NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Ammh mutane sun kasa gane haka,suna ta zunden cewa kwadayi ne yakai bukar din to inba hakaba,saurin meyakeyi,wasu harcewa suke haka zai kare wajen kwadayi,auren da yayimata na farko,shima kwadayin yabi ammh ba”a kai ko”ina ba aka sakomai yarsa da ciki,to gawani ya sake yimata ko dandara baiyi ba,wasu harsuna cewa zaiyi hankali in wannan karan yaji lbrin anyi kudi da kan yarsa tukunnah,kuma duk masu wannan gulman,wasu daga cikin yan”uwansa ne,dakuma wasu daga ciki  lalatattun makota marasa tsoron Allah.

WANENE ALH KABIRU BAKANO

Alh kabir bakano haifaffan garin kano ne gaba da bayansa,aiki ne yakawosa maiduguri Shine manajan dayake rikeda babban gidan Nepa dake maiduguri,yana da tarin arziki matuka don mahaifinshi ya mutu yabarmai tarin dukiya daga shi sai mahaifiyarsa wacce suke cema inna,Alh kabiru ba yaro bane,don ko bukar zai girmemai kadan ne,shekaransa ashirin da auren Yagana wacce itama yar asalin maidugurince tun Sadda yafara aiki achan suka hadu ya aureta,tun da kuma ya aureta Ko batan wata bata taba yi ba,Hakika mahaifiyarsa inna tana bukatar ganin Jikokinta ma”ana ya”yan danta ammh kuma abu shuru,dole yasa ta shiga nema mai aure,tunda shiko ance yanema baya nema,Inna da kanta nema mai auren wata budurwan anan kanon ammh abun ban haushi yarinyar ko wata shida batayi ba ta gudo daga maiduguri tacema iyayyanta baxata iya ba dole suka raba auren,na biyu ma data nema mai bazawara ita ko tarewa ma batayi ba ya saketa na uku kuma satinta uku ya saketa tadawo gida ganin abunda yakeyi ne yasa ko inna taje neman mai Aure ake hanashi saboda dabi”ansa na auri saki,tu tana fadan hartagaji ta zubama sarautar Allah ido taci gaba damai addu’a.
    
  Duk abunda ke faruwa matarsa yagana ne ke asssashi,yagana macece mai kishi da son abun duniya tana matukar son mijinta kabiru shiyasa bata kaunar wata mace ta rabeshi koda uwarsa ne,itace ta lalata aurensa na farko na biyun ma ita ta mata asirin tabar gida shikenan kuma sanadiyar barinta gidan,na ukun kuma ita da kanta ta umarceshi daya saketa saboda yadda ta asirceshi sai abunda takeso yakeyi jiki ko na rawa ya saketa,to tundaga lokacin ta kafeshi ta tare gaba tatare baya,ko mganar aure kabiru bayaso amai saboda yadda yagana ta mike tsaye da shiga malamai.

Alh kabiru aboki ne ga bukar wanda sun dade suna tare tunkan auren zahirah na farko duk abunda yafaru yasani, tunda bukar na fadamai,mutuwar aurenta da haihuwarta duk yasani,Alh kabiru saboda addu”an Da inna kemai yasa yafara dawowa cikin hayyacinsa yaji shima yana sha”awar yayi aure har shima ya haihu,shiyasa tunda bukar yabashi lbrin zahirah shikenan yaji komai ya tsayamai,kwadayin samun zuru”a da ita yasa yayima bukar zencen Aurenta in ya Amince,Bukar babu yarda zaiyi domin Kabirun yanada wani mtsayin agunshi,na wanda bazai iya neman abu agunshi yahanasa ba,shiyasa ya amince da batun nasa,yaso yabari ta yaye yaran ammh Alh kabirun ya mtsa sai anyi yanzu saboda kwadayin yaran da za”a kaimai gidansa ko bakomai yau shima zaiji wani dadi matukar yashigo gidansa yaji kukan jarirai,yagana batasan da wannan auren ba,inna ce kadai ta sani wacce tayi rawa tayi juyi sai dai ita ta kwabeshi da karya fadama yagana komai tukunah sai in Lokacin Tarewan yayi.

Adaren Ranar da”aka Dauran auren bukar ya shiga har dakin zahirah ya yimata nasiha bayan ya damkamata sadakinta ahannunta,saboda rudewa  Zahirah sulalewa kawai tayi akasa tana kuka,aure kuma? takai wadan nan yaran ina? wayyo ta shiga uku kenan ya tabbata rabuwarta da mu”azzam ya tabbata,har bahna din nata yafice bata sani ba saboda yadda take kuka,yana fita tatashi da dauko little Ummi da moodu ta rumgume tana kuka tana fadin”Shikenan anmin katangar karfe da Abbanku,wayyo nikaina,wlh bazan iya zaman aure da kowa sai kai ya mu”azzam”Haka taketa fada tana kuka,maghana ne ta shigo ta sameta awannan halin ita ta zauna ta dinga lallashinta tana fadin

  “Kibar kuka yahna,halin dakika shiga shiyasa tadama mahaifinki da hankali,don Allah zahirah ki donne zuciyarki kiyima Bahna dinki biyayyah ko hankalinsa zai kwanta,mu’azzam kuma ko kin zauna aure fa ya kare atsakaninku dole ne ko kina so ko baki so sai kinyi wani auren”tafada da sigar lallashi.

