MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Malika dataji wani abu ya daki kirjinta ya gangaro har zuwa cikinta da maranta bata iya maidama Zahra da amsa ba ta dafe cikinta tana Cije baki cike da azaba lokaci daya hawaye na wanke mata Fuska,wata Shewa zahra ta saka kafin tace”Ji munafukar mata daga mgana sai ki dafe ciki kina kuka,Toh ni kam ban tabaki ba balle ace zan kashe rai..”Tafada kafin tayi tsaki tayi Wucewarta daki,

Malika taji hawaye suna zubomata basa yankewa ga maranta daya kulle cikinta na juyawa tama kasa daga kafa,tana kuka ta cije baki tana salatin cikin wannan Halin Joda ta Fito ta isketa cikin Tashin hankali ta isa gareta tana rikota take Fadin”innalillahi Anty malika,meya sameki,haihuwar ce..?

Bata iya mata mgana ba,saboda wani azaba daya Turnikota dafa joda tayi tana Sauke numfashi lokaci daya da kuka dakyar ta iya Furta”Ki ki..Kira maman Abba joda inaga haihuwar ce tazo..”Tafada tana cije baki,da sauri joda tatashi ta Shiga daki ta dauko wayan Malika ta kira Maman Abba ta sanar da ita,ita kuma tace tana asibitin yanzu haka,ammh gatan zuwa,kafin ta iso joda ta hada komai na haihuwan datazo sai su Koma asibitin tare dasu,aiko da hanzari joda ta Bude karamin akwatin Malika ta rinka jidan kayan haihuwanta tana sakawa aciki,kafin ta kulle ta zari hijabinta da hanzari ta kinkimo akwatin zuwa falo,koda ta Fito Malika ba yarda take,domin sai mukurkusi take tana kuka,Rikota Joda tayi tana mata sannu kafin tace”Na kira Maman Abba tace gatan zuwa mu je asibiti ko na kira Ya Saleem ne na sanar dashi..”Duk tana halin ciwo sai da ta girgiza mata kai alamun karta kirashi,rike joda tayi kawai tana nishi sama sama ga zufar datake ta Ketomata Malika girgiza kai kawai takeyi tana Tunanin kila ita kan tata ta kare,Sannu kawai Joda ke jerama,ammh ina batama jinta banda Sharban hawaye da Cije cijen baki babu Abunda takeyi,..

Acikin wannan Halin zahra ta sake Fitowa ta tarar dasu,kallon banza ta bisu dashi ganin Malika na wash wash tana zufa yasa ta rike baki tana yar Dariya tace”Topha Abun yazo ne…”Tafada cike da izgilanci,daga Malikar har Joda ba wanda ya kulata kichen ta Shiga ta dauko Tazo tazauna Afalo tana Sha hankalinta,kwance saima Rimot din Tibi data dauka ta chanza tasha,zuwa wata wacce ake wakokin Turanci harda kure Volume tana bi tana karkada kafa.

Maman Abba ce ta Shigo ahankalinta tashe ganin halin da Malika ke ciki ne yasa ta rude ta kamota tana Fadin”Kamota joda,haihuwace..”Riketa sukayi har zuwa motar Maman Abba suka sata abaya,kafin Joda ta koma ta dauko akwatin kayan haihuwan da wayarta data Malika,Zahra na zaune bisa kujera tana jijjiga kafa suka Fice daga gidan zuwa Asibiti


Saleem bai da masaniyar Abunda yafaru sakamakon yayi busy ko wayar dayake ma malika ma yau din kwata kwata bai samu yimata ba,har ya dawo gida wajen after 8,dayake zahra keda girki bayan yayi wanka ya sauya kaya zuwa jallabiya,sai ya Fito Falo ta Fitomai da abinci ta durkusa tana cikin Serving dinshi kenan ya kalli barayin dakin Malika yana wani nazari kafin ya kalli Zahra yana Fadin”Ina Malika,tana lafiya dai ko? don Tunda na dawo banji Duriyarta ba daga ita har Joda..”

Tabe baki Zahra tayi Daidai tana ijiyemai Filet din Tuwon shinkafan agabanshi tace”Bansani ba,nida naga wannan Nurse din ta shigo sun Fita da ita da Sauri,kamar dai kila haihuwan ce tazo…”Wani uban Zaro ido Saleem yayi yana Fadin”What..”!Haihuwa fa kikace zahra..? Kallonsa tayi cike da mamaki tana Fadin”Eh nake ganin kila haihuwan ne,nifa bansani ba don ba wacce tamin mgana da zasu Fita..”

