MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL
MALIKA MALIK COMPLETE HAUSA NOVEL BY Janafty

Dakyar ta bari yashiga yayi wanka ya Fito bayan ya dauro alwala yazo yayi sallar issha’in data Subucemai,Shafa’i da Wuturin daya sabayi yau baiyi ba saboda nacin Zahra kawai biyemata yayi saboda sun kwana biyu basu wayar dare ba,koda Ranar ma sama sama suke mganar,Hira suke tasha tana bashi lbrin irin tanada tanadan datayima bikinsu wanda takejin kamar tajawo ranar biki zuwa gobe saboda Zumudi,Shi ko zumudin bayayi ammh ita datake budurwa rawan kafanta yayi yawa Shi har mamakinta yakeyi,tunda yake baitaba ganin Amarya mai Shigen rawan kafa ba irin Zahra,wanda halittace domin da zata bari data bari Tunda Momi na mata Fada,hakama Nadira wani lokacin kamar ta maketa takeji in tayi wani abun,shiyasa basa shiri da Yaya Nadir,saboda yadda bata komai cikin natsuwa..’lalle zahra kin samu mtsala????
Bata barshi ba sai wajen 12 koda ya Fito Falo Tun har sun kashe komai na kayan Wuta sun Shige daki sun kwanta,bai shiga dakin ba ya dawo dakin yayi Shirin barci ya kwanta cike da Tunanin yadda zai Tunkari Malika da zencen kara aurenshi,bayaso yakara tadamata da hankali kan wanda take ciki,bata gama warwarewa,ammh ya yanke shawaran zai sanar da ita,ammh zuwa gaba kan lokaci ta dan saki ranta.
Washegari Da Saleem zai Fita office,Joda tayi mai mganar Cefane,hakika Saleem yaji dadi ko bakomai yanzu Duniya andaina kiwon Dabba kamar da,yanzu duniya cike take da masu saka ido,yanzu haka Allah kadai yasan mutanen da sukayi zundenshi na Siyan abincin dayake Tafe yi kullum ba ranar banza,Musamman yan wajen aikinsu yasan baza”a rasa masu dogon baki ba????.
Har afuska ya Nuna ma Joda jin dadinsa akwai yana Fita ba dadewa sai ga Sargent musa ya Kawo kayan Cefena niki niki,Joda ta karba ta kai kichen ta sanya komai cikin muhallinshi,da ta bude store din kichen din wanda ke shake da kayan abinci kala kala Nau’i Nau’i,nan da nan Joda ta zage damtse tana hada hadar Dora,girki ita kuma Malika tana daki yau ko Falo bata Fito yan mulkin sun motsa,shiyasa ko Saleem daya Shigo dubata da safe barci karya tayimai,har ya fice basu gaisa ba sai da ya Fita kana ta bude ido,tana bin bayanshi da kallo cike da Soyayyarsa mai Cike da muradi da sadaukarwa.
Sai da Maman Abba ta Shigo kana Malika ta Fito da katon cikinta suka gaisa tana mata sannu,Joda ma dake kichen ta Fito suka gaisa kafin takoma ta cigaba da aikinta don Malika tace tayi mata Tuwon Shinkafa miyar Ganye,Maman Abba taji dadin ganin yadda Malika ta chanza ta cire damuwar komai acikin ranta,har ta nuna mata ta hanyar Furta mata,daga karshe tabata Shawaran ta rinka zuwa kichen din duk da haka tana kallon Abunda Joda keyi tana koya da haka zata sha mamakin abunda zata Tsinta kafin Allah ya sauketa lafiya,Malika taji dadin haka tace daman zaman kadaichi ya isheta in Joda ta Shige kichen ta barta ita kadai,gashi ita kallo bai dameta ba.
Sai da Joda tagama Tuwon nan Maman Abba taci kuma tatafi dashi saboda yadda Tuwon yayi mata dadi,Malika ko taci taci takara kamar cikinta zai Fashe,wanda ya ragu Joda ta ijema Saleem,malika ta dauke tace shi zataci da daddare,dole Joda ta girkama Saleem farar Shinkafa da miyat kaji,Koda ya dawo Joda ta gabatar da abinci bakinshi ya kasa rufuwa nan Falon ya zauna dirshan yana cin abinci,ammh sai yaga Malika nacin Tuwo daya tambayi Joda ina Amanarshi ta samu Tuwo,nan take sanar dashi ita tayi dazu kuma yar Rigimar nasa ta dauke tace shi zata ci kafin ta kwanta.
