MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty


Dalilin wannan Abun yasa Shakuwa tare da Tsantsan Damuwa da juna ta Shiga tsakanin Nadir da Zahra,shi duk a kokarinsa na ganin ta dawo Normal zahran ta kuma Alhamdulillah yabada Gudumuwaa domin ko Zahra bata dawo duka ba,tafara dawowa sai dai yanzu wannan Zahra ta gama Daukan Darasin Rayuwa sosai kuma ta kara gogewa da wayewa ba kamar da da bata wayau sosai ba,yanzu Saboda Cudanya da jama”a yasa idonta ya bude Sosai ta kuma gane Rayuwa.

Wannan Shakuwarsu nasu ita iyayensu ke kallo da makusantansu suke zaton suna soyayye ne,kuma ba Haka bane,Kawai kulawa ne da kuma Shakuwa,hatta Matarshi ta Fara Shaka da Zahra shiko ko ajikinsa bai maida kai ba,hatta Nadira tana ta addu”an Allah sa Ya Nadir ya auri Zahra da tafi kowa murna Har Ummah su ta kita ta tsegumta mata itama Tayi murna Sosai bata kuma jira komai ta kira Abban Zahra ta sanar dashi wanda yaji mganar abazata Duk da dai Shima yana ganin Shakuwarsu ammh ko da ya tambayi momi sai tace batajin akwai wani Abu atsakaninsu,Ammh jin Batun Umman lagos yasa yace zai Nemi Shi Nadir yaji..

Koda ya kira Nadir ya zaunar dashi yana Tambayanshi shi ya kira Umman lagos yace yana Son Zahra,mamaki ya kama ya Nadir yayi Shuru yana hasaahen Daga ina wannan mgnar ta Fito ganin yadda yayi ne sai Abba yace kada ya damu in ba haka mganar take ya sanar dashi,girman Abba a idonshi da kuma Kimarsa da Yadda yake arayuwarsa yasa yakasa masa musu ya amsa da eh shi ya kirata ya sanar da ita,jin haka yasa Momi da Abba sukaji dadi sosai har suka kasa boye murnansu Afili,Shiko Ya Nadir zahra ya kira ya Fara tambayanta itama taji mganar tayi mata bazata Tace itama bata sani ba,sai da ya kira Umman lagos yake tambayanta ta kyalkyacemai da Dariya tana gayamai yadda sukayi da Nadira tace taga ya tsaya kunya Shiyasa ita ta kira baban nashi ta sanar dashi kada wani yamai Shigar Sauri,ganin yadda gabadaya lamarin ya Daure Nadir shiyasa ya share bai nuna ma kowa bai ta ma Zahra kallon Wacce zai ya Aura ba yana kallonta ne da Sigar dayake kallon Nadira,ammh kuma Abba ya Wuce haka agurinsa bazai taba watsamai akasa a ido ba,Zai auri Zahra koda baya sonta ai kanwa take awajensa..

Tunda Abun na gida ne Umman lagos ne kadai tazo aka sanya Rana wata biyu masu Zuwa sai lokacin Ya Nadir ya sanar da matarshi,Taji wani iri sosai kuma bata iya boye kishinta ba,harta koken ko don bata taba Haihuwa ba yasa zai kara aure,lallashinta ya shiga yi da bata bKi har ta sauko ta karbi mganar hannu bibbiyu ta kuma yi mai Fatan alheri Duk da kishin Mijinta na cinta ammh ta danne Tunda dai mijinta bai Chanza mata Daga Son daya ke mata,Sai dai Wani dan Abunda ba”,a raasa ba Tunda Dan adama ajizi ne Tara yake bai cika goma ba.

Zahra ma haka taji Abun kawai Daga sama,Ammh kuma akasan Ranta tayi murna Domin Shima ya Nadir Namiji ne,Kodai baikai Saleem ba to zata jerasu a Aji da Takama da isa,lokacin daya Fara zuwa wajenta da Sigar Mijin da zata aura yayi mata mganganu sosai ya kuma sanar da ita sai tayi Hakuri don yana mata kuma ta sani,so suyi Hakuri da juna duka sai su zauna lafiya,Zahra bata daukan ma kanta Tun Farko ba,tuni ta watsar da wani kishin Banza ta rike Sabon Mijinta kuma yayanta dakyau gefe daya kuma suna ta Shiryen Shiryen bikinsu,da farko ita fara wasan buya da Madam,sai da bita har wajen aikinta bayan ta dawo daga asibiti tana mata tsiyan haka zasu kwashe In ta Shigo ai an zama daya,Zahra tayi murna sosai nan da nan suka koma kamar da,wani lokacin in Zahra tatashi Daga wajen aiki ta kan biya,Nadira kuma ta fikowa murna kamar me,tana ta addu”a Allah yasa kada ta Haihu sai bayan biki cos tana son ta baza kara”i ne part 2 awannan karon.

