NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

  Mu’azzam dake kallonta cikin mamakin yaushe Ummi takoma mara imani haka,fuska babu Annuri,maida kallonta tayi kansa kafin tace”Kai kuma na dawo kanka,wlh tallahi ko kallon arziki kaima yarinyar nan,indai naji lbri sai ka dandana gudarka,kai ko dakinata ban amince   ka shiga ba,in kuma ka kwatanta hakan Ranar zaka san wacece SUHAIMA”Tafada ranta na mata kuna lokaci daya kuma idonta ya ciko da hawaye cikin karaji takalli Zahirah tace”Ki fitarmin daga Falo bakar munafuka wlh yadda na tsani mutuwa na haka na tsani ganinki,ki ficemin daga gaba”Ummi tafada kamar zata kifa mata mari.

  Da hanzari ta mike jikinta narawa tafara tafiya hartana, hardewa da hijabi tayi baya zata fadi sai kuma bata fadi ba,da hanzari gudu gudu ta shige dakinta tana kuka,da harara Ummi tabita zuciyarta na mata suya ji take kamar tatashi ta rufeta da duka harsai ta mutu.

Mu’azzam dake zaune kamar mutum mutum ta kallah kafin ta mike tana fadin”Nasan kana Tunanin Yaushe na koma haka ko? tafada tana kallonsa kan tayi mirmishin dayafi kuka cewa tace'”Shettima da Fadi su suka maidani haka,kai kuma kabasu damar bayyanar haka ta hanyar yarda ka auro ta ka kawota cikin gidan danake rayuwa so kabi ahankali in ka saba Umarnina wlh Na lahira sai yafika jim dadi kaji ma na fadamaka'”tana gama fadarka ta haye sama da sauri.

    Da kallo mu’azzam ya bita har ta bacema ganinsa ajiyar zuciya ya sauke yana dafe kansa,yama rasa mafita yadade zaune kafin yatashi ya shige shashensa wanda bazai iya fadan hakikanin meke damunshi ba,ammh tabbas zuciyarsa babu dadi.

  Itako Zahirah tana shiga daki bedroom dinta ta shige tafada bisa gado tana kuka,kuka mai tsuma zuciyar wanda ke saurare ji take zuciyarta na mata daci,wani zazzabi me mai zafi da ciwon kai ya rufeta saboda ita mutum ce mara son hayaniya balle fada,tun tana kukan harta gji y
Tayi tayi shuru,nan barcin wahala ya kwasheta bata sani ba.

  Ummi kuwa itama kukan tayi adaki harga Allah acikin ranta batajin yadda takoma ammh kallon Fuskar zahirah kadai yakan haifarmata da Bakinciki da takaichi,hakika bazata ta iya control din kanta ba matukar tana kallon Fuskar yarinyar acikin gidanta,tadade tana Tunanin wani ma mataki yakamata tadauka kan shegiyar don so take ta gudu Da kafarta saboda wahala.

  Ranar haka gidan ya Wuni ba walwala da daga Ummin har Mu’azzam ba wanda yafito Su karime sun jera abinci bisa,Dinning, ammh wayam suke ji,sai da zashi masallaci sallar Magriba ne suka ganshi ya fito koda suka mai mganan Ga dinner girgiza kai kawai yayi kafin ya wuce abinsa donshi ko sha’awan abinci bayayi yanzu,Ummi kuwa Tea ta hada tasha da Bicuit saboda batama kaunar sakkowa kasan Don Ranta ajagule yake,Su karime da sukaga dai yau gidan ya murde sai suka kwashe abinci suka dibi nasu saura suka bawa su sani sukace su diba,sauran kan sai azubar don ina ma kaga mai bukata anguwa kowanne na fama da Naira.

  Itako Zahirah bata tashi ba sai, wajen Bayan mangriba,koda ta tashi jikinta duk ya saki idanunta sun kumbura Tiolet tafada ta dauro alwala tafara rama sallolinta bayan ta kammalla haka tadaga hannu tana addu’a tana kuka,jugum tayi domin cikinta yafara, kiran Ciroma wani azababben Yunwa takeji sai mutsu mutsu takeyi tarasa mafita,ganin ba Sarki sai Allah sai ta hau duba kayan da”a zo mata dashi acki tasamu Cincin harda tubulan da alkaki shi ta dauko tazauna ta hauci kamar ba gobe,sai dataci taci jikinta ba wani waje kana takura,falo tafita ta bude Fridge wanda ke cike da lemoka da Ruwa,guda daya tadauka ta bude nan take shanye,ajiyar zuciya ta sauke kafin ta sulale ne nan bisa kafet din Idonta na zubar kwallah Aranta tanajin ita tata KADDARAR KENAN.

