MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Abunda yafimai Ciwo shine yadda Saleem ya ci mutumci Malika,kuma ya tozartata mafi munin Tozarci kamar wani dabba,wanda baije mkranta ba,ko wanda bai taba sanin Addinin ba,ai duk mai cin zarafin mace dan akuya ne,kuma duk mai Ramuwa kan mace tayimai Abu bai cika jarumi,macen da”aka halliceta da hakarkarinka,kafita daraja ta ko’ina kana gaba ita akowani fanni,kai Shugaba kake gareta,ammh saboda sakarci kakoma bayanta kana wani kunfar baki,Haba ai aiko anyi asara ba kadan ba,Shi ji yake kamar Saleem ba jininsa bane,Tunda har zai iya tozarta mace,wanda Shi Tunda yake baitaba kwatanta ynkuri tozarta mahaifiyarsu ba,balle yace gado yayi ko kuma Abunda yaga anayi ne ya kwaikwaiya,Toh ba daya kanwar Biyu kawai Duniyace tare da Shedan suka kulla Abota dashi yaci zarafinta,daga karshe ni kuma ya batamin suna,ammh bakomai Duniyace ta ishi wanda baizo bama,ballatana wanda ke cikinta,Haka Abbi yayi ta sake sake aransa,Abun yaki barinsa ko kadan.

Sai da Ummi tazo tayi ta lallashinsa,tana bashi baki kana ya dan sausauta damuwarshi,yana kada kawai,domin Shi kadai yasan Abunda ke ranshi,na bakinciki da takaichi,haka mutanen kumo suka koma suma da lbri mara dadin ji,Itako Hajiya Babba baki ta rike tana Fadin”Anya ni kabiru shigan Salihu aikin yan sandan ba shaye shaye yaje yafara ba..?

Ya marwan ne yace”Ba wani shaye shaye Hajiya,dan iska ne kawai,kuma ba komai yakeso yaga ya cimma ba,sai bata sunan Abbi aduniya,kuma ya aikata hakan shikenan aie..”,Yafada yana huci Girgiza kai Hajiya tayi kafin tace”Anya ni ina tamtama kila dai yafara shan Wiwi ne aboye ba”a sani ba,ammh cikakken mutum mai hankali bazai aikata Abunda ya aikataba gaskiya..”Tafada tana jadadda Bayaninta,ba wanda ya sake kulata,domin kowa yasan Saleem ko taba bayashi tsabar Wulakanci ne da tozarci kawai,Shi kanshi marwan Saboda halin da”ake ciki ya sa yakara kwana biyu kafin yakoma,rana daya Suka wuce da Sadiq.

Itako Saleem dataji lbrin Abun yayi mata dadi,domin tace Abunda ya saleem yayi Shine daidai,domin ita haka kurum ta tsani Malikar wlh,taji yadda aka koyamata Hankali,tayi kokarin kiran Layin ya saleem,din ammh bata tafiya,sai da sukayi waya da Sadiq ne yake sanar da ita ai Saleem baya kasarma,shi ya sanar da ita Abunda ya faru da Malikar da mahaifinta,wanda ko alama bata tsausaya musu ba,sai ma Allah kara datakeyi acikin zuciyarta,gefe daya kuma tana sakama Saleem Albarka.

  ***

Kwana uku kenan da Faruwar al”amarin Inda Malika ta farka,tunda ta farfado,ta kuma dawo daga hayyacinta ta tuna dukkan Abunda ya faru da ita batayi mgana ba,illah kuka datake tayi,wanda baya da Sauti sai dai kaga hawaye nabin gefen idonta yana gangarowa,komai sai an mata bata iya zama saboda Dinkin da akayi mata akasanta,wadanda dai ada ta raina su ke dawainiya da ita,Hajiya binta da joda,wadanda tsausayin Malikar yakasa barinsu sutuna Abunda tayi musu abaya,Bata iya mgana sai dai kallo da ido,bini bini kuma sai kuka.

  Ayayinda Alhaji Abdulmalik kam jiki sai godiyar Allah,domin bakinsa ya karkace baka iyama jin Abunda Yake fadi saboda baknsa babu Dadi,ammh kowa ya Fahimci Malika yake tambaya,wacce kuma anki sanar da ita Halin dayake ciki ne kada takara shiga wani hali.

Yan Malumfashi Sun koma,illah Kawu Shitu da”aka bari sai yadan kara kwana biyu,saboda ya taimakama Hajiya binta da jinya,Tunda Masu laluran guda biyu ne,kuma ita kadai bazata iyaba,Don ma Joda na tayata kula da Malika,shiyasa Abun yazo mata da sauki.

Sai dai Malika tayi sati kana tafara koyon zama da dubara,kuma aranar ne tayima Hajiya mgana tana tambayan Daddynta,Dafa kafadanta tayi tana Fadin”Ina so ki saurareni dakyau Malika,ki kuma yi hakuri da Abunda zan sanar dake,bisa faruwar Abunda ya Faru dake,shiya yi sanadiyar Faduwar Mahaifinki har Dalilin haka yasa ya kamu da ciwon barin jiki,yanzu haka shima yana kwance acikin asibitin nan..”