Biki ya karato Duk da ba gayyah Zahra tayi sai yan wajen aikinsu kawai sai wasu daga cikin kawayensu da sukayi mkranta Zahra ce ta matsamata ta kira Saleema ta Sanar da ita zatayi aure,bata yi musu ta karbi lambarta ta kirata sai da ta sanar da ita Sunanta kana ta ganeta Saleema tayi mamaki sosai kuma tayi murna da jin Zahra zatayi aure,nan take Sanar da ita Tayi Nauyi ammh zata Roke Ya Sadiq in ya yarda zata zo Katsina ta kwana sai su taho tare da Malika,jin haka yasa Zahra tace ta Rubuto mata Full address din gidan Saleem da lambar wayar Malika nan ko take Saleema ta tura musu suka rabu cike da Farinciki kowa na Mamakin yadda dan”uwansa ya chanza wai Saleema keda ciki wai Chanchadi????

Nadira tabama Zahra Shawaran taje Har katsina ta kaima Malika Katin biki da cimgam,da kuma nemam ya Fiyan juna Tunda yanzu komai ya Wuce,Zahra ta yarda da mganar Nadira hakama momi ta amince mata taje,domin itama tace zata kira Ummi ta sanar da ita Ranar bikin,Nadira ta so ta raka Zahra ammh sai Dr ya hana Don cikinta ya tsufa,Shiyasa Ana saura kwana goma biki Zahra ta Tafi katsina da kanta ta tuka kanta cikin Sabuwar motarta ammh sai da ta tambayi ya Nadir ya kuma bata dama.

Insha Allahu MALIKA MALIK Zai kare a page 40 ne,Duk da ba haka na so buh Lbrin ne yazo ahaka,Darasin ya Fita,kun ilimantu kun Nishadantu da abubuwan dake ciki bayan Tarin Fadakan da kukayi,ina Fatan zakuyi amfani da Abunda kuka ci karo dashi mai kyau zaku watsar dana Banza…Babu amfanin tsawaita lbri tare da Jan rai matukar an cimma Abunda Ake Nema,Allah kabamu ladan Taruwa dani da ku wajen Wannan Rubutun…

SHAKIRA
JANAFTY
ANITHA
MOMYN LADINGO

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

Mallakar:Janafty????

KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

              KAR’SHE…????????????

  …..”Full Address Din da Saleema ta Turo mata tabi da kuma tambaya sai gata abakin makeken get din gidansu Malika tana zuba hon da hanzari megadi yazo ya wangale mata get yana mata barka da Zuwa,yana zaton kawar Hajiya Malika ce.

Aparking space ta adana motarta kafin ta Fito tana Sanye da abaya doguwar riga baka ta kamfanin Armani Wacce ta yane kanta da karamin bakin gyalenshi, Kafarta Sanye da Cover baki,mai wani Fulawan baki Ajikinsa,sai karamar bakar jakarta dake hannunta Hade da key din motarta cikin Sha”awa take bin gidan da kallo kafin tafara taku Zuwa Wata kofar glass din da zai sadata da cikin Babban Falon gidan.

Tana sa kanta Falon Cikin Sallama Da karamar muryanta kamar ba Zahra ba, babu kowa a makeken Falon,sai karar Talabijin din da ta kusa cinye bangon Wajen Saboda Girma,tana kokarin sake Maimaita Sallaman nata ne Sai ga Merry ta Fito dauke da Aryan ahannunta yayinda Dose ke Tura Ayyan a wani karamin keke da alamun na koyon Zama ne…

Da kallo Zahra ta Bisu dashi tana Mamakin Yaushe Malika ta Sake Haihuwa Domin ko ba”a Fada wannan ya”yan Malika ne da Saleem Saboda yadda suka kwaso kamanin Babansu da kuma Hasken Fatan Mamansu,Merry ce Tafara gane Zahra cikin Mamaki da doki ta Furta..”Anty….”Tafada cike da mamaki da Murna lokaci daya.

Mirmishi mai Sauti Zahra ta Saki kafin tace”Yes Merry..”Tafada tana mika hannu ta karbi Aryan daga hannunta tana Fadin”Ina Malika..? Ko bata nan ne..? Dose ta gaisheta ta amsa cikin sakin Fuska tana ma Ayyan wasa hannunta na dauke da Aryan,Da hanzari merry ta Haura sama ta kwankwasa dakin Malika,wacce Fitowarta wanka kenan tagama Shiryawa kenan cikin wata Atamfanta Riga da Sikat,tana Daura Dankwali tazo ta bude kofar ganin Merry yasa tace”Merry anthing..? Merry na Washe baki Tace”Anty Zahra ce tazo tana Falon kasa tana jiranki..”Cike da Mamaki Malika ta Furta”Wata Anty Zahra..”,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button