MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Girgiza mata kai tayi tana dukar dakai,Gefe Ummi ta ijiye mata katon Farantin bisa cafet din dakin tana Fadin”,Toh maza kiyi kizo kici abinci kada ki zauna da yunwa kinji ko.? Gyada kai tayi kafin tace”Tanque Ummi..”Mirmishi Ummi ta mata kafin tace”don’t kinji..Is my Duty…”Daga haka ta Fice daga dakin.

Ajiyar zuciya ta sauke aranta tana Fadin”Zuciyar iyayansa mai kyau,ammh shi ko ina ya gado bakin hali oho..”Bata gama mamaki ba ya sawo kai dakin waya makale akunnenshi yana waya,bai kalli inda take ba,illah Fadawa dayayi bisa makeken gadonsa yayi Ringigine,yana cigaba da amsa wayarsa,da ga duk alamun yadda yake mganar zaka san wanda yake wayarshi dashi bayi da wani muhimmanci saboda yadda yake bada amsa ayangance daga baya ma tana ji ya yanke kiran yana sakin wani Siririn tsaki.

Tsayawa tayi kyam tana kallonshi daga saman Fuskarshi zuwa kirjinsa,yadda ya Lumshe idanuwansa kamar mai barci bayan ya goya duka hannuwansa bisa kirjinsa,ta Zurfafa da kallonshi tana yaba kyau da tsarin Fuskarsa bata ankara ba taga ya bude idanuwansa ahankali yana kallonta,Daburcewa tayi tana Zare ido kamar wacce tayi karya Bai mata mgana ba,illah juyamata baya dayayi yana Sauko da kafarsa daya bisa cafet din dake dakin,ganin haka yasa ta jingina da wardrope din dakin tana sauke wasu tawagen Numfashi,Ta hanzari ta dauki hijabin data cire,ta saka bata san gabas kawai ta tari yammah ta tada sallar tana ta buga Shirmen data saba.

  Kamar ance ya waiwayo,sai yayi mugun gani,Ware ido yayi yana kallonta tana sallah,na farko ba gabas take kallo ba,na biyu wlh bakinta baya motsi baijin tana karantana wani Abu,daga sujjadan har ruku”un yi kawai take kamar wacce take dukawa tana duba wani abu,bai gama mamaki ba yaga ta zauna tahiya tayi Shuru kawai ta kurama waje daya sai chan kuma ta sallame,kara mikewa tayi zata kabbarta wata sallan da hanzari ya diro daga kan gadon sai gashi gabanta da kakkausan murya yace”Ke tsaya da sallar nan naki don Allah…”

Yafada yana tsareta da ido,ba alamar wasa,jagale tayi atsaye tana raba ido,Habansa yakama da hannu yana Fadin”Ke yanzu sallar me kikayi..? Kanta na kasa tace”Na Azahar.. Jinjina kai yayi kafin yace”Ammh dai baki karanta Fatiha da sura ko? don naga ko minti daya bakiyi kike dukawa..? Dagowa tayi tana kallonshi ganin yadda ya tsareta da ido ne yasa ta sadda kai cikin sanyin murya tace”Fatiha kadai nake karantawa..”

Dan ware ido yayi kafin yace”Why..?ko bakisan raka,”a biyun Farko Fatiha da sura bace,sai a raka’a biyun karshe ne zaki karanta Fatiha kadai..”Jim tayi kafin tace”Menene Sura,Ai ni d only Fatihan na iya..”Baisan sadda ya sauke ahannunsa ahaba ba yana binta da kallon mamakin kin Wuce Tunanina,jin shuru yasa ta dago tana kallonshi ganin yadda yake kallonta kamar na rashin hayayyaci yasa taji jikinta yayi sanyi sosai,nan da nan idanuwanta suka cika da kwallah.

Bai samu zarafin mata mgana ba, saboda mamakin dayakeyi kai tsaye yasake jefomata tambaya”Guda nawa ne Farillan alwala,kuma nawa ne Sunnoninsa..? Bata dago ba,taji hawaye sun taho mata bata taba nadamar rashin ilimin addinin ba irin na yau,in da ta iya data ba Saleem amsa koda ta muzantashi kamar yadda yayi mata,sai dai kash bata san komai ba.

Ganin tayi Shuru yasa ya bude baki yace”,Shima baki sani ba ko..?Kai ta gyada mai ahankali tana kokarin maida kwallar data kusa zubomata,baki ya rike yana binta da kallon Ina da aiki,kai tsaye ya sake cemata”Ke wai tsayama,Kina wanka inda Janaba ta sameki,ko kuwa kina tsarkake kanki inda kin gama jinin al”ada..? Yafada yana kara saka mata ido kur yana kallonta.

