MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Ranar da”akayi sadakar ukune sai ga Maman Abba ita da megidanta sun zoma Malika da Saleem gaisuwa,Zahrin gaskiya Malika taji dadi sosai haka ta Rumgume Maman Abba tana Fadin”Maman Abba kinga yadda Rayuwata tadawo ko? Babu uwa,uban dani ke kallo amtsayin madubina shima yatafi ya barni..”Take Fada tana kuka,bayanta Maman Abba ta shiga bugawa tana Fadin”Kina da wani Madubin Malika,mijinki shima bangon kine,ina mai tabbatar miki Allah bazai dauke Daddy kuma yahanaki soyayyar Saleem da kulawanshi ba,sai dai ya daukeshi don gwada imaninki,kiyi tawakalli sai kiga Allah ya Dubeki da idon Rahama ya haska rayuwarki,wanda Daddy na cikin kabari Allah zai nuna mishi ke,kuma yayi alfahari dake..”Kalaman Maman Abba ya sanyayama malika rai har sai da ta murmusa tana digan hawaye,sake Rumgume juna sukayi tana kara lallashinsa.
Joda dake gefe kuwa sai tayi mamaki ganin yadda Malika ta saki jikinta da Maman Abba,wacce ke ta bata baki tare da wasu shawarwari,Itako Malika sai gyada kai take tana nuna alamun gamsuwa,sai yammah sukayi Shirin tafiya,Har waje Malika ta rako Maman Abba tana mata godiya,wanda ganinta haka bakaramin Dadi Saleem yaji ba,kura mata ido yayi yana kallonta,Itako kallo daya tayimai ta kauda kai tana Jin kunya ganin Abokinshi Sadiq na wajen ga sauran Manyan mutane irinsu Abbi.
Suna sallama da Maman Abba,shiko Saleem shida Sadiq suna musabaha da Baban Abban,ammh kacokan hakalin Saleem naga Malika ganin yadda kawai yaga ta wani rame,kodon bai kara ganinta cikin rana bane,? Sadiq ne ya lura da kallon da yake mata,shima ya kalleta aranshi yana yaba kyanta ba karya,har motar su Maman Abbah ta Fice daga gidan bata koma ciki ba ita da Joda,Ganin haka yasa Sadiq ya zunguri Saleem yana Fadin”Haba Acp wannan dogon kallon ai ya wuce na Shari”a..”?
Wani banzan kallo ya jefamai kafin ya cigaba da kallon Malika so yake su hada ido ita kuma tana lura dashi sai taki yarda,dariya Sadiq ya Sheke dashi kafin yace”Kuma gaskiya Ba laifi Matar naka akwai kyau,gata jinin Turawa ko banza zakuyita haihuwan Jajayen Fata kyakyawa..”Saleem bai san Dalili ba,kawai yaji mganar Sadiq ta cakanmai rai sosa,wani takaichi ya kumeshi,Kirne Fuska yayi kafin ya fara takawa zuwa kusa da malika wacce ke Shirin juyawa zata koma gida,bai ce mata kala ba,ammh yana biye dasu har suka Shiga Falon gidan,wanda joda ta dingama Malika radan ga Saleem nan na binsu abaya,bata juyo ba,ammh ita kadai tana Sakin mirmishi domin da babu Saleem arayuwarta wannan Rashin ya faru,kila itama da yanzu tana kwance,shiyasa akowani lokaci take jinjina ga gwarzon maza Wato Saleem domin ya zama zakara ne acikin zaratan maza.
Sai da yaga sun Shige kana ya dawo wajen Sadiq yana kallonshi duka hannunwanshi cikin aljihunsa yake Fadin”,Dazu kace ina kallonta? matarka na kallah ko matata? kuma dakake yaba kyanta uban wa yakai idonka Akan matata? plz mallam wlh karka kara,In so kake ka yaba kyan mace sai kayi aure kaga sai ka yaba naka…”Daga haka yayi Wucewarsa zuwa Rumfar dayake zaune,shiko Sadiq baki ya rike yana Fadin”Au abun harda gori,toh muna kwana nawane inda rai da rabo.
Washegari sai ga Baban Zahra yazo gaisuwa wato tsohon Alkalin alkalai na kasa gabadaya,Zahirin gaskiya Saleem yaji dadi sosai wanda har cikin gida ya shiga dashi yayi ma hajiya da Malika gaisuwa,bai jima ba ya Tafi,bayan tafiyan ne Sadiq da Abbu suma suka dau hanyar Abuja bayan ya Shiga har ciki an kiramai Hajiya Binta da malika yayi ta musu Nasihan mai ratsa jiki,wanda ta Shigesu,haka suke hawaye kawai don yadda zukata suka raunana babu wani abunda baki ya isa ya Furta,gashi tun yau hudu da rasuwar Daddy mutane duk sun fara watsewa za”a barsu su kadai Abun yazo ya rafkesu.
