NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Mu”azzam na kwance kan kafet baya da riga daga shi sai Wani bakin dogon wando,kallo daya zakamai ka kauda idonka saboda yadda yakoma,ya rame ya lalace kamar wanda ciwon ajali yakama,wayarsa dake gefe dake keta kuka tundazu ya mika hannu cikin karfin hali ya dagota da niyyar ya kasheta gabadaya,Sunan wanda yagani yasashi mikewa yana rike kansa Da hannu daya BUKAR MAID ne ke kiransa.

Sai da ta katse yakasa daukan kiran saboda yadda zuciyansa ke amsawa,tuni kansa yayi masa wani Nauyi,wani kiran ne ya sake shigowa cikin karfin hali ya daga kiran batare da yayi mgaba ba don ji yayi bakinsa ya kafe da Wani miyau mai daci,Bukar kuwa yanajin mu”azzam yadaga kiran yace kai tsaye”Zahirah ta dawo gida,Ranar data dawo Allah ya Sauketa lafiya yau kwana hudu Tasamu karuwan yara biyu mace da Namiji,zaka iya zuwa,ko ka aiko da sakon Sunan da za”a sanya ma Yaran..”daga haka kawai Bukar ya yanke wayar yanajin Haushin mu”azzam har cikin ransa,don harda shi aka taru aka boyemai Halin da yarsa take ciki,wanda daya nada,lbri wlh da dakanshi zaije ya daukota yadawo da ita gida.

Mu”azzam kuwa wani tari ne ya sarkeshi saboda jin yadda bukar din yamai mgana,ga murnan Samun Lbrin Hiransa lbri mai dadi harda lbrin haihuwa ya”ya biyu Allah Abun godiya,Mirmishi yake mai kama da kuka lokaci daya tarin na kara sarkeshi lokaci daya hancinsa yafara zubar da jini,wani abu ya tahomai abaki da yawa yana tara hannu yazubo da jini mai yawa,cikin rudewa yake bin jinin da kallo lokaci daya yana dafe saitin zuciyarsa dake masa ciwo yana cigaba da tarin,kuma hancinsa bai daina zubar jini ba.

DON”T FORGET TO COMMENT,SHARE AND VOTE…

Mami Jamila
Salam.
Sanaz ce
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

Intelligent writer’s Asso

Wannan Safin kacokan sadaukarwa ne gareku UWAR MIJINAH FANS1 expecially u guyz My Shatutu????,my Esha????,momy mubeena(Takwara),Aisha bello,Rukkayat❣,na gaisheku,hakika salon sarhinku na kashe ni da dadi,keep it up bbys u always make proud ,Allah ya bar so da kauna Janaf tana godiya sosai

NOT EDITED????

             NO 25

     
  Shureim ya tabbatar tunda yaji muryan Ummi cikin kuka,to babu lafiya tuni zuciyarsa tazargi Ummi ta fuskanci abunda Mu”azzam ke boyematane,shiyasa yasakin ma motarsa gudu cikin lokaci sai gashi ya iso Abuja,hon ya zuba maigadi yazo ya budemasa get yana masa barka da zuwa.

Cikin hanzari ya fito daga motan yashiga cikin gidan,da Ummi yafara cin karo tana zaune afalo tayi tagumi idanunta sunchanza kala alamun tasha kuka kenan,tana jin sallamar shureim ta mike jikinta na rawa take fadin”Shureim ka taimake ni don Allah,wlh mu”azzam zai kashe kansa yau kimanin kwana hudu ko Fitowa baiyi ba,babu ci babu sha..”Takareshe fada tana tsiyayar hawaye.

  Baisamu zarafin mata mgana ba, ya nufi shashen mu”azzam din yahau bugamasa kofa yana fadin”Dan”uwa kazo ka bude nine…”ammh ina mu”azzam na jinsu sai dai kuma baida karfin iya tashi saboda yadda jikinsa ya saki gabadaya jininsa ke zuba ta baki ta hanci ga yadda zuciyarsa ke zafi,yana so ma ya mike ya kasa.

  Hankalin Shureim ya tashi da baya yaja yama kofar duka daya ta bude, da gudu suka rankaya shida Ummi cikin daki suna kwalamai kira,Ummi kuwa kamar ta zare tsabar rudewa,sun shiga bedroom din suna kiran sunansa ammh duk basu lura dashi yashe kan kafet ba,sai da Shureim ya duba tiolet nan ma babu shi kana yafito yana kokarin Ficewa daga bedroom din ne yaji ya shuru kafan mutum,cikin wani razana yakai kallonsa kan mu”azzam wanda gabadaya jikinsa ya baci da jini cikin wani karaji ya karisa garesa yana rikosa lokaci daya yake fadin”Mu”azzam…..”da karfi cikin tashin hankali.

