NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

  Jikin Abbie da mooh na rawa suka karisa Suka rikesa Abbie na fadin”Don”t go Son,wakeup nabaka auren Lubna gobe sai adaura muku aure..”yafada yana jijjigasa,lumshe ido mu”azzam yayi yana sakin mirmishi kafin ya damke hannun Abbie yana fadin”Tanque Abbie…”yafada kafin jinin yafara zubowa ta hancinsa lokaci daya jikinsa na saki,kafin kuma idanunsa suka fara rufewa

Da wani irin Ihu da firgici lubna take Furta..”No….”lokaci daya tana tare jinin da duka hannuwanta.

Wowowo Janaf fans ya kukaga page din yau? very interresting ko? Tarihi ne zai maimata kansa,domin haka Moodu yayi daga zuwa sudan yadawo da Ummi Suhaima,tabbas hakan yana cikin kaddaransa ne,ga mu”azzam ma zai dawo da lubna,shima yana cikin kaddaransa,ga zahirah Alhaji kabiru yafara moran sadakinsa,bata da yarda zatayi shima yana cikin kaddaranta,bakomai kake so Arayuwa kake samu ba,ba kuma koda yaushe ake Farinciki,yau ayi Farinciki gobe akasani haka,so tari muna mallakan abu ne batare da munsan abun zaimana wani amfani ba,sai don kawai bamu da yarda zamuyi ne,sau tari zamu hadu dawasu mutune,mu so su koda son bazai mana amfani ba,to lubna tana son mu”azzam koda soyayyar bazata amfaneta ba,Shima zai aureta koda Auren bazai amfaneshi ba,Allah kadai ke iya tsarama bawa Rayuwarsa yadda yake so kodon yabamu wata aya dazai zama izini garemu,am srry duk wanda page dinnan bai masa ba,ya yafemin haka Salon lbrin yake,Ngd sosai Allah ya sadamu da kaddaran da zamu iya dauka Amin????

Sharhi nakeso yau sosai bani son wannan godiyar yau,kufito ku tattauna saboda Karfin gwiwata plz

comment, share and vote

    Janafty   
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

   *Mallakar:JANAF*
   *Wattpad:Janafnancy12*

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

I Dedicated dis page to u guyzs ZUMUNTA NOVELLA.,.Special thanks,to u Maman sayeed and Noor,Aisha Aliyu,Yar Fulani,Nusiba gidado(wish u quick recovery dear),Ummu sudess,and u Ummu husna,and all members of d group,..Thank you once again,Janafty relli appreciated????✌

NOT EDITED????

        *NO 36*


Cikin azama Mooh ya mike yana fadin"Abbie kamosa muje asibiti kamar fa ya suma ne? yafada yana rikosa da hanzari lubna ta mtsa baya Abbie ya tallabo Mu"azzam mooh ma yatallafo gefensa suka fice dashi zuwa haraban gidan,lokacin tuni ya suma jikinsa ya saki,bayansu lubna tabi tana rafzan kuka,mota mooh suka sanyasa,kafin Abbie yazauna baya tare dashi shikuma mooh ya shiga bangaren direba yaja suka fice da hanzari.

Lubna ta nufi motarta tana fadin”mubi bayansu mom..”tafada cikin kuka,komawa mom tayi ta yafo gyale kan doguwar rigar dake jikinta tafada motan Lubna suka mara su Mooh baya.

Asibitin da lubna take aiki Suka kaisa suna isa cikin,gaggawa likoci suka amshesa sukayi cikin emergency dashi suna kokarin ceto Numfashinsa,ciki harda Dr Sultan ,lubna ko tana waje takasa shiga, kuka kawai takeyi kamar ranta zai fita mom ce ke rumgume da ita tana faman lallashinta mooh ko da Abbie suna tsaye suna safa da marwa,fuskokinsu babu Annuri ko kadan hankalinsu amatukar tashe.

Likitocin sunyi matukar wahala akan Mu”azzam domin condtion din dayake ciki yayi over gaskiya wannan karan ma,ya rasa jini da yawa,koda akazo cikin gaggawa ana bukatar jinin Lubna ta mike zata bada Dr Sultan ya dakatar da ita domin yace ko tamanta ne,bafa tayi wata da bada jininta ba,bazai yuyu yanzu asake diba ba,sai alokacin su Abbie kejin Lubna tabawa mu”azzam jininta tun farko,tundaga lokacin Abbie ya yarda ya Amince yarsa tafada kaddaran son mu”azzam wanda shikuma yake kwance yana fama da jinyar soyayyar watanta.

Siyan jinin akayi leda biyu aka sanyamai bayan anyi nasaran Tsaida jinin dakuma daidatuwar Numfashinsa,ammh ta taimakon Na”urorin dasuke jawo Numfashinsa,likitocin sunyi ta masu Abbie fada suna fadin”Tayaya za”a dinga barin masu wannan problem suna zama cikin damuwa yakamata duk abunda suke bukata ayi musu shi cikin gaggawa,ba”a son su dinga zama su kadai balle su yawaita tunani mara kyau,yanzu gashinan yakai mataki na biyu domin gefen zuciyarsa hartafara kumbura sakamakon mtsamata dayake da tunani hade da damuwa,sunce agaggauta yimai duk abunda yake so kafin ya farka matukar suna son da”nsu araye domin akara Faruwan haka daidai ne yake,da Rasa rayuwarsa domin zuciyarsa tana gabda kaiwa stage din karshe.

