MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty


Bayan Sati biyu Zahra ta samu waya daga kano cewa An kwantar da momi Hajiya Saratu a asibiti,Dole suka Shirya tafiya harda Malika sukaje suka dubata,ammh su sai ka dawo Saleem yace Zahra ta zauna ta kwana biyu Tunda dama bata taba zuwa ba,ammh afuskar Zahra ya Fahimci bata ji dadin Cewar da yayi zai barta ba,haka ta bata rai har suka Tafi,ita kuma ba komai ne yamata bakinciki ba,sai yadda zata bar Malika da mijinta su kadai agida shine kishi ya Turniketa taji kanon ya Fita aranta,itako la’akari da Momi dake kwance ba lafiya batayi ba,A’a ita hankalinta na gida,Shiyasa Adaddafe tayi kwana hudu ta dawo sai dai suka ganta kwatsam,Saleem yayi mamaki Domin Sati daya yace tayi daya tambaayeta ba’asi sai tace Ai momin ce taji sauki Ita tacema ta taho gidan Mijinta,alhalin ko achan cema Momi tayi ita da Nadira Cewa Saleem ne yace kwana uku yabata ta dawo gida,Abba najin haka ya hadota da Direba ya maidota Zamfara.

Momyn ladingo..

  MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

MALLAKARJamila Umar A.K.A janafty*????

KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada

  30

“”Shigowar Su Malika ne ya dakatar da Saleem daga,d’aga hannun dayayi zai Naushi Bakin Zahra,wacce ta Sulale kasa tana kuka hannunta Rufe da bakinta tana makyarkyarta.

Malika ko Wajen Ayda ta nufa cikin Rawan jiki ta dauketa tana jijjigata batama kai ga Zarafin mgana ba,Taji muryan Saleem cikin wani yanayi yana Fadin”Why..? Zahra me nayi miki..? Me malika ta tsare miki..? Wani alhaKi Yar jaririya Ayda tayi miki da kikeson kasheta.?.”Atare joda da Malika suka kwalolo ido suna bin Zahra da kallo Wacce ke girgiza kai tana kuka take Fadin

  “Wlh batamin komai,Sharrin Shedan ne,ammh ni ko kuda Bazan iya kashewa ba..”Tafada tana gunjin kuka tana daga hannuwanta,Saleem bai iya mata mgana ba,sai da Numfashinsa ya koma daidai kafin yace”Hakane bakomai,Allah nagani ban Aureki da Wata Zuciya ba zahra,nayi kokarin ki zama mace tagari hakan ya gagara Daga karshema Saboda bakin kishinki kamaki nayi kina neman kashe yar Jaririyar Allah Wacce bata ji ba bata gani ba,ammh ngode ma Allah daya Toni asirinki Tunkafin ki aikata Abunda kika niyya,kije bazan hada ki da hukuma ba,ammh zan Sallameki daga Rayuwata sallama ta har Abada,Saboda haka kije na Sakeki saki biyu kuma Tsakani dake Zahra Allah ya isa,bazan taba yafe..Miki ba..”Yafada kamar kwalla zata zubomai Shiyasa ya Fice Daga dakin da Sauri yana Share hanci.

Itako Zahra zaman yan bori ta karayi akasa tana kuka hannunta biyu bisa kai tana kururuwa tare da kuka alokaci daya tana Fadin”Wayyo Allah na..!Kaicho na ni Zahra na kashe Aurena dakaina..”Take Fada tana kuka mai hade da Nadama mai karfi,Malika da joda dake tsaye agabanta suka daskare atsaye suna binta da kallon mamaki mai cike da tsoro.

Zahra ta rarrafa zara riko Kafar malika,ita kuma tayi Saurin yin baya tana girgiza kai Wasu hawayen Tsausayin kanta dana Yarta na kamata,kara rumgume Ayda tayi tana Fadin”Ban taba Zaton zafin kishinki akaina har yakai kiyi Tunanin kashe Jaririyar da batasan komai ba,haba Zahra me kika Dauki Duniya ne,duk Abunda Zaman lafiya da hakuri bai baki ba,Wlh tallah akasinsa bazai taba baki ba,Meya Rufe miki ido?Dukiya.?ko ko Shikanshi Mijin..? Wanda duka Zaki Mutu ki barsu anan Duniya kije lahira ki girbi Abunda kika Shuka..,Hakika kin bani mamaki Zahra,ammh kuma ngd ma Allah daya Tsaremin Ayda baki riga kin aiwatar da mugun Nufinki akanta,babu Abunda zence miki,tunda kin riga da knga karshenki..”Tafada tana kuka kafin ta sakai ta Fice daga dakin Zahra na kururuwan Kiran Sunanta.

