MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Momi batayi sanya ba ta Daga waya ta kira Abban Zahra tace ya dawo gida yanzu ba lafiya,jin muryanta cikin wani yanayi yasa ya umarci Direba daya juyo dashi gida,dama yana hanyar Zuwa gidan Wani abokinsa ne,koda yadawo gidan nan ya iske bakin lbri wanda ya kusa saka Zuciyarsa bugawa,yayi tambayan Duniyan nan Zahra taki mgana sai kuka take,daga karshema tashi tayi ta Shige daki Nadira tabi bayanta,ganin haka yasa Abba ya kira Layin Saleem din ammh kuma wayarsa tana kashe,sai ya sauya alaqaan kiran Zuwa ga IGP KABIE KUMO,wanda Shi Abba ne ma ke Sanar dashi Abunda ya Faru don su basu da lbri,ammh yabashi hakuri da janjanta lamarin inda yace zai Nemi Saleem din yaji gaskiyan batu

Abbi Ummi ya sanarmawa Abunda Bukar Mada ya kirasa ya sanar dashi kirji ta Dafe tana salallami,wayar Saleem tayi ta kira bata Shiga sai ta kira na Malika,bayan sun gaisa take Tambayanta ina Saleem,wanda lokacin yana dakinsa duk Wunin yau bai ci abinci ba saboda Damuwa da Nadamar Auren Zahra daya lullubeshi Malika tayi ban hakuri ammh yace ta rabu dashi bayason cin komai,Yana kwance akan gadonsa ta mikamasa wayar tana Sanar dashi Ummi na Son mgana dashi karban wayar yayi ya saka akunne alokaci daya yana gaida Ummi bata tsaya amsawa ba ta Shiga jeromai Tambayoyi kan Abunda Bukar Mada ya kira Abbi ya sanar dashi baiyi Nauyi baki ba ya sanar da Ummi duk Abunda ya Faru baki ta rike tana mamakin Zahra,Duk da Zahra tayi Abunda bai kamata ba,ammh Ummi tanuna Saleem yayi kuskuren yanke Hukunci cikin Fushi,ta kuma bashi Umarnin ya kira Mahaifin Zahra yamai bayani don daga mganarsa Zahra taki mgana,ya sanar da ita zai kirashi da Safe,da haka sukayi sallama tana Fadin Allah ya kyauta na gaba

Koda ta Sanar da Abbi lbrin da Saleem ya bata tsaki yaja yana Sababin Yarinta kenan da Shigen Rawan kai irin na Saleem,ammh ina shi ina mata biyu,da lokacin da ya Rarito an hanashi ba hanuwa zaiyi ba,ammh yanzu wa gari ya waya..? Allah ya kyauta ammh sam basu da Tunani inda suna dashi da duk haka bata Faru ba,shima Allah ya kyautan yayi toh babu wani gyara Tunda Saki ukun ya cika kemata sai Da Fatan Allah yasa yazama darasi garesu gabadayansu… 

  Hajiya Babba ko dataji Fada takamayi da saleem din wai meyasa bai bata kashin mutuwa ba kafin ya tarata,Shiko Ya marwan dama yace Daga ganin wannan amaryar ta Acp batajin mgama,Saleem ko sai Washegari ya kira Bukar Mada ya Warwaremai zare da abawa Tundaga Farko har karshe sai gashi Daga karshe Bukar Mada kebama Saleem Hakuri yace babu komai kanta tamawa,koda Hajiya Saratu momi taji batayi wani mamaki ba,don tasan wauta da sakarci irin na Zahra kuma ga Abunda Nadira tace ta kirata tana fada mata,duka Momi ta hada Fadan da kuma Takaichin Zahra ta Watsar illah ta Sanar da ita idai kan kishiya zata kare rayuwarta aiko Tana da Wahala don yanzu Rayuwa ta chanza ba lalle bane mazan yanzu su zauna dakai kai kadai ba,balle keda kika je kika tarar ammh har kina da kokarin Son ki kori ta ciki,wanna Shine kaikayi ya koma kan mashekiya.


Sai bayan kwana biyu kana Saleem ya warware,ranar monday ya Fita office,ammh adaren sunyi Tsiya da Malika kan tacemai ita daya nemi Shawaranta da bai saki Zahra ba,Wanman mganar Shiya batama Saleem Rai har ya Nunama Malika hakan,Dakyar ta bashi hakuri ya hakura ammh ada har ya dau Zafin da Cewa kila ko bata Sonshi ne,da har zata ce ya cigaba da zama da Zahra wacce bata son Jininsa toh aiko bata Sonshi karyan banza ne kawai.

Da Maman Abba Taji lbri sai da tayi Guda bayan ta juya Duwawau Tacema Malika ta tayata barka,domin Rabuwa da muguwar kishiya irin Zahra babban nasara ce,wanda zama dasu bala’i ne Tunda Zuciyarsu bata da kyau sam,Toh ita kanta Malika Tasan Zahra ba masoyiyarta bace,ammh sakin ne bai mata dadi ba,shiyasa ko da taga Saleem yasa anfitar da komai dake dakin Zahra an saka Sabbi tsoffin kuma yabama megadi yace yakai ma ilayanshi ya karba yana murna Hade da godiya,Sai merry ta koma tana kwana adakin,joda kuma bata dade ba takoma Katsina wajen Hajiya.


