NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

  Kofar falon tana budene, tana turawa ta bude,falon babu kowa tsint ammh ko”ina sai tashin kamshi yake tsaf tsaf kamar ba dakin Namiji ba bedroom din ta nufa ta sanya hannu tayi knooking daga chan bangaren Mu”azzam da fitowarsa wanka kenan yace”yes come in..”da sallamarta ta shigo bayan ta turo kofan ahankali,tana dagowa karaf suka hada ido,tsuramata ido yayi yana kallonta sama da kasa,aransa yana fadin”Sarki ya tabbata ga Allah shugaban halittun duniya.

  Itako kunyane yakamata ganin yadda rigar wankan ya damesa har yana fitar da surar jikinsa,kirjinsa kuwa abude gargasa tayi kwance luf ruwa na diga ajikinsa,sunkuyar dakai tayi tanajin kamar ta juya,ganin haka yasa yayi Fuska kawai ya wuce gaban dressing mirror dinshi yana kokarin shafamai yayi kamar baisan da tsayuwarta agun ba.

Comment and vote,share

One luv Janafty Fans
     
[18/08, 14:18] 80k: ????UWAR MIJINA..!????
   (Soyayyah,sadaukarwa,hakuri,tare da biyayyah mai tsanani)

      Alkalamin:JANAF
      Wattpad:Janafnancy

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

I Dedicated dis page to u My Sisi of life…AISHA ALTO…,Soyayyarki gareni mai girmace,kaunarki gareni Allah ne kadai yasan iyakarta…Hakika kin zamo wani jigo na rayuwata,ina godiya da kulawanki agareni Janaf tafada kuma takara fada,AISHA ALTO KINA BURGENI????

NOT EDITED

             NO 16

     Kusa da sit din,wata yar budurwa aka ijiyeta wacce ashekaru bazata wuce sa”ar Zahirah ba,mirmishi ta sakarmata bayan Teacher nasu ya gabatar da ita amtsayin sabuwar Dalibarsu,itama zahirah mirmishin ta maida mata murna ya cikata na ganinta cikin sa”anninta da sunan daukan karatu,farincikinta yakasa boyuwa har ya bayyana akan Fuskarta,koda tazo Maths akeyi dayake double period ne,shiyasa ana kammallawa aka fita break.

  Kowa yafice sai Zahirah kadai ke zaune tana raba,ido yarinyar data mata mirmishi ita tatashi tazo har sit dinta tana fadin”Assalamu Alaiki yar”uwa..”Tafada tana zama kusa da ita,Zahirah tadago tana kallonta lokaci daya take amsa sallaman nata”Amin wa”alaikas salam..”Ta amsa cikin sakin Fuska hannu ta mika mata tana fadin”My Name is ASMA”U GADDAFI NURA daya daga cikin daliba ta Nurul bayyah”Tafada tana mata mirmishi cikin Farinciki zahirah ta mikamata hannu suka sarke tana fadin”My Name is ZAHIIRAH ABUBAKAR BAHGANA Naji dadin haduwa dake Asma”u”

   Hannunsu rike da juna suna mirmishi Asma”u tace”Nima haka Zahirah…”Atare suka kalli juna suka murmusa daganan kowacce tayi shuru sai chan Asma”u ta kalleta tana fadin'”Bazaki Fita break bane..”Gyada mata kai kawai zahirah tayi Ok kawai Asma”u tace tana tashi,sit dinta taje ta bude jakanta ta dauko wani katon biccuit da Madarar holladian tazo ta kawoma Zahirah tana fadin”Nima bancika fita break ba,komai nake bukata nakan zo dashi daga gidane,so muci wannan..”Kallonta zahirah tayi tana ayyana kirkinta mirmishi tayi zatayi mgana Asma”u ta marairaice tana fadin”Plz Besty karki ce A”a don Allah..”Ganin yadda tayi yasa zahirah takasa mata musu,nan sukaci biccuit din suna korawa da madarar holandian din,har suka koshi,hira suka cigaba dayi Duk da Asma”u ce keta hiranta,ita daga Umh sai A”a.

  Suna zaune aka dawo aji sai Asma”u takoma gun zamanta,koda english Teacher ya shigo maida hankalinsu sukayi kansu harda zahirah wacce taga bambamci sosai ta fanni da dama da mkrantar garinsu,dayake tana son Abun aranta Tuni ta cire komai ta maida hankalinta kan Abunda ake koya musu,ahaka har aka tashesu,koda aka tashi tare suka fito aji ita Da Asma”u wacce ke rike da hannunta kam,har bakin get din school inda Direban Asma”un ke jiranta,Haduwar farko Asma”u tayima Zahirah tayin shiga motarsu su kaita gida ammh Zahirah tace itama za”a zo daukanta ba yadda ta iya illa ta shiga motar direba yaja tana dagama Zahirah hannu itama tana dagamata,basu dade da Tafiya ba sai ga Ushe,wanda daman Mu”azzam yafadamata shi zai dunga zuwa daukanta in an tashesu.