Joda ta Shiga Tafa hannu tana fadin”Innalillahi ni joda na Shiga Aljannah,ammh dai kinyi Asara wlh,yanzu ke Zahra ina miki kallon mara hankali Ashe kallon biri nake miki kina min na ayaba,Toh Allah ya Shiryeka yasa wannan Ya zameki Darasi knga dai karshen Wanda yaja da ikon Allah don Malika da Saleem haduwar Allah ce bata ta mutum ba..”Tafada kafin tajamata dogon Tsaki ta Fice,

Nan Zahra ta kara Faduwa tana kuka harda birgima Nadama Tare da danasani suka Shigeta lokaci Daya tana Danasanin meyasa ta biyema Sharrin Zuciya Dana Shedan,gashi ya kaita ya baro,yanzu me zatacema iyayenta a auren da ko Shekara bai yi ba..? Bazata iya bude baki ta Furta irin Abubuwan Data aikata Saboda Tasan Halin Abba da momi suma bazasu mata da Wasa Ba.

Gajiya Tayi da kukan ganin babu mafita yasa ta tashi ta Shiga hada kayanta amanyan akwatunanta,Sai da ta hada komai nata kana ta koma ta Zauna tana Sharan kwallah,sai ga Saleem ya Shigo saurin mikewa tayi tana mutseke ido zatayi mgana kenan ya Mikamata Farar Takarda hannunta da jikinta na Rawa ta mika hannu ta karba tana kallon Fuskarshi wanda ya kauda kai alamun bayason ganinta ma kwata kwata,Ta karba ya sakai ya Fice ya barta tana zubewa bisa gado Tana Tsiyayan Hawaye.

Zahra da kanta ta Dinga jidan akwatunta zuwa waje,megadi ne ya Fita ya samo mata mai Napep ta Shiga Zuwa Tasha inda ta hau motar Kano,har suka kai kano Zahra na kukan Nadama da kaicho da Rayuwarta haka Napep din data Shiga da Inda mota ta Sauketa zuwa,gida nan ma kuka tayi tayi,kuma haka ta Fadama Falon gidansu tana wannan kukan megadin gidansu ne ya Shigo da akwatunta yana Sanar da Momi Mai napep na waje yana jiran kudinsa

Momi da ke Falon ita da Nadira suka mike Arazane atare suka Tarbi Zahra suna Tambayanta lafiya bata iya mgana ba illah Takardan da Saleem ya bata ta zaro ta daga cikin karamar jakarta ta mikama Nadira,momi kuma na kokarin ciro kudi cikin pos dinta Dake kan kujeran daya Daga cikin wadanda sukama Falon kwanya 500 ta mikama megadi ammh Rabin Hankalinta naga farar Takardan Da Nadira ke warwarewa tafara karantawa abayyane kamar haka.

  NI SALEEM KABIR KUMO Na kara karishe yanke igiya biyun daya Rage a tsakanina da ZAHRA BUKAR MADA Sakamakon munanan hallayata wanda in kuka Tambayeta zata Sanar daku da kanta,Ina Rokon Allah in azamana da Zahra na cutar da ita ko na Mintina daya na yarda ku iyayenta ko Rokarmata Allah ya Sakamata,in ko Azamana da ita Ita ta Cutar dani kuyatani Rokon Allah ya sakamin Akanta..

                * ACP S.K.Kumo.*.

Daga Nadira har Momin hannu Suka Dora bisa kai suna kiran Sunan Allah da Salati lokaci daya,itako Zahra kasa ta Sulale tana gunjin kuka Momi na kallonta cike da Tashin Allah..”Innalillahi Wa’inna alaihiraju’un Zahra garin ya haka ta Faru,yaushe Mijinki ya sakeki da zai ce ya karishe igiya biyun dake Tsakaninku,yaushe wannan Abun ya faru ammh mu bamu sani ba…? Tafada tana Rike haba cike da damuwa,Itako Zahra taki mgana banda kuka babu Abunda takeyi Haushi yakama Momi takai mata Duka tana Fadin”Don Ubanki bazaki mgana ba..? Mekika aikata har ya sakeki saki biyu lokaci daya,kuma a yadda yaron nan yayi Rubutu Zahra kece kika jama kanki Zawarci da yarintarki,Kinje kinyi Abunda kika kashe kanki kika kuma kashe mu iyayenka,Wlh baki kyautamana ba Zahra..”Take Fada tana kuka Nadira ce ta Rikota tana bata hakuri tana Share mata hawaye,itako zahra kukan ta take karama Volume Saboda bata da karfin gwiwa bada lbrin Abunda ya Faru

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button