MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Yana Dariya ya kai bakinshi Saitin Kunnanta yana Fadin”Don Allah nayi….”Da Sauri ta dago ta kalleshi kafin tace’Kayi me…? Ido ya lumshe kafin ya Shafa saman Nonuwanta har Zuwa saman karamin matashin Cikinta kafin ya gangaro Zuwa kasar maranta yana Shafawa ahankali,kafin yace”Wannan…”yafada yana Kokarin Turamata hannu cikin wandon jiknta,duk da ya kashe mata jiki,Tureshi tayi tana Fadin”lalle naki wayon,na kwada wani yanzu..”Tafada Tana Nufar hanyar kichen din,Ganin Haka yasa ya Ijiye Filet din a bisa kujera ya isa gareta da Sauri sai dai taji ya Dagata sama cak yana Fadin”Ni da Hakkina adnga min yanga,lallema yarinya..”Yafada yana Dariya,itama Dariyan take tana bugunshi akirji tana ihun ya sauketa,shiko bai Direta ko”ina sai kan gadonsu,tana kokarin Tashi ya bita ya Danne,bayan ya sakarmata Nauyinshi,Baknta take kokarin Budewa sai yayi Caraf ya Hade bakinsu waje Daya.


BAYAN SATI DAYA

Aikin ginin Masallacin da makarantan Da malika ta gina Tuni ya kammallah har sun kirata sun Sanar da ita,itakuma sai ta Sanar da Saleem,shine ya bata Shawaran Asanar da jama”a Saboda su samu hallartan Taron Bude Wajen,da kuma Addu”a Ga Daddy,Malika ta yarda da Shawaran Saleem nan aka Fara Sanar da gaddamar da makranta da kuma Masallacin da Malika malik ta gina y’a marigayi Alhaji Abdulmalik Dankasuwa domin Sadakatul Jariya Zuwa gareshi wanda zai Gudana agarin Malumfashi RANAR ASABAR Da misalin Karfe 9 na Safe.

Kafin kace kwabo wannan Budaddiyar Sanarwan Hade da Gayyatan ta iske kowa yaji sai ya sakama Malika albarka domin akwai ya”yan masu dashi da yawa wadanda iyayensu ke Mutuwa su bar musu Tarin Dukiya,ammh bazasu taba Tunanin Yi musu Sadakatul jariya ba sai dai Suyi ta Facaka da kudi suna Abunda suga dama,ammh sai Gashi Malikan da ba”a taba Zato ba tama kowa mamaki,kuma wannan ba komai bane,Sila illah Saleem wanda Shine keda kaso 90% wajen Daidaita Rayuwar Malika hartazama Abun yabo da koyi awannan zamanin.

   Ranar taron Tun wajen Karfe 8 Suka isa Malumfashi ita da ACP SALEEM dinta,cngam dinta kenan,suna Sanye ne da Shadda mai Ruwan kasa,wacce akallah zatabama Dubu 50 baya Saboda Yadda take Fitar da maiko da yarari,Shi Saleem yayi dinkin Tarzace ne Dinkin Muhammed na Samarin zamani masu ji da kyau da Mukami,Da hulansa Zannah bukar wacce take Kalan,Ruwan kasa ajikinta haka takalmin kafanshi ma Rufaffe ne Mai Kalan Ruwan kasa,hadadde na Fatan Damisa,hakama agogon Fatan Dake Hannunsa,shima Kalansa kenan wanda na kamfanin Rado ne…

Itama Malika Dinkin Jikinta Riga da zani ne,Stone work ne,Rigar harpjmp ce,domin ta sauko mata har Gwiwa,sai Babban mayafinta mai kalan Ruwan kasa,da Takalminta mai Dudu Shima mai kalan Ruwan kasa,hakama yar karamar Jakar dake Hannunta,agogon Hannunta kala daya ne,dana Saleem ammh Shi nashi is For men,ita kuma nata For women ne????in ka gansu sai sun Burgeka kaji kana ta kallonsu baka sani ba,saboda yadda suka zama Abun Burgewa.

   Taro yayi taro wanda ya Gudana a haraban sabuwar mkranta Wacce dama masallacin ke kusa da mkrantar,Abbi da Ummi sunzo,hakama Hajiya binta tazo,hakama manyan malamai hadda Dan majalisar Dake Wakiltar Malumfashin yazo,Yan jaridu harda gidan Talabijin duk sunzo daukan gani da ido Bayan Bude taro da Addu”a inda Wasu karin bayanai suka gudana,sai kabama Malika damar mgana,wanda Tunkan aFara gabatar da Taron ta Fara Hawaye, Saleem ne yake Damke da hannunta alamun lallashi,ta Fita ta karbi Abun mgana ammh kuma ta kasa mgana,saboda Tunawa Da Daddyta datayi Abu daya ta iya Fada Bayan ta mika godiya Allah (SWA) sai ta koma mika sakon Jinjinarta Zuwa ga gwarzonta kuma bango gareta,wanda Shine Silan Faruwa komai,shi zata mikama sakon Godiyarta,kuma ta Wakiltashi amatsayin wanda Zai yi bayani Amadadinta,Awajen babu wanda baiji kwallah ba,lokacin da Malika ke Fadin ta Gina wannan mkrantan ne Fisabilla da kuma Sadakatul Jariya ga,Mahaifinta Allah yaji kansa Da Rahma,Kuka ne yaci karfinta,sai da Saleem yazo ya kamata ya Rumgumeta ya maidata wajen zamanta,,taron bai wani jima ba akayi Abunda ya kamata,Malika ta dauki Nauyin malaman mkratan da duk Abunda za”a bukata karatu takeso akoyar kyauta batare da an anshi Sisin kwabon wani ba,Anyi Addu’o’i Da fatan Allah yajikan Daddy,ita kanta Malikar tasha addu”a da Fatan gamawa Da Duniya lafiya kafin Taron ya Tashi bayan an gaddamar da Sunan masallacin MARKAZUR UMAR BIN KHAD’DAB Sai Shikuma Mkrantan MADARASATUL UBAIYU BIN KA’AB.

