MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Sai da tasha ruwan sosai kafin ta zubda Sauran Tana ajiyar Zuciya Kallonta yayi yana duba agogon Fatan dake hannunsa yana Fadin”Kinga Malama zaki tashi mu tafi ne,ko kuwa ni nayi gaba ne..? yafada yana Wani kallonta a hagunce,Tana jin haka tafara kokarin mikewa,ammh kuma takasa,saboda kanta dataji yayimata Nauyi,dafe kasa tayi tana cije baki ta samu ta mike tana Mustsike ido,ammh kuma kafafunta na rawa,ganin zatayi baya yasa tayi hanzarin mikamai hannu ya kamata,ada yaso yaki mikamata hannun nashi ne,ammh ganin dayayi zata Fadi da gasken shiyasa ya mika mata hannunsa da karfi ya rikota tayo Rimi ta fado jikinsa bata samu masauki ako”ina ba sai Afaffadan kirjinsa.

Dukkansu sai da jikinsu ya amsa,shi harda sakin ajiyar zuciya ammh Siririya,ganin suna bisa Titi ne,kuma mutane na Wucewa suna ganinsu,shiyasa ya sassauta rikon dayayi mata yana Fadin”Ke miye haka,baki da kunya ko? yafada yana kallonta cikon ido,bata kulashi ba Tunda ta samu ta iya tsayuwa da kafarta sai kawai ta sakeshi ta Wuce ta Shiga mota tana sauke Numfashi.

Tabe baki yayi Ya shige bangaren Direba yana kokarin tashin motan ne yaji muryanta tana Fadin”Ban yi sallah ba..”Bai ko kalleta ba sai da ya tashi motan ya daidaita bisa Kwalta kafin ya kalleta yana Fadin”Ke wai don Allah hala ni bawanki ne? karki ka ga nayi Shuru na kyaleki kina Abunda kika dama,Tun dazu daga kice wannan sai kice wannan,kamar kin samu wani sakarai ko bawa,Toh bari kiji kada ki dauka don Mahaifinki yabani amanarki,zan lalace agindi ina miki bauta ba,u bettee stand up yarinya,don Wlh ni ba bawanki bane,uselless girl kawai…”Yafada yana Huci.

Hawaye suka wanke mata Fuska ta sadda kai tana Sharbewa wani wawan tsaki yaja yana Fadin”Ji bakinta don Allah,wai banyi sallah ba..? Ke dama kina sallah ne,kin ma san wani Abu waishi addini ,tsayama don Allah plz ke musulma ce..? Yafada yana kallonta kai tsaye duka hannunsa na kan Sitiyari yana murzawa,dagowa tayi ta kallesa Idanuwanta cike da mamaki bata samu zarafin mgna ba ya katseta da cewa”Eh nace ke Musulma ce? Koda ke musulma ce,ina tamtama da addininki don ban yarda da Kalmar shahadanki ba,sai na kara fada miki kin tabbatarmin tukunnah..”

Jagale Tayi tana kallonsa cike da mamaki,gefe daya kuma Zuciyarta cike da tsoro na,hallayar Saleem wadanda suke Fitowa daki daki,ganin yadda take kallonsa tana tsiyayan hawaye yasa ya watsamata harara yana Fadin”Stop looking at me,in ba haka ba yanzu na chanza ma Fuskarki kammani,Bush girl..”

Tana jin haka ta maida kanta gefe,tana tsiyayan hawaye,kukan tsausayin kanta na kamata,tanayi tana saka gefen hijabinta tana Sharewa hawaye dagan motar ta dau Shuru,tuni ya taka motar yana Gudu son Ranshi kamar zai tashi sama.Itako Tun tana kuka har ta hakura wani barci ya sake kwasheta ta sulale bisa kujeran motan tana barcinta,sau daya ya kalleta bai kara,ammh Ransa in yayi dubu ya baci gabadaya an kashemai Rayuwa,tsakani ga Allah.

Yana shiga gidansu Ana kira kiran sallah mangariba,har yasa motar nashi aparking space Malika bata Farka ba,shikuma bai tasheta ba,sai da ya Fito ya bude booth din motar Megadi ya cida akwatunanta zuwa cikin gida yana masa barka da zuwa,Bude motar yayi inda take ya duka ya fara marin kumatunta yana Fadin”Ke..Ke..Tashi mana..”Dakyar Ta bude ido tana binshi da kallo idanuwanta suna budewa dakyar.

Gaba yayi yana kokarin ciro wayarsa Daga aljihu wacce ke neman Dauki,sunan Abbi yagani,bai daga ba illah waigowa da yayi yana kallonta ta Fito daga motar tana tafiya dakyar,Wani kallo yake mata na lalle yarinyarnan,ganinshi tsaye yana jiranta yasa ta daga kafa ta cimmai,bai mata mgana ba,yayi gaba tana binshi abaya tana kallonsa yadda yake komai cikin izza da jarumta,Aranta tana Fadin ga Namiji har Namiji ammh ya bata kanshi da mugunta da mugun Hali.

