NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Yagana ta amsa da Amin daidai lokacin datake kiran Ummi a waya,takira ta shiga ammh har ta yanke ba”a daga ba,sai takara kira,Lubna dake bedroom din Ummi tana shiryamata kaya awardrope taji wayar Ummi na ringing ta dauko ta kawomata kafin ta sauko kasa wayar ta yanke,Tamikama Ummi wayar kenan kiran ya sake shigowa Lubna tace”Yauwa gashi Ummi ana kiranki..”

Ummi dake zaune Afalo ta amsan wayan tana kallon Screen din wayar take fadin”Mutan maiduguri ne,Yagana ce,Allah yasa lafiya..”tafada tana daga kiran daga chan bangaren Yagana tace”Uwar ango akaro na biyu..”Dariya Ummi tayi tana fadin”yagana yau kuma sabon suna na samu,me aka samu ne,naji muryanki tayi chakwai ne,kamar wata yar budurwa yar sha takwas..”Tafada cikin zolaya.

Gyara zama yagana tayi kafin tace”Dole kiji muryata haka,Zamu sake kawo miki zahirah akaro na biyu..’Da hanzari Ummi ta mike tana fadin” Ban…ga..ne..Me..Ki..ke Nu..Fi ba..”?Tafada cikin rawan murya yagana tana dariya tace”Auren ya mutu,yanzu mahgana ke fadamin Zahirah ta kirata take fadamata wai ma kwana goma da sakin nata..”Da wani hanzari Ummi tace”Bani son zolaya yagana,wlh zuciyata zata buga..”da Sauri yagana tace”Wlh da gaske nake Suhaima,Mu”azzam da Zahirah Allah ya dubesu ya sake hallarta musu juna akaro na biyu.”

Ai da wani hanzari Ummi ta sulale kasa tana yima Allah Sujudda ta dade tana kwararo godiya ga Allah kafin tadago Fuskarta shabe shabe da hawaye Lubna dake gefe takalli Ummi tace”Ummi,lafiya kuwa daga gama waya kina kuka kuma? da hanzari Ummi ta mike ta rumgume Lubna tana fadin”Ya saketa Lubna,wlh ya saketa…”Da mamaki lubna ke fadin”Ya saki wa..?

Ummi tace”Zahirah mana..”Ido Lubna ta zaro ta rike Ummi tace”Da gaske Ummi..? batama bari Ummi tayi mgana ba ta saki Ummi ta rumtuma dakin Mu”azzam tana kwalamai kira,shiko yana zaune bisa gado yana aiki bisa system dinsa jin irin kiran da lubna kemai da karfi ne yasashi saurin durowa daga gadon hankalinsa tashe Daidai ta shigo sukaci karo da juna.

Cikin hanzari yace mata”Ke lafiyanki kuwa..?”Haki takama kafin tace tana dariya'”An saketa…”Harara ya zabgamata kan yace”ke natsu an saki wa kuma,yanzu daddare nan..?”yafada yana jijjiga kafadunta.,Hannunsa ta riko tana fadin”Zahirah aka saka yanzu aka kira Ummi ana fadamata daga maiduguri..”Zaro ido yayi yana kallonta kafin ya damki kafadunta da karfi yana fadin”wai wasa ko gaske..? yafada yana neman Fita daga hayyacinsa.

Lubna na dariya tace”Wlh da gaske ya mu”azzam Zahirah ta sake zama naka akaro na biyu..”Ai batama karisa ba ya sabeta ya fara juyawa da ita, acikin dakin yana dariya gefe daya kuma hawaye yake,Lubna tana kallonsa tana dariya hawaye na zubomata,sai da yagaji da kansa ya sauketa kafin ya Rumgumeta kamkam yana fadin”Tanque So much..Tanque Lubna Tanque for been their for me..’yake fada yana hawaye.

Hannuwanta Lubna tasaka ta rumgumesa back bayan ta kwantar da kanta abayansa hawaye suna kwaranyomata,lalle Tayi gaskiya data hasaso dawowar Zahirah Rayuwar Mu”azzam ne kadai zai sa tasamu mtsayin Kallo mai daraja A idanun Mu”azzam,Hawayen tsausayin kanta suka cigaba da zubomata lokaci daya tana kara kamkame Mu”azzam din.

Zakujini Shuru Cuz ina Katsina na tafi biki,buh in,na samu lokaci zaku jini..,One Luv#Janaf fans#

Kakata wacce tahaifi mamata hadiza,Bata da lafiya har anyi addmitting dinta a hospt,plz include her in ur Prayers

Comment,share and vote.

