MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL

MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Gyada kai yayi kafin yace”Allah ya bada nasara,ya kuma dafa maka…”Kasa amsawa yayi da Ameen,saboda nauyi da nadama,yana jin zuciyarsa na kara Rauni,kafafun  Daddy yake kallo,yana Tuna sanda yazo da kafarshi ammh yau sai gashi zaune baya iya takawa ko nan da chan,Wani imane yakara kamashi,yana Tunanin iyaye irin Daddy sun kare,wanda za’a yima yarka wannan Cin zarafin da tozarcin,ammh kuma ka hadu da wanda ya aikatama haka,kuma ka karbeshi da duka hannuwaka..? Lalle yaji kamar ya maida hannun agogo baya.

Daddy ne ya kalli Hajiya Binta yana Fadin”Binta samomai Abun shama,kinsa fa ya yo Tafiya..”Gyada kai tayi zata Fice yayi saurin cewa”A”a Daddy abarshi bana jin kishi…”Girgiza kai Daddy yayi kafin yace”A”a kar muyi haka dakai,kafa sha hanya,dole kana bukatar Ruwa,maza binta kawomai don Allah…”Da hanzari ko ta Fice,shiko saleem duk ya kasa sakin jikinsa,ballema ya dago kanshi Daddy ne ya kalleshi yakuma karanci yanayinsa mirmishi kawai yayi kafin yace”Ya ka barosu Abbanka,ya kuma su Hajiya da Umminka..? Kansa na kasa yace”Duk suna gaisheku..”Ya amsa da “Muna amsawa….”

Daga haka Shuri ya biyo baya har Hajiya ta dawo dauke da tire shake da kayan sanyi,ta jiye agabanshi kafin ta sake Ficewa,Hannunsa Daddy ya saki yana Fadin”Sha ko Ruwane Saleem ka jika makoshi…”Baiyi gaddama ya dauki roban swan mai sanyi ya Tsiyaya akofi yana sha kadan kafin ya ijiye yana sauke ajiyar zuciya,so yake yayi mgana ammh kunya da Nauyin Daddy sun hanasa wani motsi.

Gajiya yayi da sadda kai,ya dago yana kallon Daddy kafin yace”Armm Daddy dama Dalilin zuwana Abu daya ne zuwa biyu,na farko domin na baka Hakuri bisa Abunda ya faru,don Allah Daddy kada ka rikeni ka yafemin ajizanci ne na Dan Adam,da kuma sharrin Shedan sai na biyu don na sanar dakai na dade da maida Malika amtsayin matata,yanzu haka nazo neman izininka ne zan tafi da ita,muje mu zauna muyi zaman Aure na hakika..”

Har ya gama mganarsa Daddy na mirmishi kuma yana jinjina kai,Bai katseshi ba sai da ya gama kafin yace”Saleem…” ya kirasa da muryansa cikin taushi da kulawa dagowa yayi yana kallonsa Kai Daddy ya kada mai yana Fadin”Taso kazo kusa dani kaji…”Bai yi gaddama ba,yaja jiki zuwa kusa Da daddy,wanda ya kama duka hannuwanshi ya rike gam,yana kallonsa ido cikin ido kafin yace”Bantana rike ka araina ba Saleem,saima Dadin Abunda ka aikata Naji,ko banza kafara Daidaita rayuwar malika,ni kuma kasa na gane gaskiyan dana gaza ganewa shekara da shekara,Hakika zuwanka Rayuwar Malika Saleem haske ne,kuma Rahama ne,dama aikinka ne kai kafara kuma kai zaka karisa,Malika zata bika,duk inda zaka sanya kafa zata saka Domin na bar duka amanarta ahannunka ne Saleem…”Ya fada kwallah tana cikamai ido …

Gabadaya gwiwan Saleem tayi sanyi yama kasa mgana,ya bude baki zaiyi mgana kenan hajiya binta ta dawo dakin tana tambayan Saleem ko akawo mai lunch ne,girgiza mata kai yayi batare da yayi mgana ba,Daddy ne ya kalleta yana Fadin”Binta taimakeni ki kiramun Bby,ki kuma umarci yan aikinta da su hadamata duka Abunda zata bukata acikin akwatunata,,ga mijinta nan zai wuce da ita yanzu…”Yafada daidai sanda kwallar dayake rikewa ta zubomai,Hajiya binta bata ce komai ba ta juya tafita,Shiko saleem yana ganin sanda hawayen Daddy ke diga bisa hannunshi,ammh yakasa kwakwaran motsi saboda kalmar nan da Daddy ya Furta na yabashi duka AMANARTA…”

Hajiya Binta zaune ta iske Malika tana cin abinci tashinta daga barci kenan,sakon Daddynta ta sanar da ita,bata bar dakin ba har sai da malika ta mike sanye da doguwar riga baka na kamfanin Armani,wanda bakin Siririn gyalen dake kanta ta sakaloshi zuwa wuyanta,kallo daya zakamata ka Fahimci tana da shigar karamin ciki,kodon ganin yadda tayi wani danya sharaf da ita,sai da ta Fice zuwa Falon na Daddy kafin Hajiya Binta ta Umarci su Dose da su hadama Malika duka kayanta na anfani cikin manyan akwatunanta,amsa mata sukayi da toh kafin su Shiga ciki su fara hada mata kayan.