Da gudun gaske Ummi ta kariso wajen ganin yadda mu”azzam yazama kamar mataccen ga jini duk yabatamai jiki ai sai ta dora hannu akai tasaki ihu tana fadin”Na shiga uku ni Suhaima, mezan gani haka mu”azzam?  tafada tana tale mai ido kamar wata zararra ganin haka yasa kawai Shureim Ficewa da sauri zuwa haraban gidan yana kwalama su Ushe kira da hanzari suka fito da hannu kawai yayi musu alamar dasu biyosa,suna shiga dakin suka tarar da Ummi durkushe gaban mu”azzam tana girgizasa tana kuka da sambatu,cikin Rudewa shureim yace”Ku taimakamana mukaisa mota..”Yafada muryansa na rawa suma din cikin Tashin hankalin suke da hanzari suka tallabeshi sukayo waje dashi,su karime dake tsaye suna ganin An Fito da yallabai kamar gawa ai sai suka rikice da kuka,Ummi kuwa kamar ta zare Amota suka sanyasa shureim ya shiga mazaunin Direba Ummi kuma dako takalmi babu balle mayafi ta shige baya wajen mu”azzam tana rumgume dashi tana kukan ta shiga uku.

  Specialist hop,suka nufa,suna isa Shureim yayi ciki yana kiran Nurses da gudu kuwa sukazo da abun daukan mara lafiya suka ciccibi mu”azzam suka dora da gudu sukayi cikin asibitin dashi,kai tsaye aka shiga emaergency dashi cikin mawuyacin hali mai wuyar fassaruwa.

Ummi zaman dirshan tayi abakin emergency tana rusa kuka,shureim yakasa mata mgana domin shima kamar yayi kukan yakeji,tabbas in abunda yake zargi ne yakama mu”azzam lalle rayuwarsa tana cikin hadari,ganin Ummi tafara tara musu mutane ne yasa ya isa gareta yana fadin”Don Allah Ummi,kiyi hakuri kibar wannan kuka,taso muje ki zauna insha Allahu Mu’azzam zai tashi bazai mutu ya barki ba..”dagowa tayi ta kallesa idanunta suncika da hawaye tace”Haba shureim inbar kuka fa kace? baka duba da ni ya nawa rayuwar zata cigaba matukar mu”azzam ya mutu ya barni,wlh rayuwata,bata da amfani ina mai tabbatarmaka nima zaku iya rasani..”Tafada tana rusa kuka.

Kallonta yake cikin tabbatar da abunda ta fada,kafin ya riko hannunta ya mikar da ita yana fadin”Naji Ummi,ammh kitashi addu”anmu kadai yake bukata ba kukanmu ba taso muje ki zauna kinji..”Dole tatashi yana riketa da ita harzuwa kan wani benci ya zaunar da ita shima ya zauna agefenta yana sakin ajiyar zuciya lokaci daya,itako Ummi hannunta ta hau kirgawa kamar tana charbi sai muyi muyi take da baki hawaye na shatata bisa kuncinta.

   Sun dade shuru kafin shureim yakatse shurun da cewa”Wai duk meyajawo wannan abun ne Ummi? ni a iya sanina Mu”azzam baita ciwo makamancin wannan ba.?.”Yafada yana kallonta,shuru Ummi tayi tana kallon kasa kan ta share hawaye tace”Takan na rabasa da wannan Tsinanniyar yarinyar mana,ashe ba haka tabarmin dana ba,sai da ta asirceshi kafin ta barshi..”Cikin Rudewa Shureim yace”Wa? zahirah Kike Nufi Ummi? badai kin saka mu”azzam ya saketa ba..?’wani banzan kallon Ummi tamai kantace”kwarai ni dakaina na saka ya saketa ,..”Tafada kai tsaye.

Shureim dayayi mutuwar zaune cikin wani yanayi yace”Kan wani dalili Ummi? Gefe ta kallah kan tace”Kan daliin cin amanata da sukayi yayi mata ciki batare da na sani ba,nikuma har abada bazan hada zuru”a da Diyar Fadi ba, har abada.”Tafada cikin son tabbatarwa.

Dafe kai shureim yayi yana fadin”Shikenan Ummi,kinyi sanadiyar dakushe Farincikin Mu”azzam,wlh tallahi zahirah itace ginshikin Farincikin rayuwarki data mu”azzam gabadaya..”Yafada cikin karaya wani banzan kallo Ummi tamai kafin tatashi ta chanza wajen zama tana hararan shureim din,shiko kallonta yake yana mamakin Ummi ashe haka tayi nisa baitaba sani ba,ki raba miji da mata,kuma harkina kirari da kanki,kai Tir da wannan bakar zuciyar,zuciyar da bazata kulla maka alkhairi kan mutane ba sai sharrinsu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button