MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Sai gashi Abbi bai baro katsina ba sai da sukayi sallar la”asar kana suka dauko hanya kamar karsu rabu,hakika Alhaji Abdulmalik yaji dadin zuwa Abbi da duk abubuwan dasuka tattauna,yanzu Fargabansa daya da kuma Tunaninsa taya zai Tunkari malika da wannan mganar,domin yasani ko giyan wake yasha bai da ikon sanar da ita komai,gabadaya ya Shiga Rudani yakasa samun mafita,kuma bayaji zai iya hakura zuru”ar kabir kumo kamili da dattako ya Wuce Malika domin bayan shi din,ba uban da zaiji hallaya tare da Abun Tir game da malika kuma ya amince Dansa ya aureta,wannan sai uba na gari,da Amini na gari.

Shiko Abbi har suka kai Abuja zuciyarsa na harbawa,yana so ya gano mai Saleem yagani wajen wannan yarinyar da zaice anema masa aurensa,shi dai bai hango wani quality wajenta ba,illah tarin munin dabi”unta,ada ya karaya ammh kuma sai ya duba da ya amince saleem ya auretama wani jihadi ne babba,toh ammh Abu daya yake son sani wani dalili ne ya sanya Saleem ke son aurenta? in har Abunda zuciyarsa ke zargi ne,to bazai lamunta ba,sai da ko yakira Alhaji Abdulmalik yabashi hakuri,ammh bazai yarda ayi Abunda daga baya zaiji kunya ba,da girmansa da komai..

    ***

Kwance yake akan makeken royal bed dinsa wanda yaji Shimfudun alfarma,katon bedroom ne mai dauke da gado,sai dressing mirror,sai wani katon wardrope wanda ya cinye rabin dakin akallon Farko zaka Fahimci ma mallakin dakin baison hayaniya da tarkace,domin daga kayansa dake sagale a hanger,sai jerin takalamsa kama daga sawu ciki,zuwa budaddu wanda suke jire bisa wani Stool mai Fadi da Tsawo.

Dakin malale yake da wani Cafet mai taushi da Santsi bayan kuma daga Fentin dakin har kalan Funutures din ash and black ne.komai dai ya tsaru kamar ba dakin Namiji ba,saboda yadda komai yake atsare.

Mamallakin Dakin yana kan gadon kwance dagashi sai bakin dogon wando,jikinsa babu Riga,gabadaya Fafaffadan kirjinsa wanda ke cike da gargasa,ya bayyana awaje,Mike yake sambal bayan duka idanuwansa suna sama suna kallon Rufin dakin,yayin da duka hannuwansa ya Sagale su abayan keyanshi yayi matashi dasu.

yayi zurfi cikin Tunaninsa kafin karar wayarsa ya Dawo dashi,da hannu ya sa yajawo wayar wanda ke kan Stool din gadon,sunan daya gani ne yasashi sakin Siririn tsaki Afili ya Furta..”Kai Dis man,in maye ne in yakama mutum wlh sai ya ga bayansa haba..”

Yafada irin Abun ya ishesa Din nan, dankawafar da wayar yayi yana tsaki bayan naga sunan mai kiran FRIEND ne da manyan baki,Idanuwansa ya kankance aransa yana Jin in ya hadu da saleema sai yaci ubanta,Bakin yarinyarnan kamar sikat,saboda rariya jikinta narawa komai akayi agida sai ta kira sadiq ta sanarmai kamar wata Sakarya,Abunda ya lura dashi daga shi har ita Tsofaffun munafukai.

Tun jiya daya dawo Sadiq keta kiran wayarsa yana kin Dauka,domin yasan Tatsuniyar gizo bata wuce ta koki,Mganar malika ne yake so yamai,shikuma haryanzu bai shirya Amsa wata tambaya ba,ko kuma ya budi baki yayi bayani Abunda ke gabansa kawai Sai ya rama ne,shiyasa yake ganin kiran yana kin dauka.

Wayar nasa ne takara dauka Tsuwa wannan karon dogon tsaki yaja ya mike daga kwance ya dauki wayar yayi niyyar ya dagane ya danna mai ashar sai yaga sunan Abbi na yawo asaman Sreen din wayar tasa,jikinsa na rawa ya daga kiran yana Fadin”Barka da Safiya Abbi.?

Dagachan bangaren Abbi ya amsa da cewa”Lafiya lau Acp,ya aikin? ya karba da”Alhadulilallah Abbi ya gida dasu Ummi…? Abbi yace”Gida dukkansu suna lafiya,jiya kuma sai ka tafi ba sallama ko? Kunya takamasa sai ya kama sosa bayan keyanshi yana yar dariya yarasa tacewa,yar dariya Abbi yayi irin nasu na manya kafin yace”Mu bar wannan mganar,yanzu dai dalilin kiranka danayi dama juz na tambayeka tsakaninka ga Allah ne,Shin meye dalilinka nason Auren Diyar Alhaji Abdulmalik Dan kasuwa..?

