MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty


BAYAN SHEKARU GOMA DA SUKA GABATA

…..”Ashekarun goman da Suka Wuce Rayuwa ta gangara yadda Allah (SWA) ya tsara Abubuwa dadama na Farincikin da akasinsa Sun Fara acikin Rayuwar Saleem da Malika,Na akasin Farincikin Shine Shekaru biyar da suka Wuce Sukayi Rashin Hajiya Babba Wacce Ta Rigamu gidan gaskiya Sai Fatan Allah ya jikanta da Rahma,mutuwar Data girgiza Iyalan Kumo gabadaya Saboda yadda Hajiya Babba take awajensu,ammh kuma basu yarda zasuyi Mutuwa tana kan Kowa muma ita muke jira.

Ababen Farincikin da suka Faru kuwa,Shine Shekaran daya Gabata  IG KABIR KUMO yayi Ritaya daga aikin yan Sanda,wannan Dalilin hakane bayan an samu chanjin gwannati aka Tsaga sunan SALEEM KABIR KUMO amtsayin IG Na kasa gabadaya,wanda Dama kafin lokacin yayi ya samu karin Girma yana mtsayin AIG ne.

Rayuwa tayi kyau Fiye da Zaton mai karatu inda Zuru”a suka cika gidan Kabir kumo wanda Suke nan Zaune har yanzu agarin Abuja,Suko su Malika Sun baro katsina Suna Zaune a wani makeken gidan Da Saleem ya Siya Mai kama da aljannar Duniya,bayan Ayda da Ayyan Takara Haihuwan Mata biyu Maza biyu,Ya”yanta Bakwai kenan,inda take da Saleema da Marwan,sai Abubakar Da Maryama,Ayayinda itama Saleema take da ya”aya biyar Cif Duka mata,Hamdiya,Hamida,Hafsart,Hadiya,Aneesa,Ya marwan ma Tuni ya”ya Sun lullubeshi shi da Joda ,ammh sukan suna Tsara haihuwan ne,Ya’yansu Uku Saleem,sai Saleema,sai Fatima wacce suke kira Ummi kenan.Ayanzu haka Sunbar lagos sun Dawo partacourt da zama Sakamakon Chanjin wajen aiki da ya marwan ya samu hakama Sadiq suma yanzu su suka koma lagos da zama sakamakon Shima ya samu karin girma Zuwa DCG,Sun tattara sun koma chan,sai dai duk bayan Wata uku suna kokarin Zuwa Abuja Hutu domin Ganin iyayen nasu da kuma Sauran yan”uwa.

Abbi Da Ummi sun Fara manyanta Duk da Kudi da Hutu Suna Boye manyantansu nasu,ammh sun Kara manyata Sosai Saboda Shekaru yaja,ita kanta Ummi tayi Ritaya daga aikin lauyan datake yi saboda Shekaru Sunja kuma Jiki yayi Nauyi,Ganin yanzu Ummi ta Manyanta Shiyasa Suka sama mata masu kyau har Biyu wadanda zasu rinka Taimakamata,Ya”yansu suna kula dasu sosai musamman ma Saleem da Malika Wadanda ke kusa dasu,Kafin Rasuwar Hajiya Sai da Sukaje kasa mai tsarki dukkansu,ahalin wanda Malika ta biya musu Dukkansu sukaje kasa mai Tsarki suka sauke Farali,ita ko da Saleem da ya”yansu basu san adadin Hajji da Umuransu ba,saboda sun mai dashi kamar zuwa Abuja daga Kano ne

Hajiya Malika Wacce ke Amsa mtsayin Malika Abdulmalik Dankasuwa,ada Sunan Mahaifinta ne yake yawo Aduniya amtsayin Wanda ya Mallaki Dukiya mai yawa,ammh Zuwa wannan Lokacin Sunan Malika ne ke yawo a ko”ina Domin ta Samu Cigaban kasuwancinta Sosai,kuma da Taimakon Mijinta ta Maida hannayen Jarin Dukiyarta Zuwa kasashen ketare,Malika tayi kyau sosai Fiye da Tunanin mai karatu ta kera jiragen sama Sunfi guda goma,ta kire Jiragen kasa,suma ba adadi bayan Ta bude Wani kamfani a kasar America,na Kera motoci wanda da Farko hannu jari ta Hada dasu sai kuma Daga baya ta Siya wajen ya zama mallakinta,agida Nageria ta Budema Matasa Shaguna Kala kala domin Dogaro da kai,Riba kadai zaka bata awata sauran Kudin nakane,Malika ta abude Gidan Marayu agarin Malumfashi da kumo,wanda ke amsa Sunan MALIKA ABDULMALIK ORPHANS Bayan haka kuma ta na da Kungoyoyi na Taimakon al”ummah mussaman ma ya”ya mata marasa galihu expecially Kungiyarta na MALIKA MALIK FOUNDATION kungiyace data ke Taimakon Mata da kananan yara,wadanda basu da iyaye ko kuma iyayensu basu da karfin da zasu dau Dawainiyarsu ta bangaren karatu da Sauransu akallah ta Dauki Nauyin karatun yara mata da maza Wadanda batasan iyakarsu ba,ta Fita da wasu kasashen wajen wanda suma bata san iyakarsu ba,tana DA office akaduna da Abuja,Tana da ma”aikatan na kusa da ita kamar Joda da Su Saleema Harta su Nadira da Zahra bata barsu ba,ta basu Mikamai acikin wannan kungiyar nata Suna taimakamata da abubuwa dadama,in wani Abu yataso zasu kirata Su Tattauna,duk da yanzu Dukkansu sun zama manya mata domin Nadira ma ya”yanta Biyar,sai Zahra dake da Hudu aciki harda takwaran Malika,harta Saleem din yanzu ya yarda komai an Dawo ana zumunci an zama Daya.