Tsuru Tsuru tayi da ido tana kallonshi kafin ta sadda kai kasa tana wasa da gefen hijabinta,Miyan bakinshi ne yaji ya kafe,saboda yadda yaga yanayinta bama sani tayi ba,mikewa tsaye yayi yana goya hannunshi abaya yace”Tambayarki nake ki sanar dani in baki sani ba,kada ki cucu kanki..? Kanta na kasa tace asanyaye”Eh ni bana kowani wanka,sai wankan da kowa yakeyi kamar wanda kayi yanzu ko bashi ba..? Ware ido yayi kafin yace”Na bani ni jikan Hafsat…Kina nufin kice ko Jini kika gama baki wankan tsarki? balle ma na saran ranar dana kusance ki bayan kin dawo hayyacinki kin Tuna  dayin wankan Janaban? Yafada idanuwansa sun Chanza launi.

Kasa kawai tayi da kafafunta tana dukawa kanta na kasa ta Furta..”Wlh bansa komai ba,ban iya bane danayi,…”Tafada hawaye na zubar mata kamar an bude Famfo,kugu yakama yana kallonta,kawai sai wani shashe na zuciyarsa yatsausayamata matuka na yadda tana yar musulma ammh bata da sani kan Addininta.

Ajiyar zuciya ya sauke yana Fadin”Is ok..Kina so na koya miki Karatun Addini..? da hanzari ta gyada kai tana Fadin”Eh plz…”,Bai mata mgana ba illah Mikamata hannu dayayi yana kallonta,itama kallonsa take kafin jiknta asanyaye ta saka hannunta bisa nashi ya mikar da ita,yana jaye da ita har cikin tiolet din bai Direta ko”ina ba sai bakin Sink yana Fadin”Sake alwalan ki nagani..?

Batayi gaddama ba ta duka ta sakeyi yadda ta iya,Girgiza kai kawai yake domin ita kanta alwalan bata iyata ba,haukanta kawai take,Baya yayi da ita kafin ya fara nadadde hannun Rigansa yana Fadin”Juz wacth me verg well kinji..”Gyada kai tayi tana kallonshi yana alwala,sai da yamayamata sau uku kana ta sake yi sau Daya,normal kamar yadda yayi mirmishi yayi mata yana Fadin”Tafiyanmu zata daidaita matukar kina da saurin Fahimta.

Haka suka koma Dakin,da zuciya daya yake koyamata sallah yana mata bayanin komai daki daki,bai samu damar koyamata wani abu ba,sai da yasata ta rama duka salollinta,Isha”i ne kadai yaja musu jam”i bayan sun idar ne ya kalleta yana Fadin”First abunda zamu fara,shine gyara sallanki,yanzu gobe zan saka asiyo miki Karamin Qur”ani izifi biyu,Da Sauran kananun littafin da zasu taimaka miki,yadda zaki fara gane komai daki daki,ammh yanzu kici abinci kizo na fara koyar dake Abun ake Fada yayin Sujjuda,da kuma yayin Ruku”u zaman tahiyan farko da zaman tahiyan sallama..”Gyada kai cike da gamsuwa sai ta samu kanta da furtamai”Tanque…”,

Bai kalleta ba yace”No godema Allah..”Kallonsa tayi araunane batace komai ba,tashi tayi ta isa ga farantin da Ummi ta kawo mata,Kolan Farko ta bude ta iske White rice,sai kula ta biyu kuma Miya ne wacce taji kazi,kadan ta diba ta Rufe sauran,taji dadin abinci sai da cinye wanda ta diba duka harda kari,tasha Ruwa,yau anci sa”a batayi ammh ba,nan ta bar komai awajen,ammh takasa tashi,tana Tunanin kamar bai kamata tabar komai awajen ba,sai ta tuna tana gida Hajiya ke daukemata ko Su Dose da merry,.

Satan kallonshi tayi sai taga baya tatata,domin hankalinsa na kan wayarshi yana Faman latse latse,sai lokacin Ta tuna da nata wayar,batama kunnata ba sai gobe,ganin yadda tayi Tsuru awaje dayane yasa yace”Kinga malama in zaki so na koyar dake kizo,in muka kina ganin zai zama takura zan kwanta ne..”,Jin haka yasa ta mike da hanzari ta isa gabanashi tana Fadin’,Gani ina so plz..”

Tashi yayi daga kishingiden dayake akasa yana tankwashe kafa,tun kafin yayi mata mgana ta tankwashe kafafunta itama,kallonta yayi yana nazarinta kafin yace”Kina bukatar Abun Rubutu,ko hakan daliban ilimi ke zuwa..”Wiki wiki tayi kafin ma tayi mgana ya tashi ya dauko mata wani karamin joter da Pen,shikuma ya bude Dirowan gadonshi ya dauko karamin Qur’aninsa izihu Sittin ya bude yana Fadin”Fara karantamin Fatiha tukunnah naji..”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button