Janafty
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

Today D Whole Chapter Is Dedicated to u,my Childhood Best Friend, FADILAT FALALU MASKA,D BRIDE????,May Allah(SWA)Albarkate ur Marriage Wit full happiness,Baraka,taqwa,love and Childreen..,HML????????????❣????????????????

NOT EDITED????

                    NO 41

         “””Sundade Rumgume da juna kafin Mu”azzam yarabata da jikinsa ya dagota yana kallonta,itama shi take kallo cikin wani yanayi na shauki da soyayya ta har abada,Mu”azzam kwayan idon Lubna yake kallo,yana ganin tsantsan soyayyaarsa,Lumshe ido tayi hawaye suka kwaranyo ta gashin idonta.

   Tattausan Hannunsa Mu”azzam ya  sanya yana Sharemata hawaye yana fadin”Stop crayiing kinji yanzu ba lokacin Kuka bane..”Ya fada yana sakin mata mirmishi jin abunda yafadane yasata Saka hannu ta karasa share hawayen da suka zubomata tana dan mirmishi itama tana gyada mai kai,Sakin hannunta yayi yana fadin”Ina Ummi na..?

  ‘”Tana Chan Falo..”Tabashi amsa ,bai tsaya wani mgana ya wuce ya fice daga dakin Fuskarsa da jikinsa suna muna tsananin Farincikin dayake ciki da kallo ta bisa kafin tazame bisa gado tana share hawayen daya zubomata na tsausayin kanta tare da Tunanin makomarta in Zahirah ta dawo tasan cewa matukar Zahirah na tare da mu”azzam Wata mace agunshi ba mace bace,saboda baya ganin kowa amtsayin Mace sai ita.

    Mu’azzam yana fita ya fito Falo yana kwalama Ummi kira,da hanzari ta mike tana dariya ta taroshi,tana fadin”Son..”take Fada tana hawayen Farinciki yana zuwa baiyi wata wata ba itama ya chabeta sama yana juyi da ita yana fadin”Ummi na,zahirahta zata dawo gareni Allah Abun godiya..”yake fada yana juyi da Ummi,dariya Ummi keyi tana shafa kansa cikin Farinciki kafin tace”To Saukeni Son,Kada ka kadani..”take fada tana dariya Sauketa yayi kafin itama yajata ya rumgume cikin Tsananin Farinciki Kamkamesa Tayi tana shafa kansa harzuwa bayanshi tana hawaye mai cike da murna da Farinciki,lalle Rayuwa juyi juyi,wai yau Ummi ce ke kukan Murna saboda Zahirah diyar Fadi zata dawo garesu..Dama Hausawa sunce Abunda yasaka Dariya watarana ba shakka shi zai saka kuka.

Dago da kansa tayi tana sharemai kwallah take fadin”Bari kuka,ango da kuka,to amarya kuma mezatayi? tafada da sigar zolaya shagwabemata yayi yana fadin”Ummi nidai yanzu ba wannan ba,tashi zakiyi muje mu Taho da zahirah don Allah..”Sororo Ummi ke kallonsa kafin tace”bazai yuyu ba Son,don yanzu muka kara mgana da yagana take fadamin Shi mijin yace ta zauna chan tayi idda kafin ya maidata ga mahaifinta,..”zaro ido Mu’azzam yayi yana fadin”What..?haba Ummi in Tazauna Ubansa zatayi masa,nidai wlh da sake bazata zauna chan zanje dakaina na dawo da ita gidan nan adakinta tazauna in tagama idda amaidamana Aurenmu..”yafada Fuskarsa na Chanzawa zuwa bacin rai.

   Juyawa kawai Ummi tayi ta isa ga Kujera ta zauna tana fadin”Son kacika rigima,ai kowa yasan Zahirah takace,so karka damu kabarsu suyi yadda sukeso bani so kayi sonkai aciki..”binta yayi shima yaje ya zauna kusa da ita yana fadin”Haba Ummi don Allah karki ce A”a nifa tsoro nakeji kada ya maidata matarsa..”yafada idanunsa na nuna tsoron.

  Hannunsa ta riko tana fadin”Nasan manufarka,abunda nakeso dakai kabari aji ta bakin mahafinta,domin ance haryanzu baice komai ba,ammh bana Tunanin bukar zai barta achan tayi iddata,kadai jira muji koma miye sai muje ayi mganar,kaji..”Tafada tana kallonsa,zuramata ido yayi zuciyarsa na gudu kafin ya maida kansa bisa kafadanta yana fadin”Shikenan..”cikin karaya,hannu tasaka tana shafa kansa tana fadin”karka damu Son,i promise u Zahirah takace insha Allahu..gyada mata kai yayi kafin ya gyara kwanciyarsa bisa cinyarta yana wani lumshe ido Farinciki tare da fargabane suka tarunmai waje daya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button