NOVELSUWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL

UWAR MIJINAH COMPLETE HAUSA NOVEL BY JANAF

   Ko Kafin wayewar gari duk wanda yakamata yaji lbrin mutuwar Auren zahirah,Lubna da kanta ta kira su Abbie tana fadamusu,bayyana irin murnan da Abbie yayi bata lokaci ne,Shikanshi mooh yataya mu”azzam Murna saboda dawowar Farincikinsa,shima Shureim Da mu”azzam din kefadamai kin yarda yayi Saida ya dawo gida Hajiya kefadamai yanzu suka gama waya da Ummi take fadamata,baki ya rike yana mamakin wannan al”amarin Lokaci daya Farinciki ya mamayesa Abokinsa zai dawo Mutum kamar da,saboda dawowar Uwar ya”yansa,kuma bugun zuciyarsa.

   
Ranar mu”azzam dakyar yayi barci saboda murna,salallo kuwa na godiya ga Allah ya jerasu ba adadi,tunkan ma zahirah tadawomai akaro na biyu,itako lubna kwana tayi kukan,kukan Tsausayinta kanta da rayuwarta domin daga Ummi har ya mu”azzam bata ta kanta sukeyi ba,suna ta murna da wannan al”amarin ne,gwara ma Ummi dataji ta Shuru ta leka tana tambayanta ko lafiya? ammh mu”azzam ko nemanta baiyi banda buge bugen waya babu abunda yakeyi ya kasa ya tsare sai Ummi takira Maiduguri taji ya ake ciki shifa,ko yau ne sai yakama hanya,Tun Ummi na ganin Abun wasa harta Fahimci Mu”azzam din da gaske yake,Waya ta dauka takira hajiya tana fadamata rigimar mu”azzam din,dariya kawai hajiya tayi kafin tace abasa wayar,magana tayi mai cikin sanyi da fahimta,tafadamai cewa yanzu ya jira yaji abunda mahaifinta zaice,kuma mganar yadawo da ita nan Abuja ya barta domin bazata yuyuba yadai tsaya iya mganar dawo da ita gaban mahaifinta tayi iddarta,ko Shidin ma kada suyi mgana Sujira suga Abunda Shi bukar din zai zartar.

Dole Mu”azzam ya Sauka daga kan dogin naki,ya bar mganar zuwa maiduguri dauko zahirah,saboda Rudewa ne da murna yakasa ganewa Gaskiyan Abunda Ummi take fadamai,dole ya hakura,ammh shima ya share kafa ya zauna yana jiran tsammanin ammh ji yake kamar yayi Tsuntsu ya ganshi gaban Zahirah,wannan Jiran zai iya sa Zuciyarsa bugawa saboda doki,dama awajen aiki ansan baida lafiya,ai sai ya sake Sabon zama,Ummi sai da takalleshi tayi dariya tana tsokanarsa da Sabon Ango,datace haka sai yabata rai yace”Bawani Sabon ango Ummi bayan kunki dawomin da matata nan..”,yake fada yana wani Tura baki kamar yaro dariya takemai Domin Ta lura yau mu”azzam din nata rigimarsa ce tatashi.


MAID

  “”Bukar kwana yayi aransa abace gari na wayewa baima mahgana mgana ba,ya dauki mota sai gidan Auren zahirah Awaje ya tsaya yakira Alhaji kabirun yace ya fito yana kofar gida,Alhajin baiwani yi mamaki ba,domin yasan za”a Rina,shima jiyan bawani barci yayi ba,jallabiyansa ya zura ya fito haraban gidan,bai ga Motar Bukar din ba,sai ya fita waje,ya gansa jingine jikin motarsa karisawa yayi yana fadin”A!a ya haka Alhaji ka tsaya daga waje,kamar wani bako? Yafada yana mikamasa hannu.
  

Bukar yace”haba abokina,babu damuwa,nam din ma duk gidane aie.”yafada yana mikamasa hannu sukayi musabaha,Damke hannun juna sukayi Suna gaisawa kafin Bukar yace”Gunka nazo Alhaji,..”Alhaji yace”To mu karisa daga ciki Alhaji sai muyi mganaer..”Saurin girgiza kai yayi yana fadin”Basai na shiga ba,nan ma ya wadatar,mganar bawata mai tsawo bace..”,yafada kafin yace”Jiya da daddare zahirah takira mai dakina tana fadamata wata mgana data girgizani,wai ka saketa tun ma kwana goma daya wuce,shine nazo naji duk meya jawo wannan Abun Alhaji..”yafada yana kallonsa

     Mirmishin karfin hali Alhaji yayi kafin yace”Tabbas hakane,duk abunda tafada gaskiyane,na sauwakemata kwana goma da suka wuce Alhaji.”yafada yana son jadaddamai,Kallonsa bukar yayi kan yace”to miye dalili,?wani laifi tayi maka koko ita ta bukaci daka saketa,yanzu na shiga na cimata mutumci..”Saurin girgiza kai Alhaji yayi kafin yace”Ko daya batama san Abunda yafaru ba sai jiya dana fadamata,wlh Alhaji in nace gawani laifi da zahirah ta aikatamin da bayan tarewarta to nayi mata karya,sai dai cikin Rashin sani,ko ajizanci na dan adam..”bukar ya numfasawa yana fadin”To meya sa Ka saketa,kagaji da ita,koko baka sontane,ai da kafadamin Tuntuni da Wlh Tu fari ma ban yarda na auramaka ita ba,indai kasan sakinta zakayi.”yafada cikin bacin rai.

