MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Abbi dake zama bisa daya daga kujerun falon,yake fadin”Tunda har shi yagama ba”a koreshi ba kema haka zaki gama insha Allahu..”Dariya takama saleem yadan dara yana kallon Saleema yana mata gwalo,Ummi ce ta kariso wajen ita da Malika wacce ke satan kallon Saleem,shiko ko barayin datake bai kallah ba.
Sannu da zuwa Ummi tayima Abbi kafin Malika ta duka tana gaisheshi,cike da kulawa Abbi ya kalleta yana fadin”Malika,ya jikin ki? ya bakunta,hop dai babu wata damuwa ko?Girgiza kai tayi kanta na batace komai ba,Abbi yace”Toh masha Allahu,Allah kara lafiya,komai dai kike bukata,ki sanar da Umminku gatanan kinji ko”Wannan karon ne ta bude baki tana Fadin”,Tom Abbi nagde sosai..”
Mikewa Abbi yayi yana tafiya zuwa sama yake cema Ummi “Wai ina hajiya banji duriyanta ba..? Saleema tayi karaf tace”Hajiya yau fa adame take,sai Fada take da mutane,hardani yau ban tsira ba..”Karamin tsaki Saleem yaja yana fadin”Wa.? ai wannan hajiyar ta Abbi ko ba”a mata komai kullim cikin Fada take,ita ko gajiya batayi.”Abbi yawuce kawai baice komai ba saima mirmish dayakeyi.,Ummi tabi bayanshi tana ma su Saleem dariya da Fadin”Ku shiga hankalinku,wlh in tajiku yau ko Sarkin kumo bai isa ya kwace ku ba..”
Falon ya rage daga Saleema sai Saleem da Malika,wacce ke gefe zaune arakube kanta duke,hanyar dakinsa yabi Saleem ta kirashi tana fadin”Ya saleem..”Waigowa yayi yana Fadin”Miye..? Yamutsa fuska Tayi tana kallon barayin da Malika take tana fadin”Ashe kuma Abbi ya matsa maka sai da kadawo da wannan watsatsiyan yarinyar gaskiya ban…”Kallon da Saleem ke watsamatane yasa tayi Shuru ta bakinta tana binshi da kallon mamaki
Ransa kawai yaji ya baci da Saleema tacema Malika watsatsiya,ko banza shine shaidan Malika,domin shi ya fara saninta abudurwa,ko bakomai zai kareta saboda martabanta,barayin malika ya kallah,suka ko hada ido,idanuwnta cike da kwallah har suka zubo,tayi saurin sadda kanta kasa tana share kwallah,sai yaji zuciyarsa batayi dadi ba sam,.
Hade rai yayi yana kallon Saleema yace”inji uban wa yace miki matata watsatsiya ce? Saleema wai yaushema kika rainani,am your mate dazaki tareni da wannan banzar mganar..? Ya fada yana kafeta da rikatattun idanuwanshi,Tura baki tayi tana fadin”Daga mgana sai cibi yazama kari..”Tafada tana juyawa zata koma daki,cike da Fushi yace”Saleema…!..
Ya kirata da karfi,cak ta tsaya kafin ta waigo tana kallonshi Hannunsa ya tura ciikin aljihun wandonsa yana Fadin”Maza go and tell her srry,yanzunan if kuma..? Yafada yana Kuramata ido,Saleema tayi tsuru tana raba ido,tanajin aranta wannan ai reni ne,ganin tana turamai baki ne yasa yafara takawa zuwa gareta yana fadin”Wlh in baki bata hakuri ba, sai na ci ubanki yanzu nan na tatttakaki awajen nan,kuma na hadaki da Abbi,stupit gal kawai..”,Wani kunya Saleema taji da takaichi kamar tayi kwallah,jan kafanta tayi zuwa gaban malika tana fadin”Srry…”Kanta gefe tafada,Malika dake duke ta dago tana mirmishin yake,tace”Bakomai..”Tafada tana jin kamar ta rushe da kuka.
Wani banzan kallon ya watsama Saleema yana fadin”Get away from here,and dis is d last zaki kalleta ki cimata zarafi in kuma baki ji ba,try me and see..”Yafada yana kada mata hannu,kuka yazoma Saleema ta kwasa da gudu zuwa daki tana kuka tsaki yaja yana Fadin”Munafuka kawai..Yafada yana juyawa zuwa dakinsa ransa amatukar bace.
Bayansa malika tabi da kallo tana jin wani iri aranta,Akwana biyun da sukayi tare,in tace bata shaku dashi ba toh tayi katuwar karya haka kurum takejin sha’awar kallonsa,sannan muryansa tana jefata cikin wani yanayi wanda takasa fassarashi.
