MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Zahra ta Tabe baki tana Fadin”Wai keda waye kike wannan uwar Kashe muryan..? Ba dai da Tsohon Likitan ba,.? Wani Mirmishin Takaichi Nadira tayi kafin tace”Eh dashi ne,kuma ke kika ga tsoho nidai bangani ba kuma,kinsan Allah best ina Son Dr Hambali sosai kuma da izinin Allah Shi zan Aura..”

Kwalalo ido Zahra tayi tana Fadin”Kutumar ubanchan,best kina da hankali kuwa..?tsohon zaki Aura mai mata har biyu da ya”ya..”.?.”Wani Dirty look Nadira ta sakarma Zahra kafin tace”Eh Shi fa,ko yana da wani Aibu ne,ok sai yanzu nagane ina kika dosa,Saboda yana da mata harda ya’ya ko? Toh ni ba Ruwana da matansa balle ya”yansa Ni da Zuciya daya nakeson Dr Hambali,kuma da Zuciya daya zan Shiga gidanshi matanshi kuma zan basu girmansu a matsayinsu na wadanda ke gaba dani ba Ruwana da kishin Hauka,kishina kenan shine na koyi yadda zan tsaya azuciyar mijina ta hanyar mishi biyayyah da yin Duk Abunda yake so,ya’yansa kuma Suma ya”ya ne Tunda Shine Ubansu kuma soyayyar gaskiya Shine kaso Uba kaso ya”yanshi Shine maganar Gaskiya…”

Tafada tana mikewa Zahra data daskare tana bin Nadira da kallon Mamaki,kafin Ta Hadiye miyau mai daci tace”Yanzu ke Nadira sai ki Shiga cikin kishiyoyi har biyu..? Tabe baki Nadira tayi kafin tace”Toh Shine me..? Naga dai kowa ya iya allonshi ya wanke,balle ma dukkansu matan nasu muna waya dasu Anty Umaima da Anty Bilkisu basu da Wata mtsala,kinga Zahra keda zaman gida ke Burgeki gaki gashi ammh nikam kinganni nan nakusa tashi,kuma mganar Auren mai mata da kike mgana in ka tsarkake zuciyarka ka Shiga da Zuciya daya wlh ko mutum nada Mugun Nufi akanka sai ya koma mai..”Daga Haka ta kada kai Ta Fice daga dakin tana wake wakenta ko ajikinta..

Da kallon mamaki da al’ajabi tare Da Nadama Zahra ta Bita,domin ta Fahimci mgana ne Nadira ta sakamata Awasa wandada suka Zafeta sosai,Tagumi ta lafta tana Nazarin Rayuwarta ta baya Sai kawai taji Hawaye suna zubomata,Tasani cewa malika bata taba kulla tanta ba kuma ta sani macece mai kirki sosai ammh son Zuciyarta da mugun kishinta ya Rufemata ido,harta kaita ga Aikata Abunda yazo ya Rabata da mijinta mai sonta da kaunarta,Kuka yazoma Zahra ta Fada kan gado,tana kuka abayyane mai cin Rai Tana juya mganganun Nadira acikin aranta,duk da Nadira bata taba bata Shawaran banza game da zamanta da Malika ba,aamh bata tsammaci zata iya murje ido ta Fadamata wadanan bakake mganuganun ba,Abun ya mata ciwo sosai Wuni tayi kuka tana karajin Nadamar Abunda ta aikata ta kuma dama ace Ana Dawo da hannun agogo baya data Ruga da Gudu ta gyara kuskuran datayi abaya,da yanzu tana gidan Mijinta cikin kwanciyar Hankali Nadira bama zata ganta ba balle harta gayamata wadanan Bakaken mganungun.

