NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

  Uwani tayi kasa tasaki guda tana fadin”ba shakka mai laya ka kiyayini mai zamani..”tafada tana musu dariya kan sufice,cike da bakincikin Zinatu tace”wannan din wata yar kazakazan ce kuma,kinajin mganar data keyi..”cikin xafi yagana tace”najita kyaleta Qawata,duk zasu gane basu da wayau dagasu har amaryan da Alhajin,nine fa,billahil lazi wannan karon sai nayi abunda bantayi ba”Tafada tana wani girgiza kafa komawa zinatu tayi tana zauna tafadin”sai mun tashi tsaye don naga suma da Shirinsu suka zo”barsu barsu..Nasu shirin suka sani basu san na yagana ba”ta katseta da kallo ta bita tawani girgiza tana cije baki.

  Har bedroom dinta bisa gadonta na alfarma suka sauketa,nan da nan yakura tafara yimata nasiha tare da nunamata sai tayi hakuri,tunda taji tagani kuma da idonta hajiya ma takara danata Ashe ko karkacewa tayi tace”ke ya”n nan dago kanki ki kalleni,bawata kalmar hakuri ban amince ki zauna wa dosara ta taka kiba,gidan mijintane kema gidan mijinki ne,in tace miki zo mu zauna ki bita kizauna in tace miki ubanki to kicemata Sai dai ubanta,don uba baifi uba ba,ke wlh indai kika zauna wannan matar tashiga hakkinki ni ba kanwar ubanki bane,kibari naji lbrin kina mata kukan nan naki,kiga yadda zanyi dake,in zaki mike ga kanki ki mike ki watsar da wannan sanyin naki atoh..”

  Kowa kallon Ashe yake yana dariya itako ta sha mur tana wani hura hanci,itako zahirah banda kuka ba abunda take,to yau kuma inda Allah ya jefota kenan,angama na Uwar miji an koma fargaban kishiya,Sun mata nasiha sosai kafin suyi mata sallama su wuce,zahirah ta rike yakura tana kuka,itakanta yakura tsausayin zahirah ya kamata dakyar ta lallasheta,suka fita suka barta tana kuka,sallama sukayi da yan”uwan Allaji wanda su little Ummi ke hannunsu suna ta dauka cike da sha”awa har bakin mota suka rakasu suna musu godiya.
 

Kifewa kawai tayi bisa gado tana kuka tafadin”Ya mu”azzam ka yafemin don Allah..”Take fadi tana kuka kamar wata zautattaciya sai da tayi ya isheta kana tayi shuru tana zaune tana raba ido Uwani tayi sallama ita da wata suna dauke da yaran Uwani tace”To amaryanmu mai kuka ga yara sun tashi suna bukatar mama..”tafada tana mikamata Little ummi Dan mirmishi tayi da kumburarrun idanunta kafin ta sa hannu ta karbesu ta dorasu bisa gado tana fadin”Na gode fa..”dariya uwani tayi tana fadin”a’a yima kaine amaryanmu.”tafada kafin sumata sai da safe su fice,sai da suka fita ta mike ta warware lifayan dake jikinta takoma ta zauna tabasu nono daya bayan daya bayan ta kammallah ne,ta mike ta isa ga wardrope din dake dakin ta bude nan taga kayanta jere harda na yaran,over roll ta dauko musu da kayan sanyi saboda taji garin da dan sanyi sanyi ta chanza musu kaya,ta kammallah kenan taji ana mata nooking lokaci daya ana shigowa da sallama.

  Rudewa tayi tayi wani baya kamar zata fadi saboda tsoro kafin tafada bakin gadon tana janye lifayanta ta saka bisa kanta jikinta na rawa yana tsaye yana kallonta ita da yaran dake kwance gefenta suna cilla kafa bakinsa yaki Rufuwa saboda murna,dogon mutum ne wankan Tarwada bai da wani kiba,sai dai ta murjewa da hutu,Ashekaru baxai wuce hamsin da wani abu ba,fuskarsa babu muni ko kadan yana da cikar zati datake amsa sunansa na Namiji,duk acikin mayafinta ta karemai kallo,nan ta tuna tabbas tataba ganinshi Saudaya agidansu yazo wajen bahna dinta…

  Cikin Farinciki ya taka ya isa kusa da ita bayan ya ijiye ledan dake hannunsa bisa side drower,ya zaune gefen inda yaran suke yana kallonsu kuma yana kallon zahirah wacce ta kudundune kanta cikin mayafi jikinta na rawa,Cikin muryansa ta dattako yace”Alhamdulillahi..Masha Allah..”yake fada kafin ya saka hannu ya dauki moodu yana fadin” Na godema Allah bisa ni”imar dayayimin nasamu zukekiyar mata ga ya”ya har guda biyu alokaci daya”yafada yana kallon zahirah kafin yadora da fadin”ko ba haka ba amarsu ta ango..”

  tacikin mayafin zahirah ta ballamai harara ko mgana bataima ba bai damu ba illah ya cigaba da wasa dasu little ummu ya dau wanan ya ijiye yakoma ma wanchan duk tana kallonsa,ta kagara ya fice yabata waje,a takure take,tana wannan mganar sukaji yagana da karfin tana kwalamai kira “Alhaji..!