Bai tsaya sauraranta ba,yasaka kafa yayi Fatali da kololin dake gabanshi ya mike yana Fadin”Ammuh ban taba ganin dabba Yarinya irinki ba yanzu ace Malika tafara nakuda har wata makociya tazo ta dauketa zuwa asibiti ki kasa kirana ki sanar dani,ammh don jakanki da rainin hankali har na dawo gida nayi wanka baki sanar dani ba,sai da ma na tambayeki,kuma kina sanar dani mganar banza..”Yafada yana Huci,mikewa tayi tana kallonshi,yadda yake kallonta kamar ya Rufeta da duka,bai tsaya sauraranta ba ya tureta tatafi ta Fadi bisa kujera yawuce dakinsa da gudu ya dauko wayarsa da makullin mota ya Fice da gudu yana cigaba da latsa wayar tasa.

Godiya da Fatan Alheri gareku yan Gidan Amana na MALIKA MALIK PAID GROUP..,Hakika kirkinku gareni sai dai nace Alhamdulilah,Allah nake roko ya dafa muku kamar yadda nima kuka Dafamin,Allah ya saka muku da alheri ina godiya Sosai da duka tarin alherinku gareni…Allah yabiyaku da aljannah Firdausi Ameen????????

Mommyn ladingo..

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

26

""Wayar Malika yake ta kira,ammh kuma gashi tana Ringing ammh kuma ba"a picking hankalinshi in yayi Dubu ya tashi,haka ya shiga cikin mota yayi zaune yana dafe kai,wayarsa ne ta dau Tsuwa yana dubawa yaga Wata Nombace agaggauce ya daga kiran yana Fadin"Hello..."

Joda dagachan bangaren tace”Hello ya Saleem Joda ce..”Jikinsa na rawa ya Fito daga motan yana Fadin”Joda,kuna ina ne,ina ita malikan? ta haihu ne? ko bata haihuwa ba..? Haka ya Shiga jeramata tambayoyi alokaci daya,cikin damuwa da alhini tace”Muna asibitin da Maman Abba ke aiki,kuma haryanzu Anty malikan bata haihuwa ba,sau biyu ana Saka mata Ruwan Nakuda,ammah haihuwar shuru,wlh Ya Saleem Anty malika tana Shan Wuya,yanzu hakama ana cukun cukun Turamu General hospital gusau ne..”

Dafe kai Saleem yayi yana Fadin”Innalillahi wa’inna Alaihirraju’un,ganin nan zuwa yanzu…”Yafada yana katse kiran ko cikin gida bai koma ba ya Fada mota ya tasheta asukwane,da Sauri ya dinga latsama Megadi hon,wanda ya Rugo da gudu ya Budemai get ya sulala zuwa waje da Gudu.


Zahra ko tana zaune kan kujeran Da Saleem ya tureta bata iya tashi ba saboda takaichi da bakinciki,tana jin sanda yayi hon da kuma Ficewarsa lokaci daya,tsaki taja afali kafin tatashi tana tattara kololin daya watsar tana Fadin”Allah sa daga haihuwar ta mutu,basai naga karyan Tsiya ba..

ko Ajikinta bata damu ba,saima gyara zama datayi afalo tana chanje chanjen tasha ko ajikinta,saboda gulma ita ta kira Saleem tana Sanar da ita Abunda ya Faru,da kuma halin da’ake ciki,shewa Saleema tayi kafin tace”Kin min Daidai ta wajena,haka nakeson ki rika yin komai cikin taku,ni Allah yasa ma wajen haihuwar daga ita har Abunda ke cikin nata su Haura chan,sai mu fatan Allah ya kiyaye hanya mu sai munzo..”Dariya suka Sheke dashi atare kafin Zahra tace”Kamar kin Shiga Raina haka nace,….”nan suka cigaba da hiransu suna zagin malika da fatan kada Allah yasa ta haihu lafiya,su Fatan mutuwa suke mata,saboda yadda sukaji jininta arayuwarsu ta Duniya.


Koda Saleem ya isa asibitin har anbasu takardan izinin tafiya da malika Zuwa general hospital gusai so bai tsaya ba,suka sanyata amota Shida Joda da Maman Abba,wacce ta bar motarta anan asibitin BAyan ta kira Baban Abba ta sanar dashi Abunda ke Faruwa,yakuma amince taje har chan general hospital gusau din.

Saleem yayi gudu bisa hanya,sakamakon ganin irin kuka da salatin da Malika keyi tana Fadin ita mutuwa zatayi,duk inda hankalinshi yake toh alokacin atashe yake,gudu kawai yake tsulawa cikin lokaci sai gasu acikin haraban general din,maman Abba ita tafita ta gudu ta sanar Da Nurses su kuma suka zo da Gadon daukan marasa lafiya,ko kafin su kariso sai suka Hadu da Saleem ya daukota ahannunshi nan suka nuna mai dakin da zai Shiga da ita,nan ya Shiga da ita ya kwantar da ita kan wani karamin gado yana kallon Fuskarta yarda halittarta ta chanza Saboda wahala.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button