  Anan zan dan yi jan  hankali garemu mu yan mata Wadanda muke Waje bamu Shiga daga ciki, ba babban burinmu Shine in mai mata yazo yace yana sonmu,Abu na Farko Shine bazamu Tsarkake Zuciyarmu ba,balle mu barta ta sakama na alheri A”a sai mu bari Shedan ya Shiga Zuciyarmu yana zugamu kan in mun shiga gidan kokarin mu,Mu Fitar da wacce muka samu aciki,bama Tunanin ita ya taji lokacin da mijinta ya auro ki ya kawoki cikin gidan..? Bata kishin Mijinta..? wlh yan mata muna Kuskure Shiyasa Auren zamanin nan kwata kwata baya karko saboda Zuciyarmu ba alheri muke Shiga gidan Aure,shi kuma Allah sai ya barmu da Dubaranmu,daga karshe inta ciki ta tsarkake Zuciyarta Daga karshe ke baki Nasarar Fita da ba, ke ki kori kanki da kanki,wlh mata mu Farka mu chanja munanan Hallayyarmu na zafin kishi wanda bazai kaimu ko”ina ba sai ga Halaka,mune fa da munji wata kawarmu zata auri mai mata ko za”a kara mata Kishiya jikinmu na raawa mu wanke kafa muje mu sameta,in munga ta kwantar da Hankalita Zunciyarta mai kyau ne,sai mu hau cewa koke kina Zaune haka kishiyafa za”a miki ko kuma ke ko yanzu wance me ya’aike ki Shiga Gidan Kishiya kuma kike Zaune baki mike Tsaye ba..? Kuji fa wani zence ..? Toh Ta mike tsaye da me? Wlh da kin yarda da Shawaranta kingama wayo don Maza yanzu Sunfara tsada kuma na garin yanzu Sunyi karanci iskanci kadan zakiyi ya taraki gida wlh da anyi mgana yace Ga mata nan Sunyi Arha kamar ledan pure water,zai maida gomanki wlh,Toh ki natsu keda kika samu Shiga ki sadda kai Ki kuma tsarkake Zuciyarki da Tsoron Allah,ladabi ,da biyayyah ga mijinki kada ki daina,ko aure yace zai kara kada ki zama ballagaza yi kishin musulunci Kina nuna kinfi Shi so ma ya Raya Sunar ma’aiki sai kiga ya Saki jiki,in kina da Rabo ma sai ki tashi da makullin motan Uwargida ta bada Halin kai????ke kuma ta Waje ko Kinshgo wlh bazai bari ki Raina matarshi Saboda Abunda tayi Darajanta ya karu ko kin Shigo da mugun Nufi sai kiga daga karshe yakoma kanki,Toh Shawarata gareku Shine keda kike Ciki kada kiyi Wasa Damke Abunki don duk yadda kika kai ga Raina mijinki in Wata zata sameshi Sarki zata maidashi saboda gata da so???? So Tun Wuri ku sauya taku,Domin nima ina kafa kafa danawa kada wata tazo Wuf tamin pdp ta Ture gwannatina na Shiga uku????,ammh bayan fa na Tsarkake Zuciyata,ALLAH YAYI MANA JAGORA YA KUMA TSARKAKEMANA ZUKATANMU AMEEN SUMMA AMEEN

Haka Zahra ta Wuni kukanta bamai lallashinta don ko Nadira ta dawo dakin Ta ganta tana kuka,ammh sai ta bata tanka ba kuma harga Allah ta gayamata hakane ta kara ankarar da ita kuskurenta bawai don gori ko Cin Zarafi ba.


Karamar mgana Fa ta zama babba Domin Mganar Auren Nadira da Dr Hambali ta Tabbata domin har iyaye sun Shiga ciki Dr Hambali ya Turo magabatansa wajen Abba sun Nemi Auren Nadira kuma yabasu kama daga yadda yayi binciken Shi Dr Hambalin Mutumin kirki ne,An sanya Rana Wata biyar masu Zuwa murna wajen Nadira ba’a mgana Zumudi take Abunda tare da kara Fito da Salo Salo na Soyayya ga Angon nata Dr Hambali.

An saka ranar da Sati daya sai ga Jerin matan na Dr Hambali da ya”yansu sunzo gaida momi su kuma ga amaryar tasu Nadira,ku kanku Abun sai ya burgeku yadda suka zo suna wasa da Dariya momi haka suke cemata momi sama momi kasa,Dama Nadira tunkan suzo ta yi musu kayatattacen Tarba,bayan ta tsala wankanta,haka ya”yansu suka zagayeta suna Kiran Anty Nadira kaza,Anty Nadira kaza,haka suma iyayen nasu Duk dukkansu sun Girmema Nadira Nesa ba kusa ba,ammh suna Darajata,musamman ma yaddaa Nadira take basu girmansu Daidai gwargwado Tunkan ta Shigo kuma hakan ya samo Asali ne da adalcin miji da suka samu kuma Dukkansu Zuciyarsu mai kyau ce…

Nan suka Wuninma Nadira sai yammah kana Dr Hambali yazo ya Daukesu harda momi da Zahra amasu rakiya, wacce Abun ya tabata,taji dama itama Tun Farko ta kwantar da Hankalinta ta tabbata Malika sai ta mata Abunda Matan Dr Hambali basu ma Nadira ba,momi Dubi biyar tabama yaran suka ki karba sai da iyayansu suka saka baki,itakuma Nadira tabama matan nashi kyautan Turaruka,suma dai dakyar suka amsa sai da Dr Hambali ya saka baki,haka suka rabu cikin farinciki kowani bangare Sun Tafi cike da Kewa da Farinciki,suna Tafiya momi na ganin Zahra da zata shiga daki tana Dauke Hawayenta itako Nadira Kichen ta Nufa domin ta Zubo abinci hayaniya yahana ta ci,Da kallon Tsausayi ta bita kafin ta kada kai Aranta tana Fadin Dama Allah ya kadarra baki da dogon Zama achan Zahra Allah ya baki wani mijin,yakuma sa wannan Abun daya Faru ya zama darasi agarki,agaremu,agareni ni mai Rubutun,da kuma agareku masu karatu Ameen ya Allah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button