NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

NOT EDITED????

                NO 28

    Lokacin da jirgin,ya Saukesu a filin jirgin na kasar egypt,bata chanza zani ba,domin Wani hotel daga cikin manyan Hotel din dake kasar,ya kama ya zauna domin bayada zabi,tunda baisan kowa ba agarin.

      Kwanansa uku akasar ammh ko kofar dakin dayakama bai Fito ba,yana cikin daki komai yake bukata sai dai Ma”aikatan hotel din su kawomai bayan yayi musu mgana,Tuni magungunansa suka kare ga yawan kwana dayake baya barci,damuwa tafara mai yawa, mugun ciwon kan nasa,da kuma jirin daya ke fama dashi na neman yadawo,baya komai daga kwanciya sai sallah shikadai ke tadashi,komai na duniyan nan yadaina mai dadi kwata kwata ya rigaya daya sallamama rayuwar jin dadi kwata kwata.

   Sai dai yayi Asati daya a egypt kafin ya karisa cikin birnin Sudan din,wanda chan dinma, Hotel yakama yayi zamanshi,baya ko marmarin Fita ma yaga kalar garin saboda yadda yake faman yaki da zuciyarsa wajen manta abunda ya faru dashi,ammh duk kwana duniya da hoton hira dana yaransa yake iya barci,inko ba haka ba,yadda yaga rana haka yake ganin dare,ga yadda yanayin jikinsa ya rikice gabadaya,ammh kuma yakasa daina zafafama kansa tunani balle yanema ma kansa mafita ,koda na fita yanemi mgani ne.


NAGERIA

  Duk wani bawa mai imani inyaga halin da Ummi ke ciki sai ya tsausayamata ballema in aka samu mai Raunin zuciya sai ya zubarmata da kwallah,Kallo daya zaka mata kaji gwiwanka tayi sanyi saboda yadda Ummi takoma kamar ba ita,ta rame tayi baki ta lalace kamar ba hajiya Suhaima ba yargata yar kwalliya,ammh lokaci daya rayuwa ta juya mata baya,bata cin abinci kullum sai kuka kamar wacce ta zare,sati daya tayi a asibitin aka sallameta bayan magungunan da”aka rubuta mata,yawancinsu duk na hawan jini ne,saboda yadda jininta yayi bala’in hawa,koda Dr.Abduljabar yayi ta lallashinta dakuma bata shawaran ta rage Tuanin jinsa kawai takeyi ammah har abada indai ba mu”azzam dinta bane yadawo an gayyato Tunani da rashin kwanciyar hankali a rayuwarta na har abada.

Koda suka koma gida bata chanza zani ba,Hajiya na nan Tare da ita,don tace ina zata tabar Suhaima cikin wannan halin dole ta zauna tare da ita,shureim shima sati daya yayi cur kafin ya tattara matarsa da yaransu sukoma zaria,shima badon aikinsa ba wlh da dawo nan zaiyi ya zauna su jajantama kansu tare,saboda shima ayanzu baida wani kuzari,domin Rashin mu”azzam tamkar rasa wani bangare na shi wanda maidasa abu ne mai wuya.

Lokacin Da Shureim yakira chan maiduguri yana tambayan bukar ko mu”azzam yazo nan,fadan tashin hankalin da suka tsinci kansu bata faduwa,Shettima fadi yayi wanda yayi sanadiyar samun paralayze ma”ana gefen jikinsa na dama yadaina aiki ga bakinsa ya karkace yana zubar da miyau babu kafa babu baki,Yakura ma fadin halin data ke ciki bamai dadi bane,ga wannan abu ga kuma laluran Shettima wacce ta kamasa sanadiyar rashin sanin inda mu”azzam din yake,Shikanshi bukar yaji ba dadi,da lbrin barin mu”azzam  gida,duk da tuni ya ya yafemai wlh baya rike dashi aransa,Dole tasa aka boyema Zahirah bukar yahana kowa ya fadamata ko mahgana ya gargadeta akan karta kuskura ta fadama zahirah wannan lbrin ko tasamu natsuwar kula da yaranta cikin Aminci batare da wani mtsala ba,duk da tana cikin halin damuwa,ga laluran data samu baffa,wanda ranar dataji wuni tayi tana kuka kamar wacce ta zare,kullum kuma cikin gwada nombar Mu”azzam din take ammh bata shiga amsa dayane ake bata wayar akashe take,tayi kuka kamar me aranta tanaji kila ya mu’azzam ya barta ne,bari na har abada tunda gashi ya yanke duk wata hanyar da zata sadata dashi,kuma tasani yana waya da wanda yaso,ita batasan Abunda ke faruwa ba.