Yanzu gida ya rage daga Malika sai mijinta Saleem sabuwar Soyayyah mai dauke da Sabuwar Rayuwa mai cike da muradi da burgewa nan suka bajema juna yadda suke kaunar junansu,kowa yana kafa kafa da Dan’uwanshi bayason bacin Ransa,gefe daya kuma suna kula da yarsu Ayda wacce take kiba tana kuma kara girma da Wayau,gefe daya kuma Malika na ta Shiryen Shiryen Biki wanda Abun ya Hade mata gata wan mijinta ne,Gata kanwar amarya kuma kawa gareta,gata kuma ta wani bangaren tamkar Uwa take gareta Tunda komai na Shiryen Shiryen bikin Hajiya Binta ita ta sakarmawa Shiyasa koda yaushe cikin mgana Suke awaya don ganin yadda Abubuwan zasu tafi kan Tsari.

Am Srry For d late update,wlh haryanzu jikina sai Ahankali,and kuma kuyi hakuri da Typing errors bansamu lokacin Editing ba..

MOMMYN LADINGO..

MALIKA MALIK…!
(Sai na rama..)

Mallakar:Janafty????

KUDUBI GIRMAN ALLAH KUREMIN AMANATA,NAYI MUKU ADALCI NIMA INA BUKATAR KIYIMA KANKU KUYIMIN ADALCI KADA KU FITARMIN DA BUK WAJE DON ALLAH????

Kada ki karanta inda baki biya ba,inda kina so kiyi karatu cikin salama ki biya kudin karatu akan 200kachal???? ta wannan account Nombar 0552179550 JAMILA UMAR Gtb ,ko kuma katin Mtn ta wannan Nombar 09069067488,Aturo hoton kai tsaye,ta Nombar dana bada

31

“””Shiryen Shiryen biki na cigaba da Wakana ta bangarori da Dama,kadama Uban gayyar yaji lbri yafi kowa Zumundin Aure Fiye da kowa shiyasa ya saki bakin aljihu ya sakarma Ummi kudi ta Aika Dubai akayo mata odar akwatuna da kuma kayan alfarma na gani na Fada,sai wanda ya gani akwati 10 cif aka Hadama Joda wanda kudin da”a ka narka kan kayan dake ciki ba kananan kudi bane.

   Bikin an Shirya Sosai ta bangaren Amarya da kuma bangaren Ango,bikin na Saura Sati biyu Hajiya Binta ta kira Malika awaya tana Sanar da ita Dangin Mahaifin joda sun aikota mata kan basu yarda Joda ta zauna awajenta ayi Taron biki ba,suna bukatar Yarsu ta dawo wajensu da zama har zuwa Ranar Daurin Aurenta,Daga yadda Hajiya Binta ke mgana zaka gane bataji dadin Zencen na Dangin Mahaifin joda ba,ammh sai malika ta shiga bata baki tana Nuna mata babu ta kyale Joda ta tafi bakomai aciki sai su tattara su Bita chan malumfashin bayan andaura Aure aka dauko amarya bashi kenan ba,Kalaman Malika su suka kwantarma da Hajiya da hankali Sukayi mganar da zasuyi kafin su yanke kiran.

Malika ita take Sanar da Saleem Abunda Dangin Joda sukace,bai damu ba yace hakan Shine Daidai Tunda gidan Wan mahaifinta Za”a Daura aure,daganan sai adauko amarya Zuwa Abuja basai ankara wahalan Zuwa Katsina ba,kafin ma Malika ta kira Ummi Ya marwan din yama su Ummi bayani kuma Suma sun gamsu,kuma Sunyi Na”am da hakan Tunda zai ma Fi sauki da ada sai ankoma ta katsina an Taho da Amarya…
 
Biki na Saura kwana goma Ummi ta Shirya kai kayan Auren Marwan,tare da kwalayen minti dasu Sweet sai goro da tabarmu harda buhun Shinkafa da Su Taliya da makori da sauransu da kudi 100k na amarya da kawayenta sai kayatattu  katinan da’aka bugo mussaman Domin Amarya,koda Ummi ta nemi malika datazo Ana gobe Abuja ta kwana Washegari suyi sakko Zuwa katsina in Hajiya Binta tagani dagachan sai Su Wuce Malumfashi,Aiko da Malika ta Sanar da Saleem murje ido yayi ya bala Toka yace wa..? Shi ba dan iska bane da zai barta tayi wannan Doguwar Tafiya ga Ayda jaririya kawai taje ta kwaso mata mura,kana kuma uwa uba Shi tatafi ta barshi da wane,Wlh kada ma tasaka rai bazata ba,Tun Tarihin zaman Saleem da Malika wannan ne karo na Farko daya hanata Abu taji Ranta yabaci wanda tayi kokarin Danne Fushinta ammh kuma ya gagara sai da ta bayyanashi,saboda takaichi sai da tayi kwallah,Ammh Saleem ko ajikinsa,da Ummi ta kirasa sai yayi mata karya da Malikan batajin dadi ne,kuma Ayda ma Tana mura baza ta samu Zuwa ba,harga Allah Ummi ta yarda shiyasa ta kira yan kumo suka taho Suka Dumguma zuwa kai kaya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button