NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

Ummi tace”Toh Allah Yakaimun lafiya..”dahaka suka datse kiran Ushe na malala gudu bisa kwalta ammh Ummi gani take kamar baya sauri saboda kaguwa da fargaba,addu”an take aranta Allah yakaisu lafiya ammh azahirin gaskiya mutuwar shettima ya girgizata ba kadan ba.

Comment,share and Vote

     Jamilajanafty
UWAR MIJINA…!
(Soyayyah,Sadaukarwa,hakuri tare da biyayyah mai tsanani)

       Mallakar:JANAF
       Wattpad:Janafnancy12

Dedicated to my blood Sisters JANAF

GIFT TO:Hussain80k

Intelligent writer’s Asso

  Dis Special page, iz belong to only u My BANANATY..,????Neesher jay writer of kibiyar Ajali????,Ashwan,am relli Appreciate ur luv dear, kip it up U always make me proud bby Neeshar,ur gwandaty say ONE LUV????????????

              NO 48
 
  “”Kusan atare Su Ummi da hajiya suka iso,don motarsu na tsayawa sun, Fito kenan sai ga motarsu suma Tayi parking akusa dasu,koda suka isa har andawo da gawan baffa gida yakura tayimai wanka an hadasa za”a mai sallah a mikasa gidansa na gaskiya,nan waje Shureim ya tsaya wajensu Bukar da mu”azzam yayinda Hajiya da zulaika suka bi bayan su Ummi.

  Koda Su Ummi suka shiga cikin gidan gwanin ban tsausayi gida ya cika da mata,sai koke koke akeyi suna shiga yakura da mahgana suna uwar daka, Suna zaune,chan su Ummi suka taddasu,zahirah na shiga ta fada jikin Yakura tana kuka riketa yakura tayi tana fadin”Ta faru takare zahirah yau an wayi gari baffanki yatafi ya barni..”take fada tana tsiyayan hawaye sanye take da dogon hijabi da chasbaha ahannunta tana tsiyayan hawaye,Ummi ta karisa kusa da ita ta zauna tana fadi”ya mukaji da hakuri yakura..”tafada tana sharban majina.

Kada kai yakura tayi kafin tace”Hakuri duka namu ne Suhaima,shettima kam an tafi sai dai Fatan dacewa da Rahamar Allah..”Duka adakin aka amsa da Amin kafin su cigaba da share kwallah,nan hajiya tayimata gaisuwa itama kafin Takoma gefe tana sharan kwallah,lubna ke zaune gefe tana rumgume dasu little dasukayi Shuru kamar sunsan Abunda ke faruwa.

   Babu dadewa aka sallahci baffa Shettima zuwa gidansa na gaskiya,wanda hakika yayi jama”a sosai dan adam sun taru makabartan dake kusa dasu aka binnesa,Hatta Dr,Abduljabar yasamu jana”izar baffa,amakabarta haka mu”azzam ke kuka harda majina shabe shabe,sai da su Shureim suka rikosa kana ya dago daga kan Kabarin baffa yana hawaye..Allahu akbar Allah kenan,wanda Shine hallicemu domin muzo duniya mu bauta masa,kuma yayi alqawarin daya bayan daya zamu koma garesa,Sai dai muyi fatan Allah ya karbi bakuncin Baffa yakuma yafema iyayyanmu,dasuka rugamu gidan gaskiya yasa Aljannah tazo kyakywan makoma agaresu Amin ya Allah.

  Bayan andawo daga makabarta awaje aka baza tabarmu mutane suka zazzauna ana amsan gaisuwa,cikin gida kuwa Mata sunsha koke Zahirah ko tana kwance zazzabi ya rufeta saboda kuka,kan kace kwabo sai kulolin Abinci ke yawo agidan da katan katan din lemuka da ruwansha wanda mu”azzam yabada Umarnin aka sauke saboda mutane,baima san zahirah bata da lafiya ba, sai washegari daya shiga cikin gidan nan ya isketa kwance,hankalinsa ya tashi sosai,Dr,Abduljabar ya dubata yace damuwace ya rubutamata magunguna harda na karin jini domin yace jininta yayi kasa sosai,Fada sosai mu”azzam ya dingama zahirah kafin yakoma lallashi Kamkame juna Sukayi ita dashi suna kukan rasa uba majingini agaresu,to yazasuyi Abunda Allah ya tsara bawa bai isa ya tsallake shi ba.

Yau akayi addu”ar bakwai din Baffa Shettima duka jama”a sun watse daga kofar gida,sai na cikin gida kadai irinsu Ummi da su hajiya,anyi addu”an bakwai kowa ya kama gabansa,Su mu”azzam da Shureim da bukar suna cikin falon gidan zazzaune anakarama juna gaisuwa,Ummi ce da Mahgana sai hajiya da yakura,su Zahirah da zulaika da lubna suna cikin daki su da yara,Taruwa sukayi suna bawa yakura hakuri saboda yadda haryau batabar kuka, ba dole tayi kuka mutuwar miji ba wasa ba,Gyada kai kawai take bata mgana sai dai share kwallah,nan Bukar ke fadamasu Ummi rasuwar matar Tsohon mijin Zahirah Alhaji kabiru wato yagana,wanda yace harma Tayi arba”in da rasuwa azencen dayakeyima harma Mahaifiyarsa tamai Aure daga kano.