  Saurin Riko hannunsa yayi yana fadi “Wlh ban Auri zahirah da niyyar na saketa ba,bani da buri illa na zauna da ita har karshen rayuwata,inada babban dalilina na sakinta,nasani inda zata koma,zata samu Farinciki fiye da yadda zata samu agidana,kayi hakuri Alhaji bada gayyah nayi ba,inada dalilina,ammh kuma kayi hakuri kada ka tursasani sai na fadamaka dalilina nayinka.”yafada Muryansa ta fara rawa.

   Kallonsa kawai Bukar keyi yana jinjina kai,kafin yace”,to Shikenan Allah yasa haka shiyafi zama alheri,ammh mgnar zamanta agidanka tayi idda Gaskiya Alhaji ban amince ba,Tafito mutafi gida Tunda Aure ya kare to mekuma za”a jira..”Alhaji kabiru yace”Alhaji badai Fushi kayi ba ko?girgiza kai Bukar yayi kafin yace”Ko daya,kawai naga kyautuwa ne takoma gida tayi iddarta,ada dai na kullace ammh bayanin dakamin wlh ka wanke laifinka awajena.”jinjina kai Alhaji yayi kafin yace”Hakane,Kana da gaskiya bari na shiga nayimata mgana..”

.  Sake musabaha sukayi, kafin Alhajin yakoma ciki,direct dakin Zahirah ya shiga ya kwankwansa kafin ya tura ya shiga,tana zaune kan sallaya da hijabi ajikinta Little Ummi da moodu suna kwance basu tashi ba,da sallama yashiga dakin,juyowa tayi tana kallonsa kafin ta amsa sallaman tana mikewa,Gaisheshi,tashigayi Shiko ya amsa yana isa kusa dasu little yake fadin”Kai yau Sunsha barci,naga sundade basu tashi ba”amsamai tayi da cewa”eh wlh dayake Jiya basuyi wani barci ba rigima sukayi tayi sai wajen asuba suka kwanta”

  Zama yayi gefen gadon yana fadin”Subhannallah..Badai wani abu ke damunsu ba ko? yafada yana kallonsu,kauda kai tayi kafin tace”Babu abunda ke damunsu rigimace sukeji jiyanan..”tafada tana tsaye abayansa,bai waigo ba ya mike yana fadin”ok,kishirya yanzu Abbanki na waje yana jiranki,zaki bishi ki koma gida..”yana gama fadar haka ya fice da Sauri,da kallo tabisa kafin ta daka tsalle tace”wayyo Dadi,dama wlh nagaji da zaman gidan nan”Tafada tana isa wardrope dinta ta hau jido kaya sai da ta kwashe fin rabi,kafin ta barshi haka,takoma tana zubasu cikin akwati,nata dana yaran sai da tacika akwati Biyu kafin tabarshi haka,da hanzari,da Dauki little ta goya kafin ta fito falo tana kwalama zulai kira da hanzari ta fito da hannu ta yafito ta suka shiga daki Moodu ta mikamata tana daukan akwatin guda daya tace”Taimakamin zulai,waje zamu Abbana na jirana..”da mamaki zulai ke bin akwatunan da kallo kafin tace”Anty ina zaki haka..”mirmishi zahirah tayi kafin tace”Gidanmu zan koma zulai Aurena yakare tsakani na da Alhaji”Ido zulai ta zaro kafin tace”wayyo Allah..”Tafada idonta sun ciko da kwallah,dafata zahirah tayi kafin tace,”Kar ki damu zulai,haka Allah ya kaddara zama na,bamai tsawo bane agidanan..”

   zulai sai da tashare kwallah domin ta saba da zahirah uba uwa su moodu zatayi kewarsu ita ta daukan mata moodu har waje inda Motar Abban ke jiranta suna fitowa da sauri ya karisa yakarbi moodu hannu zulai yana kallon zahirah wacce ke janye da akwati,booth ya budemata ta saka kafin takoma ta dauko Sauran zata fito kenan taga yagana afalo tana kwasan dariya ta kalleta,batace komai ba tasakai zata fita,sai yagana tace”dama ai na fadamiki bamai Auren mijin yagana,dole ne ko an aura a barmin miji akara gaba..”take fada tana jifanta da wani banzan kallo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button