Iya tashin hankali Abbie ya shiga dafe kansa kadai yayi yana kiran Sunan Allah mooh dake gefensa ya dafa kafadansa yana fadin”plz Abbie ka cikama Mu”azzam alqawari ka daura masa Aure da lubna,saboda gudun kada mu rashashi,haka Allah ya nufa lubna ce matarsa bawa bai isa ya gujema kaddaransa ba..”yafada idanunsa sun kada.

Juyowa Abbie yayi yana fadin"Taya zan daura Auren mu"azzam da lubna alhalin zuciyarsa,bata tare da ita,tana tare da tsohuwar matarsane,anya baka ganin hakan cutuwane garesu duka biyun damu kanmu gabadaya.."Abbie yafada yana kallon mooh,girgixa kai mooh yayi yana fadin"Kaddaran Allah kenan,ada muna da masaniyar zuwansa garin nan ,har lubna ta hadu dashi ta taimakamai? harta kawo shi gidanmu kaganshi a mtsayin wanda ka dade kana nema shekara da shekaru? bamu da masaniyar komai Abbie,to kadauka duka komai Allah ya tsarashi ne,kuma baka tunanin ita lubna na tsananin sonshi? wlh nadade da gane lubna na son mu"azzam Abbie,kuma rasashi tamkar itama takamu da irin ciwonsa ne,kenan kana so ayi biyu babu ne,? yafada hawaye na kwaranyomai.

Tsuru da ido Abbie yayimai kafin yace”u are great son..,tabbas mganarka haka take komai da Allah ya tsara daki daki yake zuwa,na yarda na Amince zan daura musu aure ammh sai in da yardan ita lubna taji tagani zata iya auransa,to ni bani da mtsala dole ne bazan musu ba dukkansu..”yafada yana kallon mom da lubna wa”inda suke gefe suna jin duk abunda suke fadi…

Takowa yayi har gabanta kafin ya kira sunanta “Lubna.”yafada yana dukawa bisa gwiwowinsa dagowa tayi tana fadn”Na”am Abbie..”tafada lokaci daya hawaye na kwaranyomata,kallonta yayi cikin ido kafin yace”Ki fadamin gaskiya bawai don zakiyi taimako ba,da gaske kina son mu”azzam? kuma kin yarda zaki zauna dashi ahaka? yafada yana kafeta da ido..

Dagowa tayi tana kallon Abbie kafin ta sunkuyar dakai hawaye suna zubomata tace”ya zanyi Abbie? juz tell me ya zanyi? wlh nayi kokarin yakice son mu”azzam tun lokacin danaji lbrinsa ammh ina Allah baya shawara da mutum lokacin dazai Umarci mala”ika daya diga soyayyar dayanmu a zukatanmu ba,bani da zabi Abbie,i Swear zan iya rayuwa da mu”azzam ahakan Abbie,shikuma yacigaba da rayuwa da son wata,i accept na yarda it my destiny..”tafada tana dora fuskarta bisa kan hannun Abbie tana kuka mai cin rai.

Mom dake gefenta ta rumgumeta tana fadin”a”a karkiyi haka dota,baki tunanin ki rayu cikin kuncin rayuwa,tunda baya sonki.”Tafada tana rumgumeta,kamkameta lubna tayi tana fadin”Wlh zan iya mom,indai zan dinga kallonsa amtsayin mijina koda bazai taba kallona amtsayin matar aurensa ba,naji nagani kuma zanyi mai biyayyah tamkar baiwa agaresa”Tafada tana tsiyayan hawaye.

Mikewa kawai Abbie yayi yama Mooh inkiya daya biyosa,tashi yayi tsam ya biyosa,suka fice,suna fita haraban Asibiti Abbie yakira wani wanda yake kamar uba garesa sukayi mgana,mota yafada yama mooh mgana akan sukoma gida,cikin lokaci kadan suka isa gida,suna zuwa Abbie ya shiga daki ya fito da wasu takardu ya kara umartan mooh daya kara jansa su koma,wanda wannan karon wani babban masallacin jumma”a suka nufa,fita Abbie yayi yashiga masallacin yasamu Liman Abudulfatahi yayi masa bayani wanda ya gamsu sosai suna cikin mganane sai ga wanda Abbie yakira awaya ya karisowa Mooh ya shigo dashi har cikin massallacin,inda suka tarar da mutane uku kachal,nan da nan aka fara neman Aure Abbie shne waliyin mu”azzam kuma yabiya sadakinsa da wani katom gidansa dake nan,sudan din wanda akallah zai kai kimanin kudi naira miliyan biyar da wani abu,ayayinda liman Abdulfatahi yayi amshI Auren Lubna tare da shaidun da suke, wajen aka gudunar da daurin Auren cikin lokaci kadan Lubna ta tabbata amatar mu”azzam,kaddara ta riga fata.

Bayan Daurin basu wani jima ba,Abbie yayima Liman Abdulfatahi godiya suka komo asibitin yana zuwa yamika Ma lubna takardun gidan yana fadin”ga Sadakinki,an daura miki aure da mu”azzam yanzunan”amsa luba tayi hannunta na rawa ta dago tana kallon Abbie kai yadagamata yana fadin”Eh..,Ina fatan hakan yazamo silar mirmishinki,dariyan mu”azzam da farincikinmu nan gaba..”Mooh da mom suka amsa da amin itako sunne kai tayi tana mirmishi lokaci daya hawaye na zubomata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button