MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Turus kowa yayi domin Tundaga shigowarsa har mganarsa Kaf akunnan Malika,wacce Tunda taji zencensa lakkan jikinta ya saki tayimai kuri da ido tana binsa da kallon mamaki,shi da fari baima Lura da ita ba,sai da yaga anyi Shuru ana kallon  barayin datake kana ya kallah,ganinta tsaye yasa ya nufota yana Fadin”Wai ga yar cin Durin uwa”Wani irin banzan dabi”a ce haka kina amarya ammh babu wani kwalliya,sai Fito da wannan banzar Shigar,ke binta kuna me baku Shiryata,ayi amikata gidan mijinta Tunda An Daura aure kuma ai babu jira…”Yafada yana kallon Hajiya binta wacce ta jike da zufa,Shiko ko ajikinsa domin bashi da masaniyar Malika batasan Abunda ke Faruwa ba.

Kawai bai ankara ba,sai ji yayi ta chakumo kwalanshi tana Fadin”Wata malikar aka Daura ma Aure…? take Fada idanuwanta sun chanza kala sun yi jawur,dayan hannunta kuma na rike da wayarta,yadda ta ci kwalan babban rigansa sai ka rantse wani sa”an ta ne nan ko ya haifeta ya juya uwa uba kanin kakartace,wacce ta haifi mahaifinta.

Gabadaya Falon aka saka salati daidai lokacin da Daddy ya shigo yana Tambayan meke Faruwa ne yaji haniya,ai ba”a bashi amsa ba yaga Malika rike da kwalan kawu Shitu,Zaro ido yayi kafin ya kirata cikin tsawa wanda Tunda aka haifeta baitaba mata makamancin irin wannan Tsawan ba.

“Malika….!! Yafada yana Kokarin saba babbar rigarsa wacce ke kokarin zamowa saboda tashin hankali,Jin tsawan da kiran sunanta alokaci daya shiyasa ta zabura ta sakeshi tayi baya Fuskarta tayi ja,ganin Daddyta tsaye yasa ta nufeshi da gudu ta fada jikinsa lokaci daya ta fashe da wani marayan kuka tanayi tana Shessheka.

Riketa yayi jikinsa yayi sanyi ganin yadda Malika take kuka,Rumgumeta yayi yana Fadin”Why Babby….? Dagowa tayi kafin tace”Daddy plz tell me d truth,da gaske an Daura min aure yau…? plz don”t say yes Daddy nasan cewa kai Uba ne mai Adalci kuma bazaka taba yimin Abunda bani so ba”?

Tafada tana kuka Kallonta yayi kai tsaye yarasa Abunda zaije mata dakyar yace”Injiwa…? waya sanar dake wannan lbrin ba gaskiya bane…”Yafada yana riko hannunta,Fizgewa tayi tana Fadin”,Gasu  nan su suka Fada,Daddy kalli wayata kalli Abunda nagani,yana yawo mai zaka kira da hakan,kuma ma infact ma mai wannan taron jama”ar yake Nufi,nafara hango Kamshin gaskiya awannan zence,juz look Daddy ka kalli wannan Hoton ka sanar dani karya ne ba gaskiya bane…”Tafada tana haskomai hotonta dana Saleem da”aka hadashi waje daya.

Karba yayi yana kallo,gabadaya kansa ya kulle baida mafita illah sanar da ita gaskiya Dagowa yayi yana Fadin”,Comon baby taho muje ciki muyi mgana kinji…? Kallonsa tayi kafin ta ja baya tana Fadi cikin tsawa”Wlh babu inda zani sai ka sanar dani gaskiyan wannan mganar….”Tafada tana huci,Kallonta yayi kai tsaye bakinsa na Rawa yace”E…Eh…Gas…Kiyane,buh ammh bby ki tsaya ki…..”

“Ya isa…..”Tafada cikin dakamai Tsawa kamar wani tsaranta,Idanuwanta sun juye Shuru yayi yana kallonta,Wasu zafafan hawaye suka biyota,kawai sai ta nufeshi,tafara dukansa a kirji tana Fadin”Ka zalunci ne,Ka cuceni bazan taba yafemaka ba,i hate u…I hate Daddy….”Take Fada tana dukansa da alamar ta Fita da hayyacinta,kunya ne da nadama suka lullubeshi na Abunda malika takeyi riketa yake yana kiran Sunanta,ammh bata ko jinsa,illah dagewa datayi tana jifansa da duk kalmar datazo bakinta,harda cemin Azzulumi Ranshi yayi mugun baci baisan sadda ya daga hannu ya kwasheta da maruka har biyu ba, Dama da hauni,wanda sai da ta kife saboda zafin marin nan da nan bakinta ya fashe hancinta yafara habo,yana xubar da jini.