  Rike baki hajiya tayi tana fadin”oh duniya Yanzu duk bala”in matanan game da mijinta,sai gashi ta mutu ta barshi..”Bukar yace”dama haka rayuwar take,ance chan wajen bin yawon bokayentane sukayi hatsari Ita da wata hatsabibiyar kawarta, ance motarsu Ta shige kasan Daf ne rai ko daya ba”a fitar ba daga motan,tsakanin kankara zuwa Dutsenma Abun ya faru..”Sallallami suka dauka Yakura tace”Allah yajikanta,duniya kenan duk yadda kaso ga Sonta watarana sai ka mutu ka barta..”duka suka amsa da Amin Ummi ce tasaka baki takira zahirah Ta fito nan take shaidamata rasuwar Yagana dafe kirji tayi kafin tace”innalillahi yaushe Ummi? wlh banji ba…”Tafada idonta na cikowa da kwallah nan Ummi ke fadamata yadda bukar yafadamusu,kanta ta sunkuyar tana fadin”Allah yajikanta da rahama..”Tafada cikin Rauni hawaye yana tarun mata,kwallah na Shirin zubomata dago kanta tayi suka hada ido da mu”azzam saurin girgizamata kai yayi yana mata nuni da hannu alamar karta bari hawayen idonta su zubo,saurin kauda kai tayi tana kokarin danne kukanta.

  Mu”azzam yakalli Ummi yana fadin”Gobe kafin mu wuce sai muje muyimasa gaisuwa,daman inason ganinsa,kunga yamazo adaidai kenan..”kowa kallonsa yayi yana mamakin Furucinsa kauda zencen yayi da cewa”Kuma Baba zamu tafi da yakura chan Abuja,su zauna tare da Ummi nan kuma sai A rufeshi duk sanda akazo sai abude asauka aciki..”Bukar yayi ajiyar zuciya kan yace”Shikenan Tunda haka ka yanke,ada naso ni na dauketa takoma gidana,ammh babu komai dachan da nan Duk dayane aie..Allah ya jikan baffa yasa ya huta..”Gabadaya suka amsa da Amin yakura na kuka tace”Dama kun barni nayi zamana anan,inyi ta sallah da ibada har nima nawa lokacin ya cinmin”Tafada tana kuka wanda yayi sanadiyar tashin zahirah da Sauri takoma daki saboda tsausayin yakura.

  Dafata hajiya tayi kan tace”a”a yakura baza”ayi haka ba gwara kikoma chan ku zauna tare da suhaima,kinga nan ke kadai ne,kadaici zaiyi miki yawa,chan ko ko banza akwai kiriniyar yara,zaki ji zuciyarki ta rage kuncin datake ciki..”Kowa yayarda da kalaman Hajiya har ita yakura ta gyada kai tana share kwallah,nan dai sukayi addu”an kafin atashi taron.

Haka ko akayi washegari da safe dukkansu sukayima gidan Alhaji kabiru kwanya,Bukar shine jagoran tafiya sunazuwa kofar gidan yadaga waya yakirasa yace gasu awaje yazo da baki ne,jin hakane yasa Alhaji kabiru Fitowa ganin mutane da yawane,yasa yace dukkansu su Shigo don Allah,ammh har lokacin bai lura da zahirah ba,dumguma sukayi har zuwa falon gidan,Alhaji yahau kwalama matarsa kira hajara tafito da sauri tana ganinsu ta hau musu sannu da zuwa,Amsamata sukayi cikin sakin Fuska kichen ta shige takawo musu lemuka,da ruwa ita da zulai,Wacce itace ta lura dasu little Ummi,aiko da gudu ta isa garesu ta dauki Ummi tana fadin”La Alhaji ga Ummi karama..”tafada tana nuna mishi ita,shima da mamaki yake kallonta kan yamika hannu yana fadin”a”a Zo zo..,”yake fada yana amsanta kan yace”ina moodu ne? Fadin haka yaji moodu ya rikemai kafa yana bangala dariya kallonsa yayi yana fadin”a”a manya diban Fari,ashe kana kusa”yafada yana dagasa da hannu daya,suka ko lafe sunamai dariya da gwarancinsu kamar sun ganeshi kallon bukar yayi kafin yace”Ai sai kacemin da yarana kake tafe kabarni Shuru sai da suka shaidani..”Dariya bukar yayi kan yace”Ai duka Alhalinmu muke tafe,harda mamansu da mahaifinsu gabadaya”yafada yana kallon mu”azzam.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button