   Yara kuwa suna cigabada da Samun kulawa yadda yakamata,dayake nonon na zahirah mai kyau ne  ga ishshen madara dasuke samu,shiyasa lokaci kadan sukayi bulbul dasu gwanin sha”awa ba”a chanza musu sunaye ba,Ummi da moodu ake kiransu yaran in ka gansu kamar ba yan Sati hudu ba da haihuwa saboda yadda suka fara wayau dasu,Tuni bukar yagama tsaida shawaransa kan zahirah Bayaso ta samu lbrin Tafiyan mu”azzam tana gidansa yafi so ko zata samu ya kasance tana gidan mijinta ne,shiyasa duk wani shiri ya gudanar ko gudanar da neman Auren gun yayyinsa akaje susuka ka gudanar da neman auren harta da sadaki an biya, kawai ranar daurin aure ake jira,ganin halin da baffa yake ciki yasa bukar dakatar da daurin auren da zarar Zahirah tayi arba”in   yabari baffa yakarajin sauki kafin komai ya kamkama.


SUDAN

   Kwanan Mu”azzam goma baitaba marmarin Fitowa ba,sai ranar daya gaji da kwanciya,kawai sai yaji aransa yanaso ya fita koda kuwa harabar hotel din ne,shiyasa ya kokarta ya fada tiolet yayi wanka,sakamakon baizo da kaya ba,kuma bai samu sukunin siya ba kayan jikinsa su yake maimatawa,gashi sunyi datti sun chanza kamanni ammh ko ajikinsa haka ya kakkabesu ya maida ga sumar kansa tayi yawa,ga yadda kasumba ta tarun mai,duk wanda yasan Mu”azzam indan ya gansa lokaci daya bazai shaidasa ba, bawani kwalisa,ba wani gayu bawani fesa turare in ga gansa alokacin kace wani saurayin Kauye ne saboda yadda ya saki rigar takusa zuwa cinyarsa,kuma ko tek tie dinsa bai saka ba,nikaina dana kallesa sai naji dariya hade da kuka lokaci daya ya kubcemin saboda tsausayin yadda rayuwa ta maida matashin Barrister kuma dan kwalisa maiji da Naira da Kwalisa yakoma lokaci kadan.????????????

  Fitowa yayi yana tafiya kamar bashi ba saboda yadda bai da lafiya domin kansa juyamasa yake,ammh kamar ingizashi ake da fitan da zaiyi,koda ya kariso haraban Hotel babu ruwan kowa da kowa jajayen Fata ne ,da larabawa keta kaida kawosu babu mai kallon wani balle har yakula da mai kakeyi,ba irin garinmu Naija ba,da in aka fara kallon mu’azzam ana dariya sai ya raina kansa????,

  wajen Hotel ya fita yana tafiya ahankali yana kalle kallen gefe,yayi Tafiya mai dan nisa kan ya isa waje daya ga mutane na zama,waje ne ba” killace yake ba,fili ne gefen wajen wata koramane datake gangara tana zubar da ruwa fari kal dashi,mai ban sha”awa,daga chan gefe kuma wasu fararen duwatsu ne suka barbazu awajen tako”ina ga kuma wata kasar rairayi mai laushi wajen,tuni wajen yazama yana bada iska sosai da sanyin dadi,shiken sai mutane suka samu wajen zuwa su zauna,ko mutum inzai dan hutu dadai sauransu,har wani ma”ikatar saida Lemuka masu sanyi sukayi amfani da wannan damar suka kara raya wajen,suka baza ma”aikatansu awajen,inkazo duk abunda kake bukata na ababen sanyi zasu kawo maka in ka gama ka biya,shiyasa wajen yake tattara kowa da kowa kama daga yan kasar harda baki masu zuwa daga kasashe mabambamta Kuma mafi akasari baki sunfi moran wajen Tunda yana daura Da hotel din wajen.

  Gurin yabawa mu”azzam sha”awa matuka shiyasa ya karisa ya zauna kan daya daga cikin duwatsun dake wajen wa”inda aka gyarasu akallo daya bazaka ce duwatsu ne wanda Allah ya kwafa ba,saboda yadda aka kawatasu kamar wasu mulmulayen kujeran zamani nazama,ruwan dake wucewa ta tsakanin koramar ya tsurama ido kawai yana kallon Ransa nadan sanyi saboda yadda iska ke kadawa,koda ma”aikatan kamfanin lemun suka karisa ko dawani abu dayake bukata hannu kawai ya daga musu alamar baya bukatar komai,basu damu ba,Suka wuce tunda waje ne daya hada kowa da kowa harda bakaken fatan ma akwai balle shida fatarsa ta hade taxama ruwa biyu babu wanda zai kallesa yace ba dan kasar bane.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button