Tafada lokacin da tafado dakin kai tsaye, Tsaye tayi musu akai shiko jikinsa na rawa ya mike yana fadin”armm dama yanzu zan Fito..”harara ta ballamai kan tace”yanzu zaka fito dinta,daga baka minti goma shine kazo ka rashe ko? to maza ka wuce muje tunkafin na saba maka”tafada tana nunamai hanyar fita,jikinsa na rawa ya wuce yana waigen zahirah datayi kasake tanaganin abun mamaki batama san sadda ta leko da kanta ta cikin mayafin tana kallonsu dukkansu imani ya kamata,ganin yadda jikin Alhaji ke rawa,kyace uwarsa ne.

  Zai fita yace”ga sako nan aleda ki duba kinji ki kulle kofa sai da safe..”yafada yana ficewa da harara yaga ta bishi kan ta waigo tana kallon zahirah tace”Kinga sakamakon mai Auren mijin yagana kenan,wannan sharen fage ne,yarinya muje zuwa.”tana fadar haka ta dakamata tsaki ta fice ta banko mata kofa,kama baki zahirah tayi tana mamakin kafin ta mike taje ta sanya kofan makulli tana fadin”Allah ya raka taki gona..”tafada tana rike baki kafin takara cewa”Yo Allah na tuba ban da kaddara ai ni banyi kama da kalan wacce zata auri mijinki ba,inda kinga mijina wlh sai kin raina kanki”Tafada tana kyafci kafin ta yada lifayan nata bisa Gado ta fada tiolet lokaci daya abunda yagana da Alhaji sukayi yanzu yashiga bata dariya.

  Suko su hajiya suna komawa suka ga babu Ummi ba ushe basu wani tsaya tambayan ba”asi ba,suka samu abun hawa sukayi sallama da su mahgana da su Ashe suka wuce ana jajantama zahirah ganin yadda duka auren nata biyu batai sa”a ba,koda suka koma gida kowa ya kwanta ushe Tuni yayi barci,Shureim kuma yashiga da Baffa cikin daki suna ciki suna hiran duniya,suka shiga suna musu sannu da gida,suna shaida musu sun dawo,Yakura takoma ta rufe gida ta sanya sakata kafin takoma ita da hajiya suka dauro alwala suka shiga daki,nan suka ga Ummi kwance bisa gadon yakura tayi dif alamun tana barci,hajiya ce tace”oh suhaima har tayi barci ma..”yakura tace”dole munfa dade gidanan hajiya,jaraban matan nan yadau lokaci”hajiya ta karba da cewa”ummh kedai bari ba wacce nake tsausayama irin zahirah da yan diyan nan,don kinga ita bamai hayaniya bace..”haka sukayita jajantama zahirah kafin su hakura su kabbarta sallah,koda suka idar bayan Yakura ta shimfida musu katifa akasa tayi musu shimfida ita da hajiya suna mganar suka dasa suna mamakin jaraba irinta yagana,Ummi na jinsu tayi kamar tayi barci,ammh idonta biyu,tuni hawaye suka gama wankemata fuska kuka na neman kwacemata tayi Saurin damke bakinta kada su hajiya su jiyota,bakincikinta daya yadda jikokinta zasu rayu awannan gidan,ga yadda su hajiya ke zencen uwar gidan na zahirah bata da mutumci ko kadan,takaichinta daya komai ya faru dasu itace sila da bata raba uwarsu da ubansu ba da yanzu suna tare da iyayansu da ita kanta,ammh son zuciya da rudin shedan sun kaita sun barota,kuka take da hawaye tana sharewa.


    
Sudan

  Babu shakka mu”azzam yasamu kwanciyar hankali matuka,domin mooh na debesa masa kewa matuka,yafita dashi ya xagaya dashi wurare,harta ma”aikatansu sai da yakaishi,Tsakaninshi koda lubna gaisuwace kawai bayan nan baya sakarmata fuska sosai,duk dai ita din kullum burinta ya dinga kulata,ko bamgana yake ta dinga sakamai baki kenan tana zagewa,Kuma ayawancin lokunta yasha kamata tana kallonsa,kuma koda ya kalleta bata kauda kai sai dai ta tsareshi da ido bako kyaftawa sai dai Shi ya kauda kai,sai dai tayi mirmishi tana kada kai ko ajikinta,Shiko mu”azzam yana lura da ita tsab,ko ranar yana daga sama yaga zuwan Dr sultan wajenta ammh tayimai Wulakanci,har mooh dasuke tare bayan sun dawo cikin gida ya shiga mata fada,kan wulakancin datakema,Dr Sultan Tura baki tayi tana fadin”ita batason Shi..,Tanada wanda take so.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button