Basu kwana ba Aranar suka Jiyo zuwa zamfara,Ranar dai Malika Mutuwar Daddy ta dawo mata Sabuwa don da suka Dawo haka ta kwanta akan gado tana kuka mai Cinrai,Sai da Saleem yayi ta lallashi da jikinsa da hannunsa kana ta bar kuka ta koma tana Sakin ajiyar Zuciya,koda Dare yayi zazzabi ya Rufeta Ruf ta kwana tana Nishi sai da Saleem ya tasheta ya bata mgani,kuma yasa Ruwan sanyi bayan ya Rika jiko Towel yana matsa mata jiki dashi,shine taji sauki har kuma ta Samu barci.


  
Sannu bata Hana Zuwa sai dai Adade ba”a je ba,an kuma ce Duk Abunda aka Sanyama lokaci Toh zai zo,gashi har bikin Nadira da Dr Hambali yazo,sauran Sati daya inda Shirye Shirye ya Kamkama Aduka bangarorin,Nadira tayi gayyah sosai kawayensu na mkranta da kuma yan uwa da abokan Arzuka,Har Saleema sai dai ta kaima kati da Minti gayyata bayan kuma ta Tura mata ta waya,.

Saleema tayi mamakin ganin Nadira tazo har cikin Asibiti ta kawo mata kati  gayyatanta Zuwa wajen Bikinta,nan nema Saleem ke Fadama Nadira itama asanya lokacin Bikinsu ita da Ya Sadiq,wanda nan da Wata uku ne lokacin take gama Housemanship dinta,Tayi Mata Fatan alheri tare da mata alqawarin indai tazo bikinta itama zata Sanar da Dr tasan bazai hanata ba,sun Rabu cikin Aminci inda Saleema ta mata alqawarin zata zo insha Allah.

Abun mamaki Nadira bata Sanar da Zahra ta gayyaci Saleema ba,shiko Saleem, Bukar Mada da kanshi ya Kirashi ta waya ya Sanar dashi,bayan kuma ya Turamai sakon gayyata ta waya,anyi haka da kwana biyu Sai ga kiran Nadira,bai da nombarta lokacin don ya Dade da Shareta da nata dana Zahra na Abba kadai ya bari,shima saboda yana kiranshi suna gaisawa ne, kada ya goge Watarana ya kirashi yace waye????yace baida mutumci,yana dagawa bayan sun gaisa tace itace Nadira,yaji mamaki sosai nan take Sanar dashi mganar bikinta tare da cemai tana gayyatanshi Daurin aure,kuma tana son Don Allah ya Turamata Nombar Malika zata kirata,mirmishi kawai yayi mata yace kada ta damu in ya samu lokaci zai zo,mganar malika kuma ba sai ta kirata ba,Zai sanar ita ammh da Wuya ta samu Zuwa don bata jin dadi cikint jikinta yayi Nauyi..”Cike da Mamaki Nadira kema Malika Fatan Sauka lafiya kafin suyi sallama bayan tace agaisheta,shikuma yace ta gaida Momi,.

Ya dade Shuru bayan sungama waya,yana Tunanin wani abu,Abunda yasa bai bata Nombar Malika ba,saboda shi atunaninshi Zahra na wajen,kuma zata iya daukan Nombar Malikan ta kirata,saboda shima kwanaki tayi ta kiranshi baya dauka,daga karshe sai ta koma tana kiranshi Da Rufaffiyar Nomba,Sai da ya kulleta kana ta daina Damunshi..

Sai da yakoma gida yake sanar da Malika sakon Nadira,tayi ta mamaki harta Fadin in Saleem zai barta data jema Momi da Nadira biki suna da kirki sosai,wani kallon lalle ne ma Saleem yayima Malika dole taja bakinta tayi gum,itama din ma jnta baki ne,ammh tasan yadda Cikin jikinta yayi kato kuma Wata 6 kenan ammh kamar wanda zai Fito yau ko gobe,duk ta kumbura musamman kafafunta,Barin ma tayi dogon Zama kafin tatashi duk sai su haye,Sai Saleem ya dawo daga aikin kafin su kwanta yayi mata massges dinsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button