Sun tafi ba Dadewa Saleem ya nemi gnin Malika,ganin da Jama”a sosai a baban Falon gidan nasu gashi ita kuma tana sama ne,ita da joda,sai Yan alqawarin nata mery da Dose,Umartan Joda tayi data bude mata wani falo dake ta waje ya shigo,aiko haka akayi Joda ta bude Kofar Falon Saleem ya Shigo sai ga Malika ta Shigo da cikinta gaba,tana sanye da wata doguwar riga mai Tsukakken hannun kamar roba.
Batama kariso ba ya isa gareta ya riko hannunta suka zauna bisa daya daga cikin kujerin Falon,kura mata ido yayi ita kuma kanta na kasa,ajiyar zuciya ya sauke kafin yace”Ya hakurinmu..? fata dai kinci abinci baki zauna da yunwa ba..? Kai ta gyada mai kafin tace”Hakuri mungode Allah..’Tafada idonta na cikowa da kwallah,Baki ya sake kafin ya dafa duka kafadunta da hanuwanshi biyu yana Fadin”Toh kuma miye Abun kuka? ashe bakijin mgana na,har saunawa zan fadamiki kuka bashine zai dawo da Daddy ba,yatafi kenan sai dai mu tayashi da addu”a Allah yasa chan yafiye masa nan..”Hawayen datake rikewa suka zubomata ta sanya hannu ta share tana Fadin”Na bari insha Allahu..’Tafada cikin wani yanayi.
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace”Dama na nemi ganinki ne,saboda ina so na Wuce zamfara yanzu,shine nake so na tambayeki ranar bakwai zaki koma gida,ko kuwa sai kin kara wani satin..? Dagowa tayi tana kallonshi cikin Rauni tace”Yau kuma..? gyada mata kai yayi kafin yace”Eh Tun jiyama naso tafiya,so rashin Tafiyar su Abbi ajin ne shi yadakatar dani,.”Jikinta ne yayi sanyi kwal kwal da ido tana so tayi kwallah,bata fuska yayi kafin ya nunata da yatsa”Karki kuskura hawayen nan su zoba..,Haba don Allah ya kikeso nayi da raina ne,Kullm kuka kullum kuka,Ehe ko kin taba tambayanta yadda kukanki ke kona kin rai ehe..? Yafada yana sakarmata manyan idanuwanshi.
Rudewa tayi ganin yadda bacin ranshi ya Fito sarari,Kukan take son hana kanta sai kawai ta fada jikinsa da karfi tana tura kanta cikin Faffadan kirjinsa,tana hana kanta kukan dayakeson kwacemata, Riketa yayi saboda tabashi haushi,ammh jin yadda take kara kamkameshi ne yasa ya tabbatar da hakuri take bashi,hannuwansa yasa duka biyun ya Rumgumota yana Sakin ajiyar zuciya yake Fadin”Toh wai miye na kuka daga nace zan Tafi yanzu? kodai baki san na tafi ne..?
Dagowa tayi ta daga ga mai tana kokarin maida hawayenta,Zuru yayi mata da ido kafin yace”Meyasa baki san na tafi,alhalin kinsan cewa zan koma bakin aiki..”Rau rau takara yi kafin tace”Kabari sai gobe ka tafi don Allah..!Ina son kasancewa tare dakai..”Tafada tana maida kanta jikin kirjinsa Rumgumeta yayi yana sakin wani munafikin mirmishi,Shafa bayanta yake yakasa mgana Lokaci daya ya dago kanta yana kallon kwayan idonta,Kasa juran kallon tayi sai ta hau lumshe ido tana kokarin maida kanta kirjinsa,Bai bata dama ba,sai ma Lebenshi dayakai kan lebenta yana tsotsa cikin wani salo,bata mai gaddama ba,sai ma kara rikeshi datayi tamikamai Harshenta ya kama yana tsotsa cike da kwarewa, kan cinyarsa ya maidata,shikuma ya cigaba da kissing dinta yana Shafa ko’ina ajikinta musassaman cikinta zuwa kasan mararta,Tuni ta Birkicemai lokaci daya itama take maida mai martani tana shafa kanshi zuwa bayanshi hannayenta na kara kaina bisa kirjinsa tana shafa kan Nipples dinshi,Shan yaji Saleem yafarayi saboda jin wani abu na zirgamai,Lafe mata yayi ajiki yana maida Numfashi,hannayeta ya rike cikin wani yanayi yake Fadin”Bari kina tadamin da hankali..”Yafada yana kamkameta cikin wani yanayi.