MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

“Tunda yarinyarnan ta Shigo gonata ban huta ba,na Rama ammh kuma Kaikayi na neman yakoma kaina…Yazama dole na ninka ramuwa na akanta na ci ubanta dakyau yadda yakamata..”

Yake Fada yana dan mirmishi kafin ya Cigaba da kurban Ruwanshi,yana wani Yamutsa Fuska kamar an sashi dole.

Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan MALIKA MALIK Akan Naira 200 kachal????,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar 09069067488 Sai kun zo ina maraba daku masoyana..

Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal????shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani

07065481260..Ko kuma 09069067488

Shakira

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

ƖŊTҼɭɭƖƓҼŊT WɾƖTҼɾى ASSɷ????

Mallakar:Janafty????

Littafin MALIKA MALIK Na kudi ne ki biya kudin karatu akan Naira 200kachal????ki turo ta account Nomba kamar haka 0552179550 JAMILA UMAR GTB bayan kin dauki hoton Sreenshoot din Transaction  din,sai ki turomin ta wannan Nombar 09069067488,Ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488 shima kai tsaye bayan an dauki  hoton katin sai aturo*

~D last Free page,kamar yadda nayi alqawari so mai bukatar ganin Wannan Kafcen,na tsakanin Saleem da Malika,da kuma ganin salon soyayya cikin Ramuwa,sai ya biya kudin karatu ta Details din dana bada asama,Ina maraba da masoyana Masu son cigabana~

  12

    “”Sati Hudu cur Malika ta kwashe a general hospital tana samun kulawa kafin ta warke sumul abata sallama,shiko Alhaji Abdulmalik sai da yakara sati daya akan na Malika kafin shima sallameshi su rankaya su koma gida.

Ba laifin an samu cigaba sosai game da laluranshi,domin sun dorashi kan mgunguna,ga kuma gashin kashin dasukeyimai kullum,shiya taimaka wajen fara motsi da hannushi zuwa kafadanshi,shiyasa suka sakasu suka siya wata wheelChair,wacce daga kasar China ma,akayi odarta,wanda take hade da rimot din sarrafata jikin keken,basai an Tura mutum ba,tana da Abun control dinta ajiki,duk inda mutum yake so yana daga zaune sai ya danna ta kaishi ko”ina yakeso indai acikin gida ne.

Koda kafin Asallameshi ya dawo gida Tun yana asibitin Hajiya binta tayi tayi dashi ya bari su Fita dashi waje,ammh Alhaji Abdulmalik yaki bari afita dashi zuwa kasar ketare domin nema mai mgani,yace ta kyaleshi kila haka Allah keson ganinshi,ta kyaleshi kawai baya bukatar aje dashi ko”ina,hadda yan”uwansa ta hadashi,ammh yaki yarda da zencensu Dole suka rabu dashi basu da yarda zasuyi Tunda yaki yarda.

Jinyar Nashi sai takoma gida,wajen Hajiya Binta,duk da koda yana asibitin ita keda alhakin kula dashi,duk da kawu Shitu na taimakamata,toh yanzu ya koma gida,saboda hidimar gabansa da kuma iyalansa,joda ce kuma ta koma mkranta duk da yanzu wahalar ta ragu Malika ta warke sai Abunda Ba”a rasa ba na damuwa.

Yanzu Malika takoma kamar ba itaba,mgana ma sai yazama dole takeyi,kosu Dose da mery sunga chanji,don yanzu suna gama hadamata Ruwan wanka zata sallemesu,ta shiga tayi da kanta,ita yanzu kunyarma Duniya ta isheta,domin tariga data sani cewa lbrinta,da mummunar gaddararar daya sameta yagama zaga Duniya,shiyasa ko Excorts dinta duk ta sallamesu,Joy da peter kadai ta bari sai su mery da Dose,suma saboda masu kula da hidimarta na yau da kullum ne.

Gidan ko Da Alhaji Abdulmalik ya mallakama Saleem ko,sai dai aka bar megadin gidan yana kula dashi,Satin Daddy daya dadawowa gida sai ga Manajojin kamfanoninsa,dana gidan mansa,dake gida Najeria,sun kawo maza ziyarar dubiyi,da kuma tabbatarmai da zasu rike amanar dake hannunsu,sun nemi ganin Malika,ammh kiri kiri taki Fitowa daga daki,dole suka tafi suna masu tsausayama wannan Ahalin ga Dukiya har Dukiya,ammh ta gaza yi musu mganin damuwarsu.

