MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Ko amotar kanzil bai cemata ba,itama bata tankashi ba,shida Sadiq suke ta hiransu sai wani lokacin ne Sadiq ke sakota ciki  itako sai da ta murmusa,shiko Saleem da Sadiq ya sako malika zai dauke baki ya hade rai,Tun Sadiq bai Fahimta Ba har yagane ma’auranta sun Samu mtsala,baiyi mgana ba kawai yayi musu Fatan Allah Daidaitasu domin yasan koyayima Saleem mgana ba Kulashi zai yi ba.


Su ya marwan sun isa ba Dadewa sai ga su malika,Ummi ta Rumgumeta tana murna Abun mamaki Saleema tazo tana gaishe da malika ta kuma yi Saurin karban Ayda tana mata Wasa,sai ga Saleema ta dauki akwatunan Malika tace dakinta zata sauka,Ummi na mata tsiyan yau kuma Anty malika akayi Uwar daki da ita,tace eh yau Ummi ba bakuwar ki bace tawace.

Dakinta ta kaita ta Hadamata Ruwan wanka da kanta Ta Shiga tayi kafin tazo ta rama sallar mangariban data samesu ahanya,tana zaune kan Dardumar aka kira Issha’i ta mike ta gabatar kafin ta Fice Zuwa Shashen baki inda aka Sauke su Joda,ko da joda da kawayenta da yan’uwanta suka ganta sai suka Fara mamakin wace mota ta Shiga joda ce ke dariya tana Fadin”Lalle masu abu da abunsu mallam ne ya taso Abunshi..”Dariya malika tayi tana ma Jodan dakuwa,ta iskesu ankawo musu abinci kala kala da Abunsa suna yaba kirkin Dangin Marwan da mahaifiyarshi,Dariya kawai malika tayi tana kara gayamusu haka suke kowa nasu ne musamman Ummi da Abbi.
.

Batabaro dakin ba sai wajen goma na Dare Saboda ta karajin barci ga gajiyan zirga zirgan biki inda Allah ya taimaketa ma Ayda na Wajen Saleema kilama tayi barci,Falon babu kowa sa yan kumo suna hira,gaishesu tayi suka amsa cikin sakin Fuska suna tambayan Ayda tace tana Wajen saleema,daki ta Wuce koda ta Shiga ba kowa Saleema bata ciki,kila tana sama wajen Ummi,yadda barci yaci idonta ne yasa bata tsaya komai ba Ta kwanta tana jan blanket ta Rufe kafafunta dashi,cikinta kuma acike yake shiyasa bata nemi abinci,ba ko minti goma batayi barci ya kwasheta Saboda gajiya ko addu’an barci batayi ba.

Saleema ko tana Falon Abba,suna hira dukkansu iyalan wadanda sukan Dade basu hadu ba,ya marwan da ya saleem da ummi da Abbi da Sadiq sai Wajen 12 kana suka sauko bayan Ummi ta koresu tace zasu kwanta suma barci suke,Koda Saleema ta Shigo dakin dauke da Ayda Wacce itama ta dade dayin barci ahannun Abbi,ganin Malika na barci sai bata tasheta ba,ta kwantar da Ayda gefe itama ta Shirya cikin kayan barcinta kafin ta hayo gadon bayan Ta Rufe musu kofa kuma ta rage Wutan Dakin Kusa da Ayda ta kwanta tana kamkameta kamar wani zai Rabasu,dama ko banza Saleema irin Abbi suna da Son yara kanana.

MOMYN LADINGO.

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

Mallakar:Janafty????

KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada

33

………………Malika Saboda gajiya dakyar ta iya tashi sallar asuba koda ta idar idonta na Rufewa ta koma bisa gado,wani barci mai Nauyi ya sake Daukanta bata tashi ba sai pass 10 lokacin data tashi har Saleema tama Ayda wanka ta goyata,baki ma Tuni sun yi wanka sun karya Wasunsu Duk Sunyi Shirin Tafiya expecillay kawayen Joda da suke Zaria da kaduna Wadanda sukayi mkranta tare.