Bata da masaniyar zuwan saleem,domin Tun safe tana daki bata Fito ba,shiyasa kanta tsaye ta shiga falon ko sallama batayi ba,don ba halin malika bane shiga waje da sallama,Bata lurama da Saleem dake durkushe gaban Daddy ba,wanda duka hannuwanshi ke hannu Daddyn kamar mai rokon wani Abu.

Tana zuwa ta duka ta bashi peck agoshi tana Fadin”Dadylove ya jikin ka..? Hajiya tace kana kirana hop dai ba wata damuwa ko..? Tafada tana kokarin dukawa kusa dashi,sai ji tayi cinyarta ya gogi Gwiwan kafar wani azabure ta kalli inda taji Abun yatabata,shima daidai lokacin ya dago suka ko Hada Four eyes dashi.

Dam!Dam!Dam! gaban malika ya buga bayan ya amsa lokaci daya,ko mutuwa tayi ta dawo bazata taba mantawa da wannan muguwar Fuskar ba,wacce bata cike da komai sai mugunta da zalunci uwa uba rashin imani,Ai sai ga Malika saboda tsoro da razana tayi baya zata Fadi Allah ya taimaketa ta rike karfen keken Daddy,ta zauni da duwawunta dabas akasa,ko”ina na jikinta babu inda baya rawa kafin kace me ta kamkame jikinta hawaye ya Shiga wanke mata fuska,Shiko saleem kallo daya yayi mata bai kara,don in ya cigaba da kallon Fuskar shegiya zai iya tashi ya zubamata marunka da zatayi hawaye mai dalili gaban Ubanta,kauda kai yayi yana jan Allah isa Aransa,sai daga bayama yake Tunanin me ma yasa ya dawo kasar? kai gaskiya Abbi bai mai Adalci ba.

Daddy daya lura da yanayin malika Sai ya saki hannun Saleem guda daya ya mika mata yana Fadin”Taho Babby,mijinki ne yazo tafiya dake…”wani yam! taji lokaci daya kanta ya sara da karfi Dafe kirji Tayi kafin tace”No Daddy…..No…”,Take Fada tana sharan kwallah gwanin ban tsausayi

Girgiza mata kai yayi kafin yace”A”a Babby karki ce haka,plz come closer kinji…”Yake Fada yana mikamata hannu,shiko saleem aransa addu”a yake Allah yasa kartace zata bishi,ammh sai addu”arsa bata karbu ba,jikinta na rawa ta matso ga Daddy kafin ta damkamishi hannunta kwara daya hada hannunta yayi dana Saleem waje daya ya damke,dukkansu sai da sukaji wani Shock yajasu,tare dukkansu suka saki ajiyar zuciya suna Runtse ido.

Daddy ya kalli Saleem yana Fadin”Saleem ga Malika nan,Na damka amanarta da amanar rayuwarta a hannunka na har abada,kai ne, uwarta kai ne ubanta yanzu,Saleem ina da kyakyawan Shaida akanka,don Allah kada ka bani kunya kayimin alfarman tsayawa tsayin daka wajen kula da tarbiyan Malika,ka koyar da ita ko kadan ne daga cikin Abunda ka sani,kazamo wa gareta,ka zamo mata kani,bayan kazama mata shafin wani kawa ko aboki, Don Allah don darajar iyayenka kada kabar rayuwar Malika ta sake lalacewa akaro na biyu,bata da wani gata anan Duniya yanzu sai kai,ni yanzu tawa ta kare,ba lalle bane na sake daura wasu shekarun araye …”Ya fada kuka ya kwace mai,Wani kuka ne yazoma ma Malika da karfin gaske ta fada jikin Daddy tana saka kanta bisa cinyarsa tana gunjin kuka take Fadin

“plz Daddy Don’t let me go…”plz….”Take Fada tana kuka mai cinrai,hannayensu ya saki kafin ya kama kan,Malika yana tashafawa alamar lallashi muryansa cikin karaya yake Fadin”Am srry Babby kidaina kuka kinji ko,ko bani na tabbata saleem,da mahaifansa baza su barki kiyi kukan maraici ba,Ki bishi sau da kafa,kiyimai biyayyah,ki kuma guji Abunda bayaso,Don Allah Malika kibi mijinki Duk Abunda yace kiyi kiyishi matukar bai sabama shari”a ba kinji ko..”Gyada mai kai takeyi tana kuka kamar zata Shide shima hawayen yake.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button