Kura ma malika ido yayi yana kallonta tana cin Tuwonta cike da Sanyinta yadda ta saba,mirmishi kawai yayi yana Fadin’,Tunda itace zataci toh nayi mata afuwa,ammh da wani ne yau Allah bazan barmai ba..”Yafada yana Hade giransa waje daya Dariya joda ta dinga musu tana Fadin”Kunfi kusa aie..In ma zaka karbi kayanka ne babu Ruwan Joda aciki..”Yana cin abinsa bai sake mgana ba,saboda yaga yau din Mulkin Malikar ya motsa ne,ganin haka yasa joda ta Shige daki ta barsu anan.
Shima yana kammallah jin abincin da kanshi ya kwashe kololin zuwa kichen ya wanke hannayenshi ya dawo Falon yana kallon Malika tana wani yamutsa baki,gabanta ya karisa yana kallonta kafin yace”Ya..? kin koshi ne..? Kai ta gyada mai akarkace,Filet din Tuwon ya dauke ya nufi kichen dashi da sauri tace”Don Allah asamin a fridge gobe zan karya dashi..”bai juyo ba,kuma bai yi mgana ba ya Shiga kichen din yasanya mata shi cikin Fridge din ya Fito.
Yana zuwa gabanta baiyi wata wata taji ya daga cak,ya sakata cikin kirjinsa da ita,kuri tayi mai da ido tana binshi da kallo ganin hanyar dakinshi ya dosa da ita,shiyasa tace”Ban wanke hannu ba Mallam..”Bai mata mgana ba sai da ya direta bisa gadonshi kafin ya durkusa kusa da ita ya Dauki hannun damanta wanda taci tuwon dashi ya saka abakinshi yara lasheshi daya bayan daya,sai da ya sule hannun tas,yana yi yana kallon kwayan idanuwanta,Lumshe ido take tana jin wani yanayi yana Shiga jikinta.
Sai da yagama lashe hannun kafin ya mike yana kallonta yace”Daga yau kinga makwancinki nan,ke ko kunyar Joda bakiyi ga dakin mijinki ammh kina kwana da wata katuwar mace..”Yafada yana Shafa gemunsa daya Tsirowa na rashin kunya????,Ware ido tayi tana kallonshi kafin ma ta samu zarafin mgana ya Fada tiolet yayi wanka ya wanke baki kafin ya dauro alwala koda ya Fito jikinsa babu riga,sai dogon wandonshi Jikinsa gabadaya yana digan Ruwa,jallabiyansa ya sanya ya shimfida sallaya ya tada sallar Shafa’i da Wututri yayi kafin ya rufe a addu’o,insa,Koda ya idar da Sallan Malika ta dade da yi barci,shiyasa yana tashi ya dauketa yakaita tsakiyar gadon ya gyara mata kwanciya,shima cire jallabiyan yayi da dogon wandon jikinsa,Ya bar kanshi daga shi sai gajeron wando ya Kwanta kusa da Malika ya Rumgumota kam,yana sakin ajiyar Zuciya,itama cikin barci ta zagaye hannayenta bisa cikinsa ta rikeshi gam,Blanket ya Rufa musu yana shafa maran Malika zuwa saman Tulelen cikinsa haka kurum yakejin Nishadi na Shigansa,yana jin wayarsa na Dukan neman agaji ammh ya share don yasan zahra ce,shi haushin datake bashi ta manta yana da mata ne? ammh sai ta dinga kiranshi duk sanda taga dama,Tsaki yaja aransa yana Fadin dole ya tashi tsaye don ya lura sam zahra bata da adalci.
Kwanaki suna ta gangarawa ayayinda muketa cinye kwanakinmu Aduniya,Ahaka ne har gashi auren Zahra da Saleem yana ta matsowa har yarage saura 4weeks ta kowani bangare anata Shirye shirye musamman ma bangaren uwar gayyah zahra,tun akwanakin da suka rage tafara banke banken mganugunar mata kamar hauka,wannan kuma shawarar Nadira ce itace kan gaba wajen amsomata tana duramata ammh basu bar momi tagani ba don susan zasu ci ubansu.
Ta bangaren Saleem ko baya wani Shirye Shirye domin ayanzu yafi jin dadin rayuwarsa Fiye data kullum,Domin shakuwa mai cike da salon soyayya ta shiga tsakanin Malika da Saleem,wanda shi Saleem din bai Fahimci haka ba,Sakamakon zuwan Joda shi yakara musu kusanci da juna,shine sanadin kwanansu waje daya wanda yayi sanadiyar kara musu Shakuwa da kusantan Juna.
Duk da halin da malika ke ciki da zarar Saleem ya nemeta bata iya mai gaddama zata bashi dukkan Hadin kai da zai samu natsuwa,shikuma yana son binta ahankali saboda cikin jikinta ammh kuma zumarta ne ke janshi wanda indai zata kwana cikin jikinsa bai ya kauda ido akanta sai ya lalubeta ko kadan ne,ita kuma bata iyamai gaddama,domin yakoya mata jarabanshi bata iya hakuri dashi indai yana nan tana kakume dashi.