MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Anyi suna lafiya angama lafiya Washegari yan KUMO da yan Malumfashi suka koma,suma cike da kayan arziki,Suka tafi suna Malika da Saleem fatan alheri da Fatan Allah Shi raya Ayyan,da Ayran.

Momyn Ladingo..

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

Mallakar:Janafty????

KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada

38

……………”Su Maman Abba da Saleema su kadai aka bari suka cigaba da soye soye basu Tafi ba sai da komai ya kammallah,Suka taimaka aka gyara gidan kana,maman Abba ta Wuce zamfara ita kuma Saleema tatafi Abuja ta kwana Washegari zata bi jirgi Zuwa Abia.

Ita kuma Hajiya, Ummi ta roketa Kan ta Zauna ta dan kara ko Sati daya ne kafin goggo Hadiza tazo wacce tatafi minna An mata rasuwa,sai ta dawo kana zata zo ta zauna Da Malika uwar mazaje.

Hajiya ta Zauna da Malika har Na tsawon Sati biyu tana kara kula da ita da Kuma su Ayyan Duk da gasu Merry suna kokarin Taimakamata,sai Ranar ta cika kwana ashirin da Hudu kana goggo Hadiza tazo,sai Hajiya Ta koma gida ta barta tana Kula da Malika wacce ta warke kamar ba ita ba.


Tun Malika na kwana 36 Da haihuwa jini ya Dauke mata tayi wanka Tafara Sallah Ammh Bata bari Uban gayyah ya sani ba,domin taga take takenshi so yake ya barta da Abun kunya agaban Goggo Hadiza,Don Tun Satin daya wuce yake damunta da ya kosa ta Fara sallah wlh a daddafe yake yayi kokari ta taimakeshi,Bata nuna mai komai ba,Sai Ta nuna mai Data Fara zata mai mgana,sai dai wani lokacin ta Saci jiki taje dakinsa ta Dan mai Dubaran,su na mata ammh Duk da haka bai wani gamsuwa shi burinshi yajishi Cikin babban Fada????.

  Ga wannan karon su Ayyan da Bala”in kuka suke da Tsotse,bata da lokacin kanta,data samu sararin zuwa dakinsa ko Dadewa baza tayi zata ji kukansu da kuma kiran goggo Hadiza,Da kuma ta Fahimci Dakinsa  Taje Sai goggo Hadiza ta kama mata Fadan zatayi kazantattacen jego matukar ta biye ma Namiji kaita zai yi ya Rabo wlh,wato yaga jiki yayi Taushi ,shine ita zata biyemai Shiyasa wani lokacin ko ya kirata bata Zuwa,sai tace mai su Aryan na Rigima.

    Yau da Wuri ya dawo yana Shigowa Direct dakin Malikan ya Shiga,yana Shiga ya ganta tana sallar mangariba,,galala ya tsaya yana kallonta,yana mamakinta domin Jiyan nan ya Tambayeta yaushe zata Fara Sallah ,tace bata sani ba,akofar dakin ya coge yana binta da kallo itako ta jikin madubi ta hangeshi sai da gabanta ya Fadi,Sai ta Daburce ta idar da sallar ammh sai ta sake kabartawa Yana kallonta bai mata mgana ba, illah takowa dayayi ya zauna agefen gado batare da yayi mata mgana ba.

Tun tana mai karyar Sallah harta hakura ta Sallame tana Raba ido,bata yarda sun Hada ido ba,tayi zaune tayi Zuru gabanta na bugawa,Ta gefen gado ya kalleta kafin ya saki Siririn mirmishi kafin yace”Kin idar da sallar..? Na zata sai gobe zaki idar..?

Shuru Malika tayi tana wasa da Gefen Hijabinta,ganin batayi mgana bane yasa ya mike yana Fadin”Ina ayda ko tana wajen goggo ita Da su Aryan..? Da kai Malika ta bashi amsa,Dariya ta kamashi yayi yana Fadin”Kin zama kurma ne..? Ko Azumin mgana kikeyi..? Bata dago ba balle ta bashi amsa,kofar ya isa ya sama key kafin yazo ya Tube karamin Towel ya daura iya kugunsa ya Fada Wanka tana binshi da kallon mamaki,tana zaune awajen har ya Fito yana kallonta Shima ita yake kallo kai Tsaye yace mata”Kinsan Hukuncin macen data kema mijinta karya..? Ya fada yana goge Sumar kanshi da wani karamin Towel,Kanta na kasa tace”Karya kuma…? Dan mirmishi yayi kafin yace”Eh kin min karya kince baki Fara sallah ba,saboda kada Nameni hakkina ki bani ko Malika..? ya Fada cikin wani yanayi,Mikewa tayi jikinta yayi sanyi kafin tace”Wlh ba…”Shiii…Is ok,ai bazan Nema ba Tunda na Fahimci Guduna kike,bakomai Zan zauna ahaka ammh ki sani in na kasa control din kaina har na Fada wani Hali kome ya Faru kece Sila..”Yafada cikin son Tabbatarwa,kafin ya isa gaban Merro ya jawo lotion ya Fara shafawa.