Washegari

    karfe 7:00am Mu’azzam ya fito daga shashensa cikin shigansa na Suit black and White na kamfanin Armani wanda ya daure wuyansa da Tie baki kafafunsa kuma sanye da Takalmi rufaffe na kamfaninn Armani harda agogon Hannunsa,Sumar kansa tayi kwance kamar bai da wani damuwa kallo daya zakamai ka fahimci ya rame saboda yadda yayi dan,wuya ammh kyau hade da zatinsa na nan babu inda sukaje Jakar brief case dinsa ne sabe bisa kafadansa sai wani Siririn medicated Glass dake makale a idonsa wanda yakara Fito da zallar kyansa.

  Koda ya fito Falon babu kowa ammh tuni an tsab taceshi,kai tsaye sama ya haura zuwa dakin Ummi koda ya shiga tana tsaye tana saka dankwali,jikinta sanye da Atamfa Riga da zani,Cikin karfin gwiwa ya karisa gareta ya karbi dan”kwalin yana Fadin”Good mrning Ummi na”Cikin farinciki tace”Mrning my son,how was ur nite”Fine Ummi na’,yafada bayan yagama daura mata kallabin.

   Thank..”Ta furta lokaci daya tana riko hannusa tace”Kayi breakfast ..’Girgiza mata kai yayi kafin yayi mgana tace”Meke damunka ban hanaka Tafiya aiki bakaci komai ba”Tafada babu wasa Afuskarta,cikin sanyi yace”Kin hana Ummi na”Tace”To meyasa zaka tafi baka karya ba”Dukar dakai yayi kafin yace”Zan karya in na isa office”Batayi mgana ba taja hannunsa suka sauka kasa.

  Suna saukowa sukaji karo da Su karime zubewa sukayi suna gaishesu suka amsa cikin sakin Fuska,Dinning din ta nufa tajama sa kujera ya zauna kafin itama ta zauna Tea tafara hadaimai kan tahadamai da soyayyen Biredi ta kwai don yanasonshi,saboda ma shi su karime keyinsa duk safiya,saboda Ummi ta mtsa yasa yadan sha kadan Buredin kuwa ita tadinga bashi abaki ko ya kauda kai sai ta harareshi,ahaka har ya koshi,shima ramama kura aniyarta yayi bayan ya ciyar da ita,share hannuwansu duka sukayi da Tissue kafin ta riko hannusu su fara Tafiya,su karime dake gefe abun yabasu mamaki,to ina amaryan da”aka kawo jiya,basuji ko duriyanta ba,
 

  Har haraban gidan Ummi ta rakasa inda Ushe ke jiranshi,har cikin mota ta sakashi tayi mai addu”a kafin yafice tana daga masa hannu Ckin Farinciki tajuyo tadawo falon,Kan kujera ta harde,tamaida hankalinta kan wani Film da”ake watsawa a go Tv.

  Allah Sarki Zahirah,itako Tunda tatashi take kuka tama rasa mafita,dakyar tatashi tayi wanka ta gyara gadon data kwanta,shiryawa tayi cikin wani material doguwar riga wanda Bahna dinta yayi mata,ko hoda bata saka ba, ammh idanunta sun kumbura harda Fuskarta,da safenma cincin din taci ta dora da Ruwa don bata manta kashedin Ummi akanta ba na kada ta kuskura ta,giftamata afalo.

  Ummi dake zaune kamar wacce aka tsikara ta mike tana kwalama karime kira,wacce ta fito a hanzarce tana fadin,gani hajiya..”Kallonta tayi kafin tace”Maza shiga dakin yarinyarnan,kice tazo ina kiranta”karime da bata gane ina hajiya ta dosa ba sai tace’Na”am Hajiya kika ce? bangane wazan kira ba”Harara Ummi ta zabgamata kafin tace”Kar Allah yasa ki gane,yarinya da”aka kawo shekaranjiya gidan nan”.

  Da Sauri karime ta washe baki tace”Oh karamar Hajiya wai kike Nufi”Tsawa Ummi tadakamata lokaci daya tana Fadin”Kada na sake jin wannan Sunan,Nikadai ce hajiya agidan nan,kinji ko bakiji ba”karime da jikinta ke rawa tace”Naji hajiya to mezamu kirata dashi Tunda matar yall….”Wani kallo Ummi ta bita dashi dole tayi shuru ta mike ta nufi dakin zahirah cikin mamaki.

  Tura kofar tayi ta shiga da sallama Zahirah dake cikin bedroom kwance jin anyi sallama yasa ta mike da hanzari ta fito falon,sai taci karo da karime,durkusawa tayi tana fadin”Sannu Mama..”Daidai itama Karime ta durkushe tana fadin”Brka da Fitowa Amaryan Yallabai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button