Gaban Saleem ya Fadi nan da nan zufa tashiga ketomai ta ko”ina azahirin gaskiya bazai iya sanar da Abbi dalilinsa na Son auren malika ba,kuma bazai iya sanar dashi don Allah yakeson aurenta,kada Allah yakamashi da laifin karya,gashi Abbi ya daureshi da cewa ya sanar dashi tsakaninsa da Allah.

Kame kame yafarayi Muryansa na Rawa Abbi ya katsesa da cewa,”Kaga Ka natsu ni ba ina Turke ka bane naji dalilinka,ni Abu dayane nakeson ji,Allah yasa ba zargin danike akan ka bane,..? Saleem ya aro baki dakyar yace”Abbi wani zargi kake akaina..?

Kai tsaye Abbi yace”Ina tsoron ko saboda kudin mahaifinta kakeson auren ta..?Ajiyar zuciya ta kwacema saleem ya saukarya yana jin wani sanyi aransa kai tsaye yace!Wlh Abbi Waye Allah..? shine Shugaban halittun duka Duniya ko? Toh Tallahi ba saboda kudin mahaifinta bane,haba Abbi kafi kowa saninmu,mu har wani kudi ne zai Rufemana ido,me muka nema muka rasa agidan Duniya..”

Mirmishi Abbi ya saki kafin yace”Alhamdulillah,Naji dadin jin haka,dama Fargaba na daya kada wannan ne dalilinka daga baya azo ana jin kunya,Masha Allah jiya naje katsina na hadu da mahaifinta,dayake munada kyakyawan alaqa dashi na sanar dashi komai,kuma shima ya nuna murnansa kuma yayi na”am da mganarka..”

Washe baki Saleem yayi kafin yace”Nagode Abbi Allah kara girma…”Abbi ya Murmusa yana Fadin”Ameen,ammh yanzu yace yana son ganinka,so in kasamu lokaci sai kaje ku gana ko? gyada kai yayi yana Fadin”To shikenan Abbi babu damuwa ko gobe ne sai naje ya ganni..”Abbi ya jinjina kai yana Fadin”To babu mtsala zan kirasa na sanar dashi zuwanka,kai kuma zan Turamaka nombarsa kaji ko..”Amsawa yayi da cewa,”Naji Abbi Allah ya biya bukata ngd sosai…”Daga haka sukayi sallama.

Saleem ya tashi da sauri ya daka tsalle yana Fadin”Game din ya kusa karewa fa…”Malika malik ganin nan zuwa gareki..”Yafada yana wani Cije baki bayan ya datse lebenshi na kasa,yana wani juyi kamar wani zakin daya dade bai ga abinci ba.


Shiko Abbi koda yadawo koda wasa bai sanar da kowa Abunda yake Faruwa ba,kama bakinshi yayi ya tsuke yana jiran Saleem yaje katsina ya dawo komai kenan daga baya kowa yaji,ko Hajiya data matsamai sanar da ita yayi sunyi waya da Alhaji Abdulmalik ya sanar dashi baya gari ammh da zarar ya dawo zai sanar dashi,toh dahaka ya kashe bakin Hajiya.

Itako Ummi bata kara marmarin karamai mganar ba,yasani ta sakamai ido ne taga iya gudun Ruwanshi,shiko yafi kowa karantarta tana da saukin kai,koman Turjiyanta kan Abu,da zarar ya tankwasata tana tankwasuwa,saboda yadda suke da Fahimtar juna,shiyasa bai damu da shariyanta ba,kuma mganar gaskiya duk wata uwa tagari bazata so Danta ya hada Zama ko Aure da Malika ba, domin kwata kwata bata cika sharudan zama mace tagari ba,Marwan ko Tun ranar litinin din yakoma,shi bai wani damu ba,don yana daukan mganar Saleem amatsayin Shirme ne kawai.

Shiko Alhaji Abdulmalik Ranar bai iya Runtswa ba saboda damuwa da Tunanin mafita,duk Farkawar da Hajiya binta zatayi sai ta ganshi zaune ya jingina da gado idonshi biyu ya Shiga zurfin Tunani,in ta tambayeshi yace mata bakomai takoma ta kwanta Kawai,Farkawanta uku tana ganinshi cikin wannan Halin,Na karshen ne tatashi tashiga tiolet ta wanko Fuska tazo ta zauna kusa da kafafunsa tana Fadin”Haba Alhaji,wai meke Damunka ne,Tun dazu  dana farka sai na ganka zaune ka zabga Tagumi,kuma na tambayeka kace bakomai,Bakomai ne zaka kasa barci Fisabillah…?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button