   Ummi na zaune Afalo ita da Hajiya suna hira,suka ga megadi na Shigo da akwatuna,cike da mamaki suke binsa da kallo har ya dire Akwatun a tsakiyar Falon yana haki,Hajiya tace”Kai daga ina kuma wadanan kayan? Bakinsa awashe yake Fadin”Magajin yallabai ne,ya iso yanzu..”Kowa yasan haka yake cemai Basu samu zarafin mgana ba,sukaji sallamar Saleem ya Shigo Falon bayanshi kuma Malika ce tana Tafe tana kalle kalle.

Da hanzari Ummi da hajiya suka mike,Hajiya ce ke Fadin”Lale..Lale marhababiki..”Take Fada bakinta washe,lokaci daya da”a tarihin rayuwar malika datataba dukawa tana gaida wani,har kasa ta zube saman cafet tana Fadin”Ina yini..”Bakinta na rawa,Hawaye na tarowa a idanuwanta,tarota hajiya tayi tana Fadin”A’a tashi ya’nan nan ma ai gidanku ne..”Saleem dake gefe yaji kamar ya make Hajiya saboda shisshiginta,Tsaki yaja aciki yana kallon Ummi yace”Ummi na Fita yanzu ko? Hararansa tayi tana Fadin”Bansani ba…”Kwabe Fuska yayi kamar zaiyi kuka yake Fadin”Nidai wlh An tsaneni agidan nan,daga dawowata ba wanda yayi kewata,Abbi ya koroni ke kuma yanzu kina hararata..”

Malika dake zaune kan kujera kusa da Hajiya take binshi da kallon mamaki,ashe dama ya iya mgana cikin Dadin rai,Bata gama mamaki ba taga Ummi taja kunni da karfi kafin ta Mangareshi a keya tana Fadin”Eh din an tsaneka ka gyara halinka in kaji haushi..”Kara yasa yana yarfe hannu yana kuma rike kunnashi Dariya hajiya tayi tana Fadin”Ke Aisha,wannan ai ba duka bane tabashi kikeyi,ki gaframai mari mai zafi kigani in zai kara mgana..”

Wani bad look yabama Hajiya kafin ya Daga hannu yana Fadin”Eh sannu fa,toh bata gafrin ba ko ke zaki Gafra min ne,Uwata…”Mikewa tayi tana Fadin”Sosaima kuwa yaro..”Ganin Ta nufoshi gadan gadan yasa ya arce da gudu,sai suka ci karo da Abbi wanda saukowanshi kenan jin hayaniya,Rikesa yayi yana bin Ummi da kallo wacce ke gefen malika suna gaisawa,Yana ganin Abbi sai ya kame hannunshi A gefen kunnenshi yana Fadin.

“Sir…”Mirmishi yayi mai kafin shima kawai ya kamemai,dariya su Ummi suka saka ita da Hajiya itako Malika mamaki Saleem ke bata,ashe ya iya mu”amala da mutane haka? Rikosa Abbi yayi har zuwa wajen dasu Malika suke,wanda tayi saurin mikewa tana gaishesa da Abbi,saboda kunya mutumin ba tun yau ba,tun yana zuwa duba Daddynta.

Amsa mata yayi yana tambayanta ya Daddnyta da jiki asanyaye take karbamai,Ummi ya kallah yana Fadin”Kamata Aisha ki rakata dakin Saleem din,ki saki jikin yata,nan ma kamar gidan ku ne kinji..? Gyada kai tayi,ammh gefe na zuciyarta na rawa da Fargaba hade da tsoro,na jin ance a kaita dakin Saleem.

Shima yana jin haka ya gimtse Fuska yana Fadin”Dakina kuma Abbi? ina laifin Saleema,tunda yar’uwantace mace..”Karo na Farko Da Daddy ya mangareshi akai yana Fadin”kaga naka nan, don yar”uwantace mace,ko saleeman na nan ai kafita kusanci da ita,ba matarka bace ok baka tuba ba ko,dama tuban na karya ne..”?Da sauri ya rike hannun Abbi yana Fadin”No Abbi wlh Tuban gaskiya ne,nakuma yi niyyah bazan kara aikata makamancin haka ba..”Gyada mai kai yayi yana Fadin”Gud..Maza dauki kayanta ka shigar mata dashi,ke kuma Ummin Marwan,ki sama mata Abunda zataci Tunda sunsha tafiya…”

Hajiya tace”Gaskiya kam,gashi kuma kusan mace mai shigan karamin ciki yanzu duk jikinta yayi mata Nauyi. “Afakaice ya zabgama Hajiya harara yana kunkuni aranshi,yana gani Ummi ta rike malika suka nufi dakinshi kamar ya kurma ihu ba dama.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button