Yan kumo ma koda tatashi Tuni motarsu ta mika,lalle tasha barci itama wankan tayi ta Shirya cikin Wata Atamfa blue mai kwalliyan pourple ajikinta,Ta daura dankwalinta irin Daurin Zahra buhara,Sai da ta karya kana ta Saka babban Mayafinta ta yane kanta dashi kafin ta Fita tana gaishe da Ummi da Ya marwan Data ga suna mgana,Saleem na Wajen Shida Sadiq gaishesu Tayi Sadiq ne kadai ne ya amsa cikin sakin Fuska,shiko Mallam Fuskarsa ba Annuri ya amsa mata da lafiya lau,daganan ya Dauke kai Duk da yana Satan kallonta ta Gefen ido domin ba karya ta mai kyau sosai a ido kamar yatashi yaje ya Rumgumeta ya fadamata irin missing dinta dayayi ammh bazai iya ba,Tunda ita datayi laifi ta gagara bashi hakuri shiko bazai bata, sai sun koma gida suciga ba daga inda suka Tsaya.

   Daganan Shashen Da’a Sauki su Joda Ta nufa taje suka gaiggaisa chan tama tarar da Saleema,sai lokacin taga Ayda wacce ke barcinta lum abayan Saleema,ko da tashiga Duk suna ta haraman Tafiya ne,nan sukace tama ya marwan mgana Kawayen Amarya zasu Wuce,awayar Joda ta kirashi ta Sanarshi yace Su Fito koda suka Fito sukama Ummi sallama ta basu 20k tace su raba kafin Marwan yasa Direba ya kwashesu Zuwa tasha su hau mota su hudu Ne Shima 20k din ya basu yace Suyi na mota suka karba suna Godiya

    Koda Azahar tayi gabadaya yan kawo amarya sungama Shirinsu suka taso keyar Amarya Joda Zuwa Falon Ummi suka Damka amanarta gareta tare da yan Nasihu sai manya Robobi guda biyar,Daya na cincin,daya na Dubulan,daya na Alkaki,daya na hikima,daya na Nakiya,sai Buhun shinkafa Biyu dana Tuwo daya sai kwalaye suma Sunfi Ashirin gasunan burjit,ba laifi dangin Uban Joda sun mata kayan gara Sosai kusan katsinawan Dikko akwai kaya da Babban Harka.????

Ummi tayi ta Fadan meyasa suka Wahalar da kansu,sukuma sukace ai bakomai an zama daya basu zauna ba Suka bar Joda nan suma Direba ya kwashesu Shi zai maidasu Malumfashi,bayan Ummi ta cikasu da kudi da Turaman zannuwa aka Rabu cikin Mutumci da karammawa.

Sai Da daddare kana Abbi ya tarasu gabadayansu yayi musu Nasiha da Fada mai Ratsa jiki,wanda kowa Nasihan Abbi ya Shigeshi musamman Wajen da Abbi ke Nusar dasu hakuri da Mazajensu da kuma girmama Aure wanda Abu ne mai matukar amfani kana ya horesu da yaki da Shedan azamantakewarsu komai ya Shiga tsakaninsu na bacin rai kada su kullaci Juna Su tsaya su Saurari uzurin Junnsu su kuma ba junansu Hakuri wanda indai Sukayi haka Har Abada bamai jin kansu,kana daga karshe ya Horesu da su zama Tsintsiya daya madaurinta daya Domin Dukkansu yanzu sun zama Ahali Guda Daya,koda akabama Ummi damar mgana bata ce komai ba Domin tace Abbi ya gama mgana Albarka tayi ta saka musu,Hajiya ma ta tofa albarkacin bakinta daga karshe ta karke musu da Tsiya da mutunin nata Saleem,wanda yake Wani cin mgani,kamar wanda akama Dole.

   Tare Sukayi Dinner dukkansu Harda amarya da ango wanda ya zaku abashi dama ya kebe da amaryansa,Aiko suna gama cin abincin Abbi da Ummi suka Haura sama,shima yaja matarsa suka Fada dakinsa suka yi lum dasu,Sadiq ko afalo suka yada zango Shida Saleema Suna Hira,Saleem ko Dakinsa ya Shigo yana Dauke da Ayda ganin haka yasa Malika komawa dakin Saleema ta kwanta tana Tunanin mafita,Aranta taji komai ya sauka Duk Fushinta itama ta Saukeshi Takuma kudiri niyyar bama mallam Hakuri da Zarar sun koma gida

  Barci yafara kwasanta taji Bude kofa da Shigor mutum kamshin Turarensa kadai ya tabbatarmata da Shine,sai ta kara lafewa jikin katifa kamar mai barci gabanta yazo ya Tsaya yana Dauke da Ayda Wacce take ta Sharar barcinta cikin Aminci,Dukawa yayi ya Kwantar da ita gefen Malika yana yafa mata blanket din da malika ta Rufe rabin jikinta dashi…

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button