Tashi tayi tabi bayanshi zuwa cikin dakin,sai ta iskeshi yana Kokarin tada sallar isha”i,batayi sanya ba ta Fada tiolet ta dauro alwala tazo da hanzari tabi bayanshi yajasu sallar,suna idarwa tace mai zata biya karatunta,bai musa mata ba,tabiya shi ko tar babu gardama,Karamata da sura biyu yayi zuwa gobe,tunda yaga karatun nata yana sauri sosai,Ummi ce ta kirashi awaya tace su Fito Falo suyi Dinner,bai sanar da ita ba illah Ficewa da yayi yana Fadin”Ki zo Ummi na kira..”
Hijabinta ta dauka,wanda tazo dashi don dai bata da wani,Koda ta fito duka iyalan gidan sun hallara bisa katon tibirin cin abinci,hajiya babba ce kadai bata awajen,may yau bata ra”ayin ci tare dasu ne,don yau kam hajiya tsiya takeji,Saleema na kusa da Ummi,inda Abbi ke gefenta sai Saleem dake gefen Saleema,Jikinta asanyaye ta karisa tunkafin taja kujera Ummi tace”,Saleema gyarama Antynki inda zata zauna..”
Wani takaichi ne ya kule dama bata Wuce da Abun da ya saleem yayi mata,Shiko yana cin abincinsa ko kallonta ma baiyi ba,balle ya lura datana jin haushinsa,Dkyar taja mata kujeran tana sakin wani Siririn tsaki,Zama malika tayi tana dan mirmishi kadan,Ummi dakanta tayi sarving dinta Tuwon Shinkafa ne miyar agun,wanda yaji manshanu da naman kan rago,Tun kafin ta fara ci taji miyanta ya tsinke,cikin Son cin tuwo taja cokali tafara ci,itako saleema na gefe tana Faman zabgamata harara,wanda data dago ido,Zata ganta tana mata wani kallo,sai dai ta maida kanta kasa kawai idanuwanta su ciko da hawaye,saboda ita bata saba da wannan rayuwar ba.
Saleem yana gama cin abinci ya yagi tissue ya goge baki yana Fadin”Abbi gobe fa zan koma bakin aikina..”Abbi yana cin abinci ya ijiye yana Fadin”Masha Allah,har kun gama mana bakunci zaku tafi? Toh Allah kaimu..”Jin Abunda Abbi yace ne yasa yace”A”a Abbi nikadai zan koma,ai Ita tana nan tare daku..”
Zuramai ido Abbi yayi yana Fadin”Miye dalili..? Kai tsaye yace”Toh Abbi nake ga kamar hakan shine daidai..”Ajiyar zuciya Abbi yayi kafin yace”Ko daya sai dai kace kai hakan ka tsara,toh don mai garinku in katafi ka barta anan wajen wa zaka kabarta..?”Wani miyan takaichi Saleem ya hadiye yana Fadin”Tare daku mana Abbi,kofa na koma kasani ba zama nake ba,toh sai naga data rinka zama ita kadai gwara na barta nan ko banza zata dinga ganin mutane..”
Mirmishin su na manya Abbi yayi kafin yace”Ra”ayinka kenan Saleem,ammh ba gaskiya bane duk uzurin daka bayar bamasu mihimmaci bane mallam,ka dauki matarka kawuce wajen aikin ka da ita,kana da muhallin bawai baka dashi bane,….”,Saleem yayi jagale yana jin wani takaichi kamar ya fasa ihu,
ya bude baki zaiyi mganan kenan Abbi ya dakatar dashi da cewa”Kul..Karka kara cewa komai,ka dauki matarka ku tafi,fakat umarni ne ba shawara ba..”,Yana gama fadin haka ya mike ya haye sama,Malika dake zaune jikinta duk yayi sanyi ganin yadda Saleem din yayi,ada in akace tabishi bazata ba,ammh ayanzu batason ya barta anan,saboda shine gatanta duniya da lahira kuma bazata so ya barta da saleema ba,don sai ta zaneta saboda yadda take wurgamata wani banzan kallo
Ummi ce tace”Ai kaji Abunda Abbinku yace ko? bai samu zarafin mgana ba ya daga mata kai,maida kallonta tayi kan Malika tana fadin”Dota kina so kibishi..? dagowa tayi tana kallon Ummi,kafin ta maida kallonta kan Saleem wanda ya kafeta da ido yana kallonta cikin wani yana so yaji mezata ce,itako wani yanayi taji yana shiganta saboda yadda ya tsareta da manyan idanuwansa masu dauke da wasu surrika
kanta ta dukar kafin ta gyadama Ummi kai,washe baki tayi tana Fadin”Masha Allah,tashi to kije ki Shirya kayanki,Da safe zaku wuce ko Saleem? Gyada mata kai yayi,yana mikewa bai kai da gama tashi ba Saleema ta ture kujera tana sakin wani wawan tsaki takama hanyar dakinta tana kunkuni,dukkansu da kallon suka bita na mamaki,Saleem ne kadai da malika su ka san dalilinta na yin gaba,Ummi ko ta dauka ko wani ne ya bata mata rai.