  Dago kai zahirah tayi idanunta na zubar da kwallah tace”to sai ayimin aure mahgana da danyen jego,ina shayarwa,kamar an gaji dani,ai abari na yayesu ko in Abbansu ya karbesu lokacin bani da wani Nauyi akaina,yanzu ko damai zanji da hidimar miji ko na ya”ya wanda kusan hakan ma mtsala ne..”Dafata maghna tayi tana fadin”Karki damu da wannan shi yaji yagani,yace dakeda yaran yake bukata,kiyi hakuri ki tashi kije kibawa bahna dinki hakuri ki kuma fadamai kin amince da zabin dayayi miki..”Jin haka yasa zahirah mikewa ta share hawayenta ta fice zuwa dakin bahna dinta,wanda tasamu yana ta safa da marwa cikin damuwa,ta shigo dakin zuwa kawai tayi ta rumgumesa tana fadin’Kayi hakuri bahna wlh na amince da zabinka gareni dam…”Shiiiii…”Yafada yana juyo da ita bayan yasaka dan yatsa abakinta yake fadin”Nasani Yahna abun da ciwo ammh to ya zamuyi sai hakuri ki rumgumi kaddaranki Haka Allah yaso ya ga rayuwarki ta tafi,tashi kije ki kwanta ki kula da ya’yanki Allah ya cigaba da dafama rayuwarki har abada.,Da Amin ta amsa bayan ya sharemata hawaye ya rakota har daki kafin yamata sallama yakoma dakinsa fuskarsa tana bayyanar da farincikinsa.

   Mahgana dake gefe tashare hawayenta tana mai jin Farinciki koba komai tana tsausayin zahirah da mahaifinta saboda sunga jarabtar rayuwa,Ranar kwana kuka zahirah tayi kamar ta zare,kuma haka ta kwana tana kiran layin mu”azzam ammh amsa daya ne akashe layin yake dole ta hakura ta shiga da kuka tana rumgume da yan diyanta tana kukan musu maraicin dasukayi dukkansu.


SUDAN

Yau kimanin kwana hudu kenan tana zuwa wajen bata ganinsa,ta shiga damuwa matuka,kuma babu yarda zatayi ta shiga Hotel din saboda dokace,sai in kanada tiket wanda yakama daki kadai awajen yakeda sai dai inzaka shiga shi ya Nuna kushiga tare,Ranta babu dadi yau dinma shiyasa bata dade ba,ta mike tana shirin tafiya kamar amafarki ta ganshi yana tahowa cikin wani yanayi yadda takaremai kallo sai taga ya rameta a ido,kuma inba idonta gizo yake mata ba hada hanya yake yana cije baki,alamar dakyar yake Tafiyan.
  

  Wajen daya saba zama yaje ya zauna,wannan karon tsakanin kafafunsa ya tura kansa,ganin haka yasa tayi azaman karisawa, wajen tanamai sallama kamar kullum,yanajin muryanta yaki dagowa,yana mamakin naci irin na yarinyarnan,duk irin wukalancin dayake mata taki barinsa ya huta,saboda ita ya dauke kafa daga wajen ammh kuma duk da hakan bai tsira ba,dole ne yau ya chanza masauki inda bazata kara ganinsa ba.

  Dagowa yayi batare daya kalleta ba ya mike, yafara tafiya yana tangali ganin haka yasa ta bishi tana fadin,”Don Allah ka tsaya baka ganin kana neman Faduwa ne..”Tafada cikin harshen Turanci,ko waigowa baiyi ba ganin haka yasa tazura da gudu tasha gabanshi tana fadin”Plz Allow me to help u…”Tafada tana hada hannayenta waje daya.

Ransa ne yabaci ya dago Afusace ya saka hannu ya tureta tayi baya tafadi dabams,wanda sai da kugunta ya amsa yafara mgana cikin Fushi, cikin haddaden Turancinsa”Ki rabu dani mana,ana dole ne? kin dameni kin takurama rayuwata, as from today don’t ever Talk to me again”yafada daidai lokacin da tari ya sarkeshi kan kace kwabo jini yafara biyo hancinsa da bakinsa,itako suman zaune tayi tana kallonsa cikin mamaki,yadda yake Turanci lalle hasashenta yazama gaskiya,duk da chan babu ruwan wani da wani ammh har anfara taruwa ganin yadda ya duke yana taro jini ahannusa,cikin galabaita da ciwo yayi kokarin cigaba da tafiya ammh taku kadan yayi ya rike kansa dayake juyamai kafin kace me ya zube kasa warwarsa babu ko Numfashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button