Tsaye yayi gabanta yana huci yake Fadin”Ba tun yau Nafara Nadamar sangartaki danayi ba Malika,Ammah yau na kara jadadda Nadama na,kuma na yarda Allah ne yafara nuna mim Isharata Aduniya,ina matsayin Mahaifinki,ammh kirika jifana da munanan kalamai,don kawai na aiwarta da Umarnin Allah,toh bari kiji daga yau na daina Saka rmiki kina Abunda kika ga dama,Tunda ke bakisan mutumci ba,kuma Auren anriga an Daura wlh ko zaki mutu yau nida kaina zan mika ki gidan mijinki,Allah barshi daga chan ki rataye kanki mutu karewar iskanci,Binta kamata ku Shiga da ita,ku shiryata a gaggauce nan da wani lokaci xan mikata gidan mijinta…”

yana gama Fadin haka ya wuce sama Fuu kamar zai tashi sama.saboda Fushi itako malika kasake tayi hannunta dafe da bakinta dake jini,Abunka da farar mace,nan da Fuskarta tayi jajir,ga shaidun yatsun nan sun bayyana,saboda bakin ciki da takaichi kukama ya kasa zuwa mata,kwanciya kawai tayi awajen hawaye suna kwararomata,bata ta zaton yau ita Malika malik,haka zai iya Faruwa da ita ba.

Tunda tataso wajen Daddynta banda soyayya da zallar kauna babu Abunda
yake gwadamata,bai taba saka hannu ya dake taba,kai ko Fada bai taba yimata,koda kuwa tayi ba dai dai ba,tsakaninta dashi sai lallashi da soyayyah,ammh yau na rana tsaka saboda Auren,Auren ma arasa waza”a hada ta dashi sai wani kazami kuchakin Dan sanda,kakin datafi tsana aduniya,tunda take gudanar da rayuwarta bata ta kawowa zata iya aure ta zauna karkashin wani abu,sai dai ko in ita taga kayimata,ta yarda ta aureka,randa ta gaji dakai ta sakeka,dama shirinta kenan koda Daddynta ya mtsamata tayi aure

Wani Siririn kuka take saki tana daga kwance,suko tsaye sukai suna kallonta,suna Allah wadai da ita,Hajiya binta ne ta karisa gareta tana dagota take Fadi”,Tashi tashi Malika kada ki zama wadanda Allah zaiyi Fushi dasu,ki bi umarnin mahaifinki don yana da hakki akanki,Ki biyashi shekarun daya kwashe yana gina rayuwarki da gata,baki taba neman Abu kin rasa ba,kullum Cikin Faranta miki yake baya son ganin bacin ranki,ke ko daidai da Rana daya baki taba Sashi Farinciki ba meyasa yau bazaki Sashi Farinciki ba,koda sau dayane arayuwarshi ya Tuna yau Malika tayi min Abunda nakeso batare da gaddama ba,haba Malika,don Allah bar kukan nan ki tashi,domin yanzu darajanki ta karu,igiya uku ke reto akanki,wanda bakowacce mace ke samun irin damarki ba…”Tafada tana rikota,haka ta data ita jikinta ya saki banda zubar kwallah bata komai,ga duk alamun mganganun Hajiya binta sun Shigeta,neman Faduwa suke gabadayansu saboda yadda Malika ta sakarmata Nauyinta,da Saurin wata kanwarta dake Malumfashi ta kariso zata rikota tayi saurin Matsawa alamar bata so.

Ganin haka yasa Hajiya binta ta yafito Joda da hannu suka riketa kowanne ya sagala hannunta daya bisa kafadansu,suka fara taku da ita zuwa sama,har dakinta suka kaita,Hajiya binta da kanta ta Shiga tiolet din ta hadamata Ruwan wanka,ita kuma Joda tana zaune kusa da ita tana Faman Sharemata hawaye kamar wata karamar yarinya,ammh ranta fal dariya,da sukace tashiga wanka banza dasu da tayi,sai ma saka baki datayi ta kira su merry da Dose sai gashi sun Fito da hanzari da hannu tayi musu mgana,Sai gashi sun dauketa cak sun Shiga da ita bedroom dinta.

Suna mata wanka tana kwance cikin bath din Idanunta arufe tana kuka ammh na zuciya,domin hawaye ne ke ta zubomata kamar an bude famfo,sukansu Dose sunji ba dadi,lalle Duk Abunda ya sanya Madam kuka bamai sauki bane,matar data ke jaruma isasahiya mai ji da kanta yau ita ke kuka da idonta.

Haka dai suka gama mata wankan suka Fito,da ita koda su shafeta da mayuka,tuni joda ta iso dakin dauke da wani Ubansu leshi mai kyau da yarari,kalan marun,and red,sai takalmin shi da jakarsa da wani katon mayafi red,ammh yana da santsi Kuma sharashara,yake yana da wasu duwatsu kanana masu kayyali ajiki,sai dan kunnen zinare guda daya Wanda mahaifinta yayimata domin zuwa gidan Miji dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button