Zaro ido tayi kafin ta fashe da kuka tana kokarin tashi,ta riketa Tana lallashinta,ammh ko sauraranta batayi kukatake Wurjanjan tana kiran Sunan Daddyta nan Hajiya binta ta kalleta tana Fadin”Kidaina kuka bari likita yazo indai da yuyuwar zuwa ki ganshi sai na kai ki ki ganshi,ammh tabbas Alhaji yaga jarbta asakarma ka y’a adaren Aurenta,kuma bayan angama cin zarafinta…,”Tafada tana jin kunar Abun.

Cak Malika ta tsaya da kukan datakeyi kafin ta Dago tana kallon Hajiya Binta tana Fadin”Saki kuma..? Ta ambata tana jin  wani iri acikin jikinta,gyada mata kai tayi kafin tace”Kwarai da gaske,bai barki ba,sai da ya Rubutu miki takardan sakinki Malika,bayan ya dawo ma mahaifinki dukkan kyautan dayayi zuwa gareshi,kuma ya sanar dashi cewa bai aureki don yana Sonki ba,sai don ya rama Abunda kijayimai….”Kuka yakara kwacema Malika,tanayi har takoma Daga kwance tana Tuna kalaman Saleem inda yake Fadin Zan Lalata miki Rayuwa adare Daya,kamar yadda kika lalatamin nawa a Shekaru biyar da suka Wuce..

Shi kawai take tunawa tana tsiyayan kwalla,Tana kuma jinjina kai,bata gama Tunani ba,Hajiya binta ta katseta da cewa”Kuma yanxu amganar dani ke miki,baya kasarnan akace Tun ranar daya aikata gudurinsa yasa kafa ya bar kasar gabadaya,Abun takaichi da haushi kamar yadda Aurenku ya game Duniya haka lbrin sakin Aurenki yagama zaga Duniya,saboda rashin adalcima muna Asibtin nan,Yan jarida sun zo har nan,suna kokarin jinta bakinmu akan gaskiyan Abunda ake yawo dashi Aduniya…”Ai sai Malika taji kamar zata Shide,yanzu kamar ita Malika malik,itace wannan Abun ya faru da ita kamar amafarki,yanzu duk jin kanta da yansda maza ke tsoronta,ammh an samu mai Wulakanta rayuwata haka bayan ya tozartani..? take tambayan kanta tana kuka harda rike kai.

Kallonta Hajiya binta tayi cikin tsausaya take Fadin”Kuka yazama dole Malika,ammh kuma bazan gaji da Furta muku wannan kalmar ba keda Alhaji,wlh ko kaffara ba zanyi ba,Allah ne,ya turo saleem ne cikin rayuwarku keda Mahaifinki domin ya koya muku Hankali,kuma ya nuna muku Akwai Abunda kudi da takama bazasu taba baka ba,yanzu Duk kudin Abbanki bai isa yadawo miki da budurcinki ba,kuma bai isa ya dawo dake Daga Malika bazawara,zuwa Malika budurwa wacce batataba aure ba,Bai isa ya kankare ikon rabbi ba,Domin bakin Alkami ya rigaya daya bushe,Da ace ke dashi kun dauki Nasihata,da kuma mganata akan ki gyara rayuwarki,da duk haka bata Faru ba,ammh kuka kekesa kasa kuka jina,kuna ganin kamar ina Takura miki ne,gashi yanzu komai ya kwabe Zakuyi Nadama sanda bata da amfani . “Tafada tana Share kwallah.

Hannuwanta ta sanya ta toshe kunnata,tana kuka harda jijjiga,kamar wata mahaukaciya,bata son mganar,ji take kamar ace yanzu ta mutu kwata kwata bata Aduniya,da wannan Abun kunyar dake rayuwarta,Ranar dai Wuni tayi kuka kamar wacce ta zauce,sai da akayi mata allurar barci kana aka samu sauki.

BAYAN KWANA BIYU

An samu cigaba sosai abangaren Daddy,wanda har ana iya Fahimtar mganarsa,kuma hakan ya samo asali ne,daga Ganin dayayima Malika taji sauki,haka ta Rumgumeshi tana kuka tana Fadin”Am srry Daddy it my Fuilt…”Take fada,shiko hawaye yake yana Fadin”A”a babby,ba kuskurenki bane nawa ne,da”ace Tun farko na doraki kan Turban da Addininmu ya koyar ban barki kara zube ba, na tabbata da baki hadu da saleem ba,balle har ki cimai zarafi ya biyo yaba yayi ramuwa gareki,na dora laifin duka akaina babby,…”Yake yana tsiyayan hawaye,kawu Shitu ne yasa baki yace in bai bar kuka toh Malika bazata kara zuwa wajensa,ba shine yasa ya daina kuka,ammh ya kafe ta da ido,yana hango tsabar rama da kuma yadda komai na Babby ya chanza,tana zaune Shuru tayi tagumi bini bini kuma ta hau sharan kwallah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button