda batasan iyakarta ba, akallah bankunanta sunfi guda 5 kuma kowanne banki Duk wata riban kudi na miliyoyi suna Shigo mata harma ta rasa wani Tunani zatayi domin Taimakon al’ummah Dashi Domin dai ita bata da muradin kudi ayanzu haka Kudinta shine mijinta da Yarta,yana mata komai na bukatan Rayuwa da cigaba baya duba tana Dashi komai dayasan hakkinshine yana kokarin kare mata shi Har gobe Kudin da malika ta mallaka bai taba Tsole mishi ido ba,Yana kokarin Dorata ahanyar mai kyau tare da kyakyawan Shawara Domin Rabauta daga Duniya har Zuwa gobe kiyama..

Mganar Filayen datace a bincikamata a malumfashi an samu har Saleem yaje ya gani an kuma yi ciniki da dillallai an biya kudin manyan Filayen Guda biyu wanda aka bashi Duka takardun Filayen mai dauke da Sunanye malika,batayi wasa ba tabama Saleem Duka dama,shi kuma sai ya Umarceta data bama kawun nan Daddy dake nan Malumfashi kwangila kula da ginin makrantan da masallacin Saboda sune ke gari,shi kuma yana Nesa,ammh yamata alqawari lokaci bayan lokaci zai Dunga Zuwa yana Duba aikin.

Haka ko akayi ta Tura musu Kudin da zasu isa Duka aikin nan da anan aka bama ma’aikatan gini kwangila,suka Fara gininsu cikin Nasara Abunka da Kudi kafin kace kwabo gini yayi Nisa kuma Alhamdulillah Da Saleem zai je Duba aikin Tare da Malika Sukaje,taga komai da idonta ta kuma yaba,awajen ma Sai da tayi kwallah Saboda Tunawa da Daddyta datayi ammh tana mai addu’an Allah jikansa da Rahma.

Tabiya Family house dinsu sun gaisa Duk da bata zauna ba,tama iske Hajiya ta koma katsina Satin daya gabata so basu hadu ba,Haka Dangin Daddy suka taru suna sakama malika albarka,itakuma sai tace su godema mijinta Domin Shine Silan zamowarta Duk Abunda ta zama ayanzu,Domin da babu Shi acikin Rayuwarta da yanzu batasan awani Hali rayuwarta Zata Shiga Ba.


Joda da marwan Sati biyu sukayi gidansu Ummi suka tatattara su ka koma lagos wajen aikin mijinta,wanda kafin su tafi sai da ya kaita malumfashi tayi sallama da yan’uwa da abokan arzuka kafin yakaita Zamfara tayi musu kwana daya ya kaita katsina wajen Hajiya nan ta kwana daya,tana Dawowa suka tattara suka tafi suka bar su Ummi Cike da kewa.


INA LABARIN ZAHRA

Zahra dai tana cikin gararin Rayuwa Domin daga Abba har momi sun Fita batunta bamai Kulata balle ya Shiga Sha’aninta har gwarama Nadira takan xauna ta lallasheta in taga tana kuka,ko ita din ma ba kamar da ba,kowa laifinta yake gani.

Zahra kishinta yakaita ga aikata Abunda yazo yana damunta,gashi tana Bala’in son Saleem ammh lokaci daya Zuciyarta da Sharrin Shedan suka Taimaka wajen Nesanta ta da Abunda tafi kauna Duk Duniya,bata Fitowa kullum cikin daki tana kwance tana kuka,shiyasa kafin tagama idda duk ta lalace ta kwarzane kamar ba Zahra ba mai iyayi da Rawan kai yanzu Duk bashi,sai ki ganta ta zauna tayi Shuru tana Sharan Hawaye kamar ba ita ba.

Ganin haka yasa sai momi ta Fara jawota ajiki ganin tana neman kashe kanta da Tunani,ammh Duk da haka zahra bata dawo da karkashinta na baya ba,Duk da ko Daga momin har Abba yanzu Sun Yafeta sun koma mata addu”an Allah ya Cire mata wannan mugun kishin kuma ya bata Wani mijin na gari.

Satin daya wuce suka Sha Bikin ya Nadir inda ya Auri Wata Scientics Aisha bala,Itama anan Asibitin Aminu kano,anan Suka Hadu suka Fara Soyayyah har ta kaisu ga Aure.Auren da akasha Shagali sosai Duk da Zahra ta dan Warware ammh ba kamar da chan ba,suna zaune awajen Asibtin Aminu kanon nan ya Nadir ke da gidanshi mai kyau da tsari.

Awajen bikin ne Nadira ta Hadu da Wani DR HAMBALI, wanda ya kasance Shima likita ne Anan Mallam Aminun kanon,kuma Senior Ya Nadir ne don ba yaro bane zai kai Shekara 45 aduniya yana mtsayin Constlant ne yanzu,matansa Biyu, ya’yansa Biyar,Bakano ne gaba da baya,yazoma Nadir Daurin Aure Anan yaga Nadira kuma yaji ta Shiga Ranshi har kuma ya gabatar da kanshi kuma nan da nan Nadira tayi accepting dinshi,bayan ya Sanarma Nadir din shima yayi Na’am da mganar,har kuma ya Sanar ma da Abba kuma ga duk alamu Nadira tana son Dr Hambali.


Nadira tana kwance Suna waya Da Dr Hambali,Zahra na gefenta tana buga game awayarta taji Nadira na gaisawa da Ya”yan Dr Hambali Abun yabama Zahra mamaki har sai da ta dago tana binta da kallo,ganin yadda take Wani Lallaba yaran kamar Wasu ya’yanta na cikinta tana ji baban ya karbi wayar Nadira ta chanza murya tana mai Shagwaba,Galala Zahra tayi tana bin Nadira da kallon mamaki,wacce Tun lokacin da Zahra ta Fara mata kallon Tuhuma bata bi ta kanta ba sai da Sukayi irin Rabuwar da suka sabayi Cike da kaunar juna,kana ta dago tana kallon Zahra bayan tatashi Zaune tana kallonta kai tsaye tace”Best lafiya..? irin wannan kallon ai sai kisa na kware..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button