Malika bata Shiga Siyasa ba ammh an Sha kawo mata tayin haka,kawayenta yanzu sune Matan Manyan Sojiji,da matan Sarakuna kowani yanki tare da Matar Shugaban,kasa da Matan Ministoci Duk da su suke Shige mata ganinta Macece da bata da kyashi ko kadan,itako tasan zaman data take da kowa,Lbrinta Babu inda bai Tsaga ba ko”ina afalin Kasar Nageria da ketare ba gidan Tibi da jaridan da bata hira da ita,ba gidan Radion da bai gayyaceta yayi Hira da ita ba,duk kuma wannan Abun bai samu ba sai da goyon bayan gwarzonta kuma bangonta Mijinta Uban ya”yanta Wato SALEEM KABIR KUMO Domin Shi ya bata duk wata dama na yarda zata Gudanar da Rayuwarta ta Hanyar Taimakon mutane da Dukiyar da Allah y bata,duk inda aka gayyaceta wani taro baya haufin barinta Tunda zatayi Shiganta na Mutumci taje,ya”ya kuwa Ayda tana Wajen Saleema Domin Malika ta cika alkawari ta bata,Su Aryan kuma suna gidan su Ummi,sai su Maryam wacce Suke kira Hajiya da Abubakar Wanda Suke kira Sadiq,sai Saleema Ummita,sai Marwan da Suke kira Khalipa,Su kadai ne yanzu agida Agabanta suma din sun girma ba yara bane,sun iya kula da kansu musamman ma Ummita da Sadiq Tunda Sune manya,Mijinta kuma bata iya hadashi da kowa matukar Suna gida Dukkansu to kashe wayarta take,musamman ma Ranar Weeked dukkansu basu Fita ko”ina sai dai in Wani kiran gaggawa ne ya taso,suna Makale da juna suna kara jadaddama Juna irin son da kowanne yakema Dan”uwansa.

Merry da Dose dukkansu sun Musulunta Merry ta koma maryam ita kuma Dose tace ita Sunan Madam take so Malika,ganin ko sun koma garinsu Danginsu Bazasu Amshesu ba yasa Saleem da Malika suke Rikesu tamkar ya”ya yanzu Haka dukkansu Sunyi Aure,ammh Maryam merry tana nan Tare dasu don mai kula da Gidan Gonar Saleem take Aure,suna zaune agida daya,wani lokacin in Duka iyayen basu nan,shashenta su Ummita ke Zuwa ta kula dasu har iyayen nasu Su dawo duk da Sun Dauko goggo Hadiza tana zaune dasu,in ma anyi Hutu kenan in ko Lokacin mkranta ne dukkansu Mkrantan kwana Sukeyi nan Nagerian Turkish acdmey,ita kuma Dose Malika tana kaduna tana Auren Wani Matashi suna daga cikin Wadanda Malika tabama Jari domin dogaro da kai.

Malika ta Waiwayi Dangin Mahaifiyarta Dga Baya Tafiyar Datayi Shi Tare da rakiyar Mijinta Da Duka ya”yanta har Zuwa birin England,koda taje yawancin dangin Maman nata Duk Sun kare,saboda dama basu da yawa wanda suka rage kuma talauci da Taufa sun Rikitasu sosai,Dakyar ma wasu suka gane Malika Diyar Juliyat ne,suka Rumgumeta Suna kukan Murna,Malika tayi takaichi mai girma na yarda ta Fito daga wannan Tsatson ammh kuma bata da yarda zatayi wannan Shine zanen kadaddaranta,Sati daya sukayi kafin su dawo gida bayan ta cikasu da kudi Sosai da duk Abunda kowa Zai Bukata,kafin su taho da yawansu an samu Wadanda suka karbi Musulunci,Wasu anan ta barsu,wasu kuma ta taho dasu ta basu wajen Zama da aikin yi.Sai gashi Malika ta zama Abun alfaharin kowa,kowa na so yaji wani yace yana da alaqa da ita,kuma kowa na jin dama matar dana ne ko kuma dama kawar yata ce,saboda kyawawan Dabi”unta da kuma Yadda take kokarin Taimakon addininta da kuma Talakawanmu marasa karfi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button