UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL
UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF
_Alhamdulillahi Rabbil Alamin....Godiya ta tabbata ga ALLAH Subuhanahu wata"ala wanda da ikonshi ne komai ke faruwa,...Aminci tare da Rahama da gafara su tabbata ga shugaban fiyayyen Halitta Annabinmu MUHAMMED (SAW),tsira da Aminci sukara tabbata garesa shida Alayansa da sahabbansa gabadaya_
GARGADI:LABARINA (FICTION STORY) NE NAYISHINE DOMIN FADAKARWA,DA NISHADANTARWA DUK WANDA YAGA WANI ABU WANDA YAYI DAIDAI DANA SUNA,KO HALLAYA,KO NA GARI,TO DUK ANSANE DOMIN KAWATA LBRI..AGUJI JUYAMIN LBRI KO SATAR FASAHA,KUMA ALLAH YA ISA GA DUK WANDA YAKARA SIYARMIN DAWANI BANGARE NA LBRINA,..KAMAR YADDA YA FARU A NAZIR..✌
Hohoho chai chai Janaf freeking fans…Nasan zakuyi suprise saboda gobene..promise dina daku..,But my Sahiba HAFSART HAFNAN..Itace tace Nabaku update yau sunday 7/7/2019..Saboda yadda take kaunarku so duk wanda yaci karo da wannan page din juz yayi mirmishi bayan ya shekamata albarka lols
KARAMCINKI NE SILA…FEEDHOM❤Hakika karamcinki ne sila,Mutumcinki ne sila,Martabanku ne sila,Karramawanku ne sila..Dattakon ki ne sila tare Karamcinki gareni yake ma”abociya Fara”a da Annushuwa..,INA ROKON ALLAH DUK INDA KIKA SANYA KAFA ALLAH YA CIGABA DA DAFA MIKI…YAYIMA RAYUWARKI ALBARKA DAKE DA ZURU”ARKI….Janaf tana Matukar girmamanki..Zuciyata haryau takasa mantawa da alherinki gareni Allah yabiyaki da aljannah mafi soyuwa FIRDAUSI????
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
NO:1
ABUJA
MAITAMA DISTRICT
“”””Saukowa take daga step cikin Takun isa,sanye Take da riga da zani na Atamfa super wax..,Tasanya wani katon lifaya tayane dukkan jikinta dashi harzuwa kanta hannunta da wuyanta sanye da zinare suna kyalli kallo daya zakamata ka fahimci balarabiyace ta usili,doguwar mace ce wanda kudi da hutawa suka maida ita
yar Dumaduma,fuskarta mai dauke da doguwar fuskar da dogon hancinta har baka..,Gashin idanunta zarazarane kamar tayi kari dan bakinta karami dashi..Gashin kanta kuwa har gadon bayanta yake… HAJIYA SUHAIMA KENAN..Hakimar mace ce Kyakyawa kin kowa kin wanda yarasa akallah zata bama shekaru 50 baya ammh bazaka taba cewa tayi wannan shekarun ba domin kana kallonta zaka hango zallah kurciyanta saboda yadda yanayin jikinta yake da kuma Shikanshi Gishirin kyan bai Tafi ba
Cigaba da saukowa tayi kafarta cikin wani flat din,shoe mai kyau da tsari saukowa tayi ta bayyana cikin wani katon falo wanda yake zagaye da Royal chairs hadaddu masu garari dakyawu,golden colour sai wani katon Plasma wanda yacinye Rabin falon in kana kallo kamar agun ake gudanar da komai falon gabadaya agyare yake komai tsaf sai tashin kamshin Turaren wuta yake.
Kan Daya Daga cikin kujerun Falon ta yada zango bayan ta kinshigida da kujera tana duban agogo wanda yake wani makeke daga yammah acikin bango wanda shima yamamaye Rabin bangon daidai daya buga karfe 9:00pm nadare..,Tsaki taja bayan tadan mike cikin kasala ta Furta..”Karime..Da dan karfi dagachan bangaren naji an amsa da Na”am hajiya..Kafin wacce aka kira da karime ta bayyana Afalon.
Cikin Rawan jiki wata yar dattijuwa ta durkushe gaban matan tana Fadin”Barka da Fitowa hajiya..”Yamutsa fuska tayi kan tace cikin Hausan ta data chakule da Larabci”Ki shiga bedroom dina ki daukomin Phone dina”Tafada tana yarfa hannu”Cikin Rawan jiki Karime ta mike tana Fadin”Angama hajiya”Tafada tana Hawa step din.
Cikin lokaci kadan karime Tadawo falon hannunta rike da wata faskekiyan wayan mai kyau da tsari wacce ake kira I phone 7+ durkusa tayi cikin girmamawa tamikamata wayar tana fadin”Gashi Hajiya..”sai da tabata lokaci kafin tamika hannu ta amsa cikin lokaci kadan ta bude password din dake cikin wayan wani Hoto ya bayyana kamar inna kalla dakyau itace acikin hoton tana Rumgume dawani Saurayi suna dariya.