Jikin Malika yayi Sanyi da azama tataka zuwa gareshi kawai sai ji yayi ta Fadaomai jiki ta kamkameshi ta haya,Hannu yasa yana so ya bambareta daga Rumgumar da tayi mai,ammh ta ki sakinshi suka Fara kokawa,ranshi bace yake Fadin”plz Ki sakeni kafin Raina ya baci,badai jikinki ki keman Rowa ba,ki jika kisha,ni bazan yi zina ba,ammh kisani zan karo wacce ko acikin wani hali na nemeta zata bani kanta..”

Jin haka yasa ta fashe da kuka tana kara Rikeshi Kamkameshi tayi ta Zuro da hannunta ta cikinshi tana mai Shesshekan kuka cike da Shagwaba,Shuru yayi mata yana bin Fuskokinsu ta jikin madubi da kallo,Kara Hade rai yayi yana Fadin”Wai ina wasa dake ne Malika,i said leave my body ko..?Narkemai takarayi kafin tace”Wlh bazan tashi ba,ni da jikina,kuma Shikenan daga kuskure kadan sai ka yankemin Hukunci baka iya tsayawa kaji Uzurina..”karamin Tsaki yaja kafin ya waigo da karfi ya kuma sa hannu ya Ture malika baya sai ta Fada gefen gado yaraf,Arazane ta dago kanta tana kallonshi kafin ta samu Zarafin mgana yace”Bana son Jin komai daga bakin plz leave me olone,indai kan ki bani hakki na ne,Malika kiyi ta Rike kayanki bazan kara ce miki komai ba Do wht ever u want i dont care..”Yafada kafin ya isa jikin Wardrope ya dauko Wasu Riga da wando na kamfanin Armani,ya saka yayi cumbing din kansa ya Fice bai kara kallon Inda Malika take ba,ta kallon ta bishi kafin ta kwanta bisa gadon Tana Fashewa da kukan takaichi da cin rai,Shiko Ficewa Yayi daga gidan gabadaya,har wajen 10 da Malika taje dakin Goggo Hadiza ta basu Aryan Nono Saleem bai Shigo sai hankalinta ya tashi Zuciyarta ta Fara mata wasu Tunanen ko dai wajen Wata yar iskan karuwan yaje..? Tuni Taji Hankalinta ya tashi,ammh sai tayi saurin Kauda wannan Tunanin Saboda tasan Halin mijinta baya shaye Shaye baya Neman mata,ammh ganin har pass 12 Saleem bai Shigo gida ba,yasa kuma hankalinta yakara tashi tayi Safa da marwan Tsakanin upstair da kuma kasa,haka tazauna afalo tayi Zuru ta Tsurama kofar falo ido,lokacin da 12:30 tabuga ne Goggo Hadiza ta sauko daga sama tana bin Malika da kallon mamaki,itako hankalinta yayi gaba bata ma san goggon ta sauko sai da taji tana Fadin”Malika…”Cike da mamaki…

Afirgice Malika ta Waigo ganin Goggo Hadiza yasa ta sauke ajiyar Zuciya tana Sosa kanta tace”Bakomai Goggo Zan kalli wani Shiri ne a Mbc yanzu…”Kallon mamaki goggo Hadiza ta Bita dashi tana karantarta kafin tace”Kuma shine kallon atsakar dare malika ..?Kina da danyen jiki,maza ki Wuce daki ki kwanta,dama na Shiga dakinki na kai miki su Aryan ne,sun yi barci kada Su tashi cikin dare suna kuka kinsansu da tsotso..”Kai ta sunkuyar Kafin ta Wuce tana Fadin”Toh Goggo sai da Safe..”Tafada jikinta asanyaye kafin ta haura sama da kallon Tsausayi goggo Hadiza ta bita kafin ta jinjina kai tabi bayanta,ammh tasan Dalilin wannan damuwar ta Malika,ita batajin Shigowar megidan ba Allah yasa lafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button