Tsakaninnsu kwana biyu sai ga wakilan Hannayen jarinsa na kasashen ketare,mrs Suzan da Mr john Abraham,Sunzo duba jikin Daddy tare da rokon Malika ta dawo su cigaba da huldar kasuwansunsu tare,domin suna jin dadin harka da ita,tun kafin Daddy ya basu amsa Malika ta basu,ta sanar dasu bazai yuyu ba ita yanzu bata da sauran wani motsi ko wani Dubara aduniyarnan,kawai su cigaba da gudanar da komai,ga waya sai su dinga tattaunawa,ammh malika bata ko sha”awar Fita yanzu domin tana ganin Tabbas duk randa tafita sai ta samu masu Nunata suna mata dariya.

Ayanzu haka tarage shigar banzanta,ammh bata iya saka kayanmu na hausawa,sai dai ta sanya dogayen Rigana,irin na kamfanin Armani,sai ta saka gyalen doguwar rigarta ta yane kanta dashi,bata cin Abinci sosai,sai in Daddy ya matsata,shiyasa wani lokacin tafi son ta Wuni daki ta kwana bata Fito ba,sai dai in Daddy yagaji da cigiyarta ne sai Hajiya ta leka ta kirata,Abinci ko wani lokacin yadda su Dose suka jera haka zasu so su dauka,sai ta Wuni bata sa komai cikin bakinta,don ita ayanzu tafi kaunar mutuwarta Fiye da komai,don gani take tatashi A malika malik dinta ta koma Malika kawai.

Dr Abbas,shine Amintattacen Likitan Su Malika,tun tuni,toh bayan dawowarsu gida shi ya rinka zuwa yana duba Daddy agida duk bayan kwana,shiya sanar dashi ya daina zama adamuwa ya rinka samun abokin hira,yadaina zama shuru,shiyasa yanzu zaka ganshi zaune afalonsa, yayi tagumi shuru shi kadai,Hajiya binta ko wani lokacin take zama,dashi in ko tatafi kichen sai dai ya zauna shi kadai.

Ganin haka yasa malika tadinga daurewa tana zama dashi,ammh wani lokacin sai dai yayi ta mganarsa bata cewa uffan,daga eh sai A’a,daya mtsamata da Nasihan tayi hakuri,sai dai kawai yaga tana share kwallar kuka,sai ya kyaleta sai dai ka gansu sunyi zugum,ba mgana shi Alhaji Abdulmalik takaichinsa Daya ko azakar din nan bai iyaba,balle aje ga karatun alqur”ani,balle ya dinga karantawa ko azuciyarsane,shiyasa sai dai ka ganshi yayi zura gwanin ban tsausayi,toh balle ita yarsa tasa,da bata san komai na addini ba.

Gabadaya Malika ta tsorata da Abunda Saleem yayimata ko barci take ta dinga mafarkin Abun kenan,haka zata farka tana kamkame jikinta tana Fizge fizge tana bashi hakuri,Sai daga baya ta gano mafarki,kuka kuwa tayishi kamar idonta zai tsiyaye in tatuna yau wai itace bazawara,Abun na mata ciwo sosai,shiyasa suna ko mai harafin S taji an ambata sai ta zabura ta tsorata,balle a ambaci sunan Saleem kai tsaye yanzu zaki ga ta fara makyarkyata tana hawaye,Idanuwanta suna nuna tsoro kara kara,shiyasa ta haddace kaminshi tsab,kamar yadda ko ya Fada Yadda bazata manta Abunda yayi mata ba ,To tana jin har abada batajin zata manta muguwar Fuskar SALEEM KABIR KUMO

Sai ga Malika,yanzu duk wannan ji da kan da rashin kunyar datakema Hajiya binta bashi,tsakaninta da ita yanzu sai gaisuwa,yau an wayi gari Malika zata kalli Hajiya binta tace mata ina kwana,duk da daga nan bata kara cemata komai,ammh ko ba komai An samu cigaba sosai,haka da Joda tadawo,wlh ganin yadda Malika Takoma sai da tayimata kwallah,ada bata tsausayin Malika ammh dole duk wani mai imani ya tsausayamata,shiyasa itama taji kawai ta tsani ma Saleem gabadaya Tun sanda ya ketama Malika haddi,bana irin yadda addini ya koyarba,sai ta hanyar karfi kamar wani dabba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button