DURLING SON..Naga tayi Dialing kafin takara akunne dagachan bangaren Aka dauki kiran da cewa” UMMI NA… Yafada cikin muryan shauki da soyayyyah mai Tsanani”cikin Dakewa ta furta duk daranta yayi sanyi dajin muryan gudan jininta,”where are u..Tun safe kafita baka dawo ba” ajiyar zuciya ya sauke yana kara kwanciya kan kujeran motan Hannunsa yadora akai yana shafawa kan ya furta cikin Jarumta” Am on my way Ummi yanzu zaki ganni insha Allahu”Katseshi tayi da cewa”Tambayarka nake ina kaje”Tafada da kakkausan murya.
Rausayar da kai yayi kafin yace” MAIDUGURI Naje Ummi Baffa Ya kirani yana son ganina..Naleka ki kan na wuce….”Kit..yaji ta yanke wayan bayan tajamai dogon tsaki.. sauke wayar yayi yana sakin mirmishin dayafi kama da kuka ciwo kan yakoma yakara jingina da kujera yana sakin ajiyar zuciya ajere Ransa namasa kuna..Baisan yaushe ne Ummi zata Kaunaci danginsa ba jigonsa? Dangin mahaifinsa da badai kamar su duk duniya? Abunda yafaru Shekara daShekaru yakamata ace Tunda anyi hankali kuma komai yakare to donme bazata hakura ba? ya tsani Halin Ummi na Riko Da rashin Yafiya.
Cikin Fushi da bacin Rai ta sakin wayar tafadi kasa kan ta mike tana huci karime dage durkushe taja baya jikinta na Rawa saboda sanin halin Hajiya, in Ranta yabaci to kowama yazo kusa da ita zata iya hadawa..Fuskarta na kallah Tuni tahadeta ba alamar Fara”a huci kawai take saki kafin tafara mgana cikin Fushi da Hausanta wacce ke chakule da Labraci” Wlh SHETTIMA BAKA ISA BA..Baka isa ga Rabani da dana gudun jinina ba wanda nasha wahala renonsa Tun yana karami har yakawo iyanzu..Tunda kuka Nunamin Tsana nikuma nayi alqawarin duk wani abu daya dangance ni sai na Rabaku dashi ciki kuwa harda DANKU DIN..MU”AZZAM NAWANE NI KADAI
Takareshe Fada da fashewa da matsannanciya kuka mai cinrai Da bakinciki kafin tashuru takalmi tafara haura Step tana kuka kamar karamar yarinya..Karime dake gefe fadi kawai take Allah ya huci zuciyar Hajiya..yan aikinta dake bangaren Kichen Uwale da Lami suka Fito hannu Dafe da kirji sunyi jugum jugum domin Inda sabo sun saba ganin Hajiya lokaci bayan lokaci tana shiga cikin wannan halin wanda ko dan lelennata bai isa ya sauko da ita ba sai don kanta ta gaji tasauko..
Jugum jugum sukayi kowacce hannu dafe da kunci suna zazzaune afalon suna kallon agogo daidai lokacin Da agogon ya buga 10:00pm daidai nadare Daidai lokacin kuma sukaji sanda Sani maigadi ya wangale katon get din gidan..Sunajin haka suka mimmike kansu akasa cikin lokaci kadan sukaji shi yana gaisawa da megadi da sauran ma”aikatan gidan kafin Ya nufo kai tsaye cikin gidan.
Yana gaba Ushe na binsa abaya dauke da yar jakarsa na briefcase dinsa,Da siririyar muryansa yayi sallama bayan ya bayyana akaton Falon, kamshin Turaransa MAN ya fara bayyana kurama kofar falon ido nayi lokacin danayi Arba dashi wow…Nafurta lokacin danayi Arba dawani Dogon mutum giant Ne tako’ ina jikinsa yana murde ne kirjinsa yana Da Fadi kamar ingarma, Chachulate colour ne shi ba baki ba kuma shi ba fari ba,idanunsa Daradara ne masu dauke da doganyen gashin ido zara zara gashin giransa cike gashi wanda takusama hadewa hancinsa kuwa har gaba yake tare da karamin lipa dinsa wanda yake maiko kamar yashafa liptick,kallo daya zakamai ka fahimci yahada Ruwa biyu Wato balarabe Da kanuri domin fuskarsa kadai zai nuna maka yana da hadaka da duka biyun..Yana sanye ne cikin wasu American Suit black and white,wuyansa matse da Tektie wanda ya mtse wuyansa Dashi hannunsa sanye Da Agogon azurfa na maza kafarsa sanye cikin Rufaffan Takalmi na Fatar Damisa..Sumar kansa tayi kwance kamar yana shafa mata shampoo kallo Daya zakamai Kafahimci tsantsan Jarumtarsa Da kamewarsa ayadda yake Tafiya zaka fahimci tsantsan miskilancinsa wanda ko Tafiyansa Da yadda yake mgana ma ya bayyana BARRISTER IBRAHIM MUHAMMED MOODU KENAN WANDA MUTANE SUKAFI SANI DA BARRISTER MU”AZZAM MOODU Baban Ma”akacin A kotun Najeria Suprame High court Abuja akallah ashekarun Haihuwa zai kai 30 Aduniya.