   Cike da Murna Zahirah ta shigo falon tana kwalama karime kira da”Mama..Na daw…”Kalamanta sun makale ne lokacin dataci karo Da Ummi,zaune tana kallonta,,tuni jikinta yafara rawa saboda tsoro durkushewa tayi bakinta na rawa,tace”Ina..Y..Ni Ummi..”Tafada tana kafta ido.

    Wani dirty look Ummi ta watsa mata tana mamakin yadda yarinyar tayi wani kyau da ita,wato tasamu hutu ko,tabe baki tayi kafin ta kauda kai ko mgana,ganin haka yasa  zahirah mikewa jiki asanyaye ta karisa dakinta,Da kallo Ummi tabita tana tsinema Shettima da Fadi,domin su suka cuceta.

     Tana shiga daki,ta cire Uniform din nata tafada tiolet tayi wanka tazo tayi sallah,tana nan zaune Sai ga karime ta shigomata da kulan abinci tana mata barka da dawowa,cikin farinciki zahirah ta rumgume Karime tana murna nan fa ta zauna tana ta bata lbrin mkranta,harda lbrin Asma”u Karime taji dadi aranta ganin yadda zahirah take cikin farinciki mara misaltuwa Ai su karime sunsha Hiran mkranta kamar ba gobe…

   Karfe hudu na bayan la”asar Sai ga wani malami yazo yace yallabai ya turo sa yazo akwai wacce zai fara yima karatun addini,Ummi bambarankwai taji zencen shiyasa afusace ta shiga ciki ta kira mu”azzam tana fadin”Kai kana haukane,wani salon iskanci ne wannan,bayan wahalan sata mkranta harda wani salo ne na dauko mata Wani malami wai da sunan zai koyamata karatun addini,yo ina ruwan wani tayi ta zama da jahilcin mana,wa ya damu”,Tafada ranta bace.

  Gyara zama yayi yana jingina da jikin kujeran dayake zaune yace”Kiyi hakuri Ummi na nayanke hukunci batare da nayi shawara dake ba,Duk abunda kikaga inayi yana cikin alqawarinmu ne shiyasa”Tsaki Ummi taja tana fadin”alqawarin banza,gabadaya ni aka cuta ammh daga baya su suketa samun Nasara akaina,to bazai sabu ba tun wuri ka chanza mgana kai wlh kaja tsiya har mkrantan sai na hana naga karyan iskanci”Shidai mu”azzam hakuri yaita bama Ummi don yasan za”a rina cikin kwantar da murya yace”To shikenan Ummi yarda kike ce,akoda yaushe bani da buri illa naganki cikin Farinciki,Umarninki shine nawa,bari nakira malamin na sallameshi kawai”Daga haka ya datse kiran yana mirmishi Yasan cewa Ummi zata kirasa daman shiyasa yaki gayamata ya shiryama hakan,illai kuwa sai ga kiranta sai da takusa tsinkewa ya daga yana fadin”Ummi na,ina kokarin kiransa ne..”Ajiyar zuciya ta sauke kan tace”It ok..Ka barshi ya dinga koyamata ba don halinta ba”Tafada ranta ba dadi,godiya ya shiga jeramata kafin ta yanke wayar,haka kurum takejin kamar wani abu zai faru gaba in ta biyema Shawaran Mu”azzam.

Zahirah taji farinciki lokacin da lami take fadamata ta shiryo tazo Yallabai ya aiko azo amata karatu,murna kamar ta kasheta aharabar gidan suka shimfida darduma harda dan allonsu,da fari sai dayafara jarabata yayi mamakin Ilimin yarinya,ammh sai ta bugaci da adawo baya,saboda dadewar datayi batayi ba,Hadisine da qur”ani,da Ahalari,da Sai Tauhidi yafara koyamata bayan ya bata littafin wanda duk dawainiyyan yallabai ne,hakika zahirah taji dadin yadda rayuwarta take budewa daci gaba ta ko”ina shiyasa gabda mangariba suka tashi karatun da malamin nata Ustaz Haruna,sallar kawai tayi ta dauko littafan nata tashiga dubawa,ranar dinner ta ma sai su karime suka dauke littafan kana ta iya cin abinci,tana kamallawa takoma na boko tana dubawa tana mirmishi murna kamar ya kasheta